ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

by Muhammad
5 months ago
ADC

Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na Jam’iyyar (ADC) ya yi watsi da bangarorin jam’iyyar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da kuma Rabiu Bala Gombe ke jagoranta, inda ya bayyana su a matsayin waɗanda ba su da inganci a bisa tsarin doka.

Da yake ganawa da manema labarai bayan taron NEC da aka gudanar a Abuja ranar Talata, Shugaban jam’iyyar na Jihar Abia, Don Norman Obinna, ya ce bangarorin biyu sun kasa cika sharuddan kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ake buƙata domin jagoranci.

  • Ɗimbin Magoya Bayan Jam’iyyun APC, NNPP Da PDP Sun Koma ADC A Jihar Jigawa
  • 2027: ADC Na Duba Yiwuwar Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Ta Hanyar Yarjejeniya — Kakakin Jam’iyya

Obinna ya bayyana cewa NEC, wanda ya ce ya ƙunshi shugabannin jihohi 20, ya nuna damuwa kan abin da ya kira tsoma bakin wasu mutane da ba su da cikakkiyar fahimta kan harkokin cikin gida na jam’iyyar.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Mun kalli abin da ke faruwa cikin mamaki, yadda wasu ‘yan kaɗan, waɗanda ba su da cikakkiyar fahimta kan batutuwan jam’iyyar, suka riƙa ɗaukar matakai bisa son rai ba tare da tunani da ilimi ba.”

Kwamitin NEC ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato (INEC), ta ɗauka na ƙin amincewa da ikirarin shugabanci daga bangarorin David Mark da Bala Gombe.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Da yake ƙarin bayani, Obinna ya ce wa’adin tsohon Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Ralph Nwosu, ya ƙare ne tun watan Agustan 2022, amma ya ƙi sauka daga mukaminsa, lamarin da ya jawo jerin shari’o’i a kotu.

A cewarsa, wani hukunci da Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke a watan Disamban 2022 ya tabbatar da cewa wa’adin Nwosu ya ƙare, don haka dukkan matakan da ya ɗauka tare da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa ba su da inganci, kasancewar ba su samu amincewar NEC ba.

Ya ce, “Wa’adin Ralph Nwosu a matsayin Shugaban Ƙasa ya ƙare a watan Agustan 2022. Rashin saukarsa ne ya haifar da shari’o’i da dama. Hukuncin kotu na watan Disamba ya tabbatar da cewa wa’adinsa ya ƙare, kuma duk wani mataki da ya ɗauka bayan haka ba shi da inganci.”

Biyo bayan waɗannan abubuwa, NEC ya sanar da naɗa Kwamitin Ayyuka na Ƙasa na riƙo domin tafiyar da harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron ƙasa.

Kwamitin ya naɗa Ogga Temitope Kingsley, shugaban jam’iyyar a Jihar Kogi, a matsayin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa na riƙo, yayin da aka naɗa Odion O. Kennedy daga Jihar Edo a matsayin Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa na riƙo.

Kwamitin na riƙo, wanda ya ƙunshi mutum takwas daga cikin shugabannin jihohi, an ba shi wa’adin makonni biyu domin tafiyar da harkokin jam’iyyar tare da tabbatar da miƙa mulki cikin sauƙi ga sabon shugabancin da za a zaɓa.

ADC
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Bangaren Sin Ya Yi Kira a Bai Wa Kasashe Masu Tasowa Muhimmanci Yayin Yi Wa MDD Kwaskwarima

Bangaren Sin Ya Yi Kira a Bai Wa Kasashe Masu Tasowa Muhimmanci Yayin Yi Wa MDD Kwaskwarima

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.