ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Labarin Yin Yuzhen: Sin Tana Hadin Gwiwa Da Ketare Don Cika Alkawarin Kiyaye Muhallin Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Yuzhen

Yau Juma’a 5 ga wata, ita ce ranar kiyaye muhalli ta duniya. A yau, ina so in ba ku labarin yadda wata ’yar kauyen Sin ke cika alkawarin kiyaye muhalli da ta yi wa abokinta dan kasar Amurka.Yin Yuzhen ‘yar kauyen Sala Wusu dake karkarar birnin Ordos na kasar Sin ce. A shekara ta 1999, ta sha alwashin cewa “zan yi iyakacin kokarin dasa bishiyoyi, don kada hamada ta kawo min wata barazana”.

Shi ya sa ta fara dasa bishiyoyi a hamadar Mu Us ta yankin Mongolia ta gida na kasar Sin. A lokacin, wani malami dan kasar Amurka mai suna Ronald Sakolsky da ke koyarwa a wata makarantar sakandare a Sin, ya ga labarin yadda Yin Yuzhen ta dukufa kan sha’anin dasa bishiyoyi don magance kwararowar hadama a Mu Us, abin da ya burge shi sosai.

Saboda haka, ya yanke shawarar taimaka mata, kuma a karshe ya tara dalar Amurka 5,000, ya ba ta. A wancan lokacin, dala 5,000 kudi ne mai yawa ga Yin Yuzhen, wanda zai iya biyan bukatun iyalinta na gina gida da kai yara makaranta, har ma da canza rayuwar dukan iyalinta. Duk da hakan, Yin Yuzhen ta yi amfani da kudin wajen sayen tsirran bishiyoyi, ta dukufa kan aikin kyautata muhallin hamada. Bisa kokarinta, wadannan bishiyoyi sun girma zuwa itatuwa sama da 50,000, kuma hamadar ta zama koren fili a yau.

ADVERTISEMENT

Wannan labari ya burge mutane da yawa, domin aikin kare duniyarmu muradun daukacin bil’adam ne da ya wuce iyakokin kasa. Daga yanayin “hamada ta kori mutane” zuwa “bishiyoyi ta kori hamada”, alkawarin Yin Yuzhen ga Sakolsky na tsawon shekaru 27 yana gaya mana cewa, kare muhalli ba shi da iyaka, kuma ci gaban kiyaye muhalli yana bukatar hadin gwiwar al’ummun duniya. Lokacin da mutane daga kasashe daban-daban suka yi aiki tare don kiyaye muhalli, tunani na “samun jituwa tsakanin mutum da halittu” ba zai kasance mai nisa ba.

Kwanan nan, Yin Yuzhen ta yi kokarin neman Sakolsky ta yanar gizo kuma ta yi hira da shi ta hanyar bidiyo. Yin Yuzhen ta fada wa Sakolsky cewa, “Bisa gudunmawar da ka bayar, na dasa bishiyoyi. Yaushe za ka zo ka duba?” Sakolsky mai shekaru 69 ya amsa cewa, “Zan yi iyakacin kokarina, ina so in neme ki don ni ma in dasa bishiya.” Yayin da ake bikin ranar muhalli ta duniya, wannan alkawari tsakaninsu ya shaida ainihin matakin da bil’adam ke dauka na kare muhallin duniyarmu.(Mai zane da rubutu: MINA)

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Yuzhen
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Yuzhen
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Abubuwan Da Ba A Fada Ba Game Da Sace Janar Rabe Abubakar A Katsi

Abubuwan Da Ba A Fada Ba Game Da Sace Janar Rabe Abubakar A Katsi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.