ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Labarin Wakiliyar Majalisar NPC Zhao Mingcui

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Npc

A cikin tsaunin Qinling-Bashan, akwai wata ma’aikaciyar gidan waya mace dauke da jakar gidan waya kore. Ta yi tafiya har fiye da kilomita dubu 180 a cikin shekaru 30 da suka wuce. Mutane mazauna yankunan karkara suna kiranta da “mai isar da sako na cikin tsaunuka”. Ita ce Zhao Mingcui wakiliyar majalisar wakilan jama’ar Sin wato NPC a takaice, kuma ma’aikaciyar kamfanin gidan waya na kasar Sin a gundumar Shiquan na birnin Ankang na lardin Shaanxi.

Wannan hanyar wasiku ta karkara, ita ce kuma “hanyar tattara ra’ayoyin jama’a” ta Zhao Mingcui. Ta kan rubuta bukatun jama’a a cikin wani littafi a kan hanyarta na aike da wasiku da kaya: Wadanne tsofaffi ke da wahalar samun magani, a wane kauye ne hanya ba ta da kyau, wane yanki ne na tsaunuka ba shi da kyakkyawar hanyar sadarwa. Wadannan ra’ayoyi daga mazauna tsaunuka sun zama shawarwarin da za ta bayar a taron majalisar NPC.

A cikin shekaru 8 da suka gabata, Zhao Mingcui ta gabatar da shawarwari sama da 80, wajen tarukan shekara-shekara na majalisar. Abubuwan da ta dade tana kula da su kamar hadewar ayyukan jigilar kayayyaki da wasiku da kwashe fasinja, sun kasance cikin muhimman ayyuka na shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14, inda aka mai da muhimmanci kan zamanintar da kauyuka da karkara. Ma’aikatar gidan waya ta kasar Sin, a shekara ta 2024, a cikin martaninta ga shawarwarin Zhao Mingcui, ta bayyana cewa, takardun kasa kamar shirin zamanintar da aikin noma da kauyuka sun karfafa kamfanonin gidan waya da na jigilar kaya da su himmantu wajen yada ayyukansu a yankunan karkara.

ADVERTISEMENT

A bana ita ce shekarar farko da ake aiwatar da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, kuma Zhao Mingcui ta mayar da hankali kan batun kariyar samfuran abubuwan gargajiya na gida kamar su maganin da ake kira Gynostemma Pentaphyllum na gundumawar Pingli da siliki na gundumar Shiquan na Shaanxi, tana yin kira da a kara dakile jabun kayayyaki. An mika wannan shawara ga taron majalisar NPC na 2026 a hukumance, kuma a halin yanzu hukumomin da abin ya shafa suna nazarinta.

“Daga tsaunuka zuwa zauren taron jama’ar Sin, na kwashe shekaru 30 ina tafiya.” Zhao Mingcui ta ce, “Ni ce wakiliyar jama’a, na fi sanin abin da jama’a ke fata. Tabbatar da hakkin wakilan majalisar NPC ba aiki na wadannan kwanakin da aka gudanar da taron kawai ba ne, aikin kowace rana ne.”

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Labarin Zhao Mingcui shi ne wani misali na tsarin dimokuradiyyar dake shafar kowa da kowa iri na Sin: dimokuradiyya tana cikin shawarwarin wannan ma’aikaciyar gidan waya, wadda ke wakiltar bukatun jama’a.

Kamar yadda ta ce: “Abin da jama’a ke fata shi ne, rayuwarsu ta kara kyau kowace rana.” An yi imanin cewa a shekaru biyar masu zuwa, za a tabbatar da karin shawarwarin wakilan majalisar NPC, kuma rayuwar jama’a za ta inganta kowace rana.(Mai zane da rubutu: MINA)

Npc
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Npc
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Mutane 7 Ne Suka Rasu Sakamakon Zazzabin Cizon Sauro Da Taifod Ba Wata Sabuwar Cuta Ba – Gwamnatin Kano

Matasa Biyu Sun Afka Tafkin Ruwa Yayin Tserewa Masu Ƙwacen Waya A Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.