Laberiya ce ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta amince ta karɓi baƙin da Amurka ta kora, inda ake sa ran irin waɗannan baƙi guda 20 za su isa ƙasar gobe Alhamis.
Gwamnatin Laberiya ta ce ta amince ta karɓi baƙin da suka kai 1,200 a ƙarƙashin shirin Amurka na tura baƙin da ta kora zuwa wasu ƙasashe na daban.
A watan Satumban bara, gwamnatin Laberiya ta amince ta karɓi baƙi waɗanda ƴan asalin ƙasashen Afirka ne da kuma ƴan asalin ƙasashen yankin nahiyar arewaci da kudancin Amurka na shekara ɗaya, bisa dalilai na jin-ƙai.
Ma’aikatar yada labarai ta ƙasar ta fitar a wata sanarwa cewa ba za a bai wa ƙasar wata lada ba a sanadiyyar hakan sai dai za a taimaka mata wajen tabbatar da samun nasarar shirin da kuma ƙarfafa harkar shige da ficenta.
Haka nan kuma gwamnatin ƙasar ta Laberiya ta ce za a bai wa baƙin damar neman mafaka a ƙasar idan suna buƙata, kuma za su iya ci gaba da zama a ƙasar idan suna son hakan.
Aƙalla ƙasashen Afirka 10 ne suka amince su karɓi baƙin da Amurka ta kora a ƙarƙashin shirin gwamnatin Donald Trump na tura baƙi zuwa wasu ƙasashe na daban.














