ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuri’ar Kwamitin Sulhu: Sai Yaushe Wasu Kasashen Duniya Za Su Warke Makantarsu?

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Sulhu

Yayin da duniya take sam-barka da amincewa da tsagaita wuta a tsakanin Iran da Amurka da wasu kawayenta, wani al’amari na son zuciya ya kunno kai yayin da ake kada kuri’ar neman amincewa da wani daftarin kuduri na amfani da karfin soji wajen rakiyar jiragen ruwa na kasuwanci a mashigin Hormuz, kwana daya kafin sanar da tsagaita wutar.

Kasashe 11 sun amince da daftarin kudurin, yayin da kasar Sin da Rasha suka hau kujerar na ki, kana kasashen Colombia da Pakistan suka dauki matsayin ’yan ba ruwanmu. Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya ya kafa hujjar kasarsa ta hawa kujerar na ki da cewa, kudurin ya gaza fito da asalin musabbabin rikicin baro-baro, wanda matukar ana son magancewa, wajibi ne a faro daga tushe, kuma a yi adalci ga kowane bangare.

Wannan matsayi da kasar Sin ta dauka, tunatarwa ce ga kasashen duniya game da sashe na 2, karamin sashe na 4 da kuma sashe na 51 na kundin Majalisar Dinkin Duniya da ya haramta amfani da karfi a kan wata kasa, tare da jaddada wajibcin bin hanyoyin sulhu wajen warware takaddama.

ADVERTISEMENT

Ba ma wai kawai matakin da Amurka da Isra’ila suka dauka na kaddamar da hare-hare a kan Iran haramtacce ne da ya yi karan-tsaye ga kundin Majalisar Dinkin Duniya ba, an dauke shi ne ana kan tattaunawar zaman lafiya. Bugu da kari, idan aka dubi hujjar nukiliya da aka bayar ta kai hare-haren, ita kanta Isra’ila da ta zama kanwa uwar-gamin abun, ba ta cikin kasashen da suka rattaba hannu kan haramcin makaman nukiliya a duniya. Kuma a tambayi hukumar IAEA mai kula da makamashin nukiliya ta duniya, shin ko a mafarki ta taba kai ziyara Isra’ila da nufin binciken sha’anin nukiliyar kasar?

Matukar ana son magance matsala da gaske, daga tushe ake tumbuke jijiyar musabbabinta, kuma wannan shi ne adalcin da kasar Sin ta nemi a yi wa kowane bangare na rikicin, domin idan ba a faro daga nan ba, zai zamo an kashe maciji ne amma ba a sare kansa ba.

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

A lokacin da Isra’ila take farko-farkon kaddamar da hare-harenta a zirin Gaza wadanda suka salwantar da dubban rayukan fararen hula, a wani tsokaci da ya yi, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce, ya kamata a duba matsalar daga tushe, ma’ana, mene ne ya haddasa harin da Hamas ta kai ranar 7 ga Oktobar 2023, domin kamar yadda ya ce, komin raunin mutum idan tura ta kai shi bango, zuciyarsa tana kekashewa. Amma me ya biyo bayan maganar tasa? Yekuwar a tumbuke shi daga kujerarsa ta MDD daga bangaren Isra’ila da wasu kawayenta, maimakon duba abin da idon basira.

A wata mukalar da ya taba rubutawa, masanin zamantakewar dan’adam, farfesan farfesoshi kan sulhunta rikicin kasa da kasa a Jami’ar Notre Dames, John Paul Lederach ya bayyana cewa, zaman lafiya mai dorewa yana samuwa ne daga magance rikici daga tushe. Shi ma masanin zamantakewa Johan Galtun a wata mukalarsa ya bayyana cewa, rikici yana kunno kai ne daga rashin adalci da daidaito.

A halin yanzu dai, kasar Sin ta haska hanya game da komawa turbar adalci a fagen kasa da kasa, kuma tambayar da mutane da dama ke yi ita ce, sai yaushe wasu kasashe za su warke daga makantarsu ta fadar gaskiya da adalci? (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Sulhu
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
Sulhu
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
  • Sulaiman
    Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

MASU ALAKA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026

Next Post
Kasar Sin Na Maraba Da Shirin Tsagaita Wuta A Rikicin Iran

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.