ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ba A Fada Ba Game Da Sace Janar Rabe Abubakar A Katsi

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Janar

Babbin bayanai sun bayyana kan yadda ‘yan bindiga suka sace tsohon Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar Batsari (mai ritaya), tare da matarsa a Jihar Katsina a ranar Asabar.

Rahotanni sun nuna cewa Janar din mai ritaya na kan hanyarsa ta zuwa Katsina ne tare da matarsa, Hajiya Amina Abubakar, da direbansa, Abdullahi Sa’idu, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke Karamar Hukumar Matazu.

Lamarin ya faru ne kusa da kauyen Zakin Baure, inda shaidu suka ce wasu mahara da ake zargin ‘yan bindiga ne suka fito daga maboyarsu, suka tare hanya tare da bude wuta kan motar. Hakan ya tilasta motar tsayawa, kafin su yi awon gaba da Janar din mai ritaya da matarsa zuwa cikin daji.

ADVERTISEMENT

Wasu majiyoyi da suka san yadda lamarin ya faru sun shaida wa Daily Trust cewa an harbi direban a hannu yayin harin, amma daga baya maharan suka bar shi ba tare da sun tafi da shi ba.

“Sun harbe shi a hannu sannan suka bar shi, amma suka tafi da Janar din da matarsa. Ya zubar da jini sosai, amma daga baya ya samu taimako kuma an yi masa magani,” in ji wata majiya da ke kusa da iyalan wadanda aka sace.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Daga baya jami’an tsaro sun gano motar da aka yi amfani da ita, kuma suka kai ta Hedikwatar ‘Yansanda ta Matazu yayin da ake ci gaba da bincike da kuma kokarin ceto wadanda aka sace.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana harin a matsayin kwanton bauna da aka shirya sosai.

“Maharan sun tare hanya suna jiran motoci. Komai ya faru cikin sauri. Suna da yawa kuma suna dauke da manyan makamai. Mutanen yankin ba su iya tsoma baki ba saboda tsoro,” in ji shi.

Wata majiya ta kuma ce tun da farko maharan sun kai hari wani wurin cajin waya a kauyen, inda suka kwashe wayoyin hannu da dama da kuma batir masu ajiye wuta (power banks).

“Sun kuma kwace babur din wani mazaunin kauyen. Bayan haka suka koma kan hanya, inda suka ci karo da wata jar mota, suka bude mata wuta,” in ji majiyar.

Lamarin ya ja hankalin jama’a sosai bayan da mazauna yankin suka wallafa hotunan motar Fijo ja da aka bari a wurin a kafofin sada zumunta tare da rubuta: “Wa ya san mai wannan mota? An yi garkuwa da mutanen da ke cikinta a kan hanyar Matazu.”

Yayin da sakon ya bazu a kafofin sada zumunta, wani tsohon jami’in soja ya bayyana cewa mutanen da aka sace su ne Manjo Janar Batsari (mai ritaya) da matarsa, lamarin da ya jawo damuwa sosai.

Sai dai wasu majiyoyi a yankin Matazu sun yi imanin cewa maharan ba su san cewa daya daga cikin wadanda suka kama tsohon babban jami’in soja ne ba.

Mazauna yankin sun ce watakila Janar Batsari ya yi wannan tafiya ne saboda a baya-bayan nan an samu dan ingantuwar tsaro a yankin idan aka kwatanta da wasu sassan jihar da suka dade suna fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Majiyar ta ce Muhammadu Fulani sanannen dan bindiga ne mai taurin kai da yawan alfahari, wanda ke son a san da zuwansa duk lokacin da ya kai hari.

“Idan ya kai hari, yawanci barnar da yake yi tana da muni sosai, kuma tana barin al’ummomi cikin tsoro da jimami. Wannan harin da ya faru bai yi kama da aikinsa ko na mabiyansa na kusa ba,” in ji majiyar.

Wani mazaunin kauyen Sayaya ma ya bayyana irin wannan shakku, inda ya ce bayanan da ake da su sun nuna cewa wadanda suka yi garkuwar ba su san ainihin mutanen da suka kama ba a lokacin harin.

A cewarsa, yadda aka gudanar da aikin ya nuna cewa masu garkuwar na iya kasancewa wata kungiyar masu laifi daban da ke aiki a yankin, ba ta Muhammadu Fulani ba.

“Daga bayanan da muka samu, masu garkuwar ba su ma san cewa sun tare tare da yin garkuwa da wani tsohon babban jami’in soja ba. Sun yi kama da masu aikata laifi da ke amfani da damar da ta samu ne kawai, ba kamar mambobin wata sananniyar kungiyar ‘yan bindiga ba,” in ji mazaunin.

Ya kara da cewa adadin maharan ya yi kasa idan aka kwatanta da dimbin mayakan da aka saba gani tare da Muhammadu Fulani lokacin da suke kai hare-hare.

“Sun yi aiki ne kamar kananan masu laifi. Ba su da yawa kamar mayakan da ke rakiyar mutanen Muhammadu Fulani idan sun fito kai hari. Motar ja ce kadai a wurin, saboda haka ita ce kawai ta zama abin hari.

“Tabbas yana yiwuwa kungiyoyin masu laifi su canja dabarunsu a tsawon lokaci, amma daga abin da muka sani, wannan aiki bai yi kama da na Muhammadu Fulani da muka sani ba, wanda aka fi sani da mugunta, kisa da rashin tausayi,” in ji mazaunin.

Janar
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
An Fitar Da “Rahoton Yanayin Muhalli Na Kasar Sin Na 2025”

An Fitar Da “Rahoton Yanayin Muhalli Na Kasar Sin Na 2025”

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.