ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Layin Dogo Na TAZARA: Shaida Ce Ta Abota Da Ta Wuce Rabin Karni

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
TAZARA

Ranar 5 ga watan Afrilu ita ce ranar bikin gargajiya ta Sinawa na tunawa da magabata, wato bikin Qingming. A ranar ta wannan shekara, an gudanar da wani biki na musamman don tunawa da ma’aikata Sinawa da suka rasa rayukansu, yayin ginin layin dogo na TAZARA, wanda ya hada kasashen Tanzania da Zambia. David Robert, yaro dan kasar Tanzaniya mai shekaru 11 ya tsaya a gaban kaburburan kwararrun kasar Sin da suka sadaukar da rayukansu, ya kalli sunayen Sinawa da aka sassaka a kan dutsen kaburburan, ya ce: “Na karanta layin dogo na TAZARA a makaranta, malamina ya ce, ya kasance alama ta abota tsakanin Sin da Tanzaniya.”

Bikin ya tuna min da abin da ya faru lokacin da na yi ziyara a kasar Zambia a watan Fabrairun wannan shekara. Lokacin da na je wurin tunawa da layin dogo na TAZARA don karrama ma’aikata Sinawa da suka sadaukar da rayukansu wajen gina wannan layi, wadanda aka binne a can, na sadu da wani dalibi mai ziyara, wanda ya ce mini: “Mun koya a makaranta cewa, Sinawa ne suka taimaka mana wajen gina wannan layin dogo, wannan ita ce ‘hanyar abota’.” Ban sami damar tambayar sunansa ba, sai ya yi murmushi ya tafi, amma na san cewa yawancin yaran Zambia irinsa suna rike da abokantaka tsakanin Zambia da Sin a zukatansu.

Wata hasumiyar tunawa na tsaye a tsakiyar wurin tunawa da layin dogo na Tazara, tana wakiltar abota tsakanin kasashe uku na Sin da Tanzaniya da Zambia.

ADVERTISEMENT

A cikin shekarun 1970, bayan da kasashen yamma suka ki amincewa da bukatar Tanzaniya na gina mata layin dogo saboda “rashin fa’idar tattalin arziki”, dubban ma’aikata Sinawa sun tafi Afirka, inda suka yi aiki kafada da kafada da mutanen Tanzaniya da Zambia don gina layin dogo na TAZARA. Duk da yanayi mai zafi, cututtuka da karancin kayayyaki, sun kai ga shimfida wannan layin dogo da ya hada kasashen da ke nisa da teku da tashar ruwa.

Bayan kammala wannan layin dogo mai tsawon kilomita 1,860.5, ya samar da sabuwar hanyar fita zuwa teku ga Zambia da sauran kasashen Afirka da ke da nisa daga teku, ta yadda albarkatun kasashen sun zama karfin bunkasa tattalin arzikinsu, matakin da ya sa kasashen suka yi watsi da tarnakin da aka yi musu ta fannin tattalin arziki tare da samun ‘yanci na gaske. A lokacin gina shi, ma’aikata Sinawa 51 sun rasa rayukansu. Saboda hakan, ana kira layin dogon “hanyar ‘yanci” da “hanyar abota”.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A bana ake cika shekara ta 50 da fara aiki da wannan layin dogo. A ranar 20 ga watan Nuwamban bara, an gudanar da bikin kaddamar da aikin sabunta wannan layin dogo a Lusaka na Zambia. A halin yanzu, kamfanin CCECC na kasar Sin yana jagorantar ayyukan gine-gine masu alaka.

A sabon mafari na tarihi, ba za a manta da jaruman da suka sadaukar da rayukansu wajen gina layin dogon ba, kuma abota tsakanin Sin, Tanzaniya da Zambia ba za ta dushe ba. Kamar yadda ministan harkokin cikin gida na Tanzaniya George Katambi ya fada a bikin tunawa: “Wadannan jarumai ba wani bangare na tarihi kadai ba ne, har ma wani bangare ne na makomarmu.” (Marubuci:MINA)

TAZARA
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
TAZARA
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.