ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lokacin Da AI Ta Ba Da Umarnin Kai Harin Kisan Yara

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
AI

Masu sauraro, ko kun taba kallon fim din Amurka mai taken Terminator? Fim da ya bayyana mana labarin yadda tsarin kirkirarriyar basira na amfanin soja da ake kira SKYNET ya mai da ’yan Adam a matsayin barazana a gare shi, har ma ya haifar da mummunar masifa gare su ta hanyar kaddamar da hare-haren nukiliya. Ko da yake kagaggen labari ne, amma bisa saurin bunkasar fasahar kirkirarriyar basira wato AI, labarin ka iya zama gaskiya, musamman ta yin la’akari da yadda a kwanan baya ma’aikatar tsaron Amurka ta sanya kamfanin Anthropic na kasar cikin jerin kamfanonin da ke “barazana ga tsarin samar da kayayyaki”, sakamakon yadda kamfanin ya tsaya ga kin yarda da yin amfani da fasahar AI wurin sa ido a kan al’ummar Amurka da kuma makaman da ba dan Adam ke sarrafa su ba.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a watan Yulin shekarar 2025, ma’aikatar tsaron Amurka ta amince da kwangila mai darajar dala miliyan 200 da kamfanin Anthropic, inda ta shigar da tsarin Claude da kamfanin ya samar cikin tsarin AI na Maven, don sarrafa bayanan da suka shafi ayyukan soja, lamarin da ake kallonsa a matsayin wani mataki mai muhimmanci da kamfanonin fasahar AI ke fara sa hannu a cikin tsarin kasar na yanke shawara a kan yaki.

Wani nazarin da jami’ar Georgetown ta Amurka ta yi ya shaida cewa, ta hanyar shigar da tsarin Claude cikin tsarin Maven, runduna mai sojoji 20 ta iya kammala ayyukan da a baya ke bukatar sojoji 2000 wajen aiwatarwa. Hakikanin abin da ya faru ma ya shaida yadda fasahar AI ta yi matukar inganta ayyukan sojojin Amurka. An ce, a matakan soja da Amurka ta dauka a kan Iran a wannan karo, Amurka ta yawaita amfani da fasahohin AI da kamfanin ya samar, inda cikin sa’o’i 24 da aka kaddamar da yaki, Amurka ta kai hare-hare kan abubuwa kimanin 1000 na kasar Iran, adadin da ya ninka na matakan soja da ta kaddamar a kan Iraki a shekarar 2003 har sau biyu. Lallai an tsara tsarin Maven ne don ya tattara bayanai daga sassa daban daban, a yayin da Claude zai kara sarrafa bayanan don dan Adam ya samu saukin nazari a kai, ta hakan za a kai ga inganta aikin. Sai dai sakamakon yadda tsarin Claude shi ma ya sa hannu a aikin zabar abubuwan da za a kai wa hari da kuma jera su, ya kuma sa hannu a aikin yanke shawara da ya kamata dan Adam ya yi. Harin da sojojin Amurka suka kai makarantar firamare da ke garin Minab na kudancin Iran da ya halaka yara mata sama da 160 ya shaida hakan, duba da cewa gazawar sojojin Amurka ta fannin leken asari da ma kuskuren da AI ta yi wajen yanke shawara ne suka haifar da hakan.

ADVERTISEMENT

Lallai, shin ya kamata a shigar da fasahar AI cikin yaki? Kuma ko ya kamata a kayyade yin amfani da AI wajen yanke shawara? In dai har fasahar AI ke ba da umarnin kai hare-hare, wace mummunar makoma dan Adam zai fuskanta? Bisa ci gaban fasahar AI, tsarin yin amfani da fasahar AI da kuma kulawa da ita ya kara janyo hankulan al’umma, kuma abin da ya faru tsakanin gwamnatin Amurka da kamfanin Anthropic ya kara haifar da damuwar al’umma.

A cikin shekarar da ta gabata, gwamnati mai ci ta Amurka ta yi watsi da manufar “AI mai tsaro da ake iya dogara da ita da kuma amincewa da ita”, kuma ta sanya “cimma nasarar takarar da ake ta fannin AI” a matsayin burin da take neman cimmawa, tare da sanya aikin cimma nasarar yaki da sauran kasashe a wani muhimmin matsayi, matakin da ya sa aka sake “shata iyaka ga fasahar AI”. Sai dai, matukar dai za a yayata irin wannan ra’ayi na ba da fifiko ga cimma nasarar yaki, to, masifa mai muni ce za a fuskanta.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Idan har ba a kayyade amfani da fasahar AI ta fannin soja ba, kuma a mai da AI a matsayin kayan aiki na ruguza mulkin kai na wata kasa, ko kuma a bar AI ta samu ikon yanke shawarar kashe mutane, lallai labarin fim din Terminator zai kara saurin zama gaskiya.

Kullum kasar Sin na nacewa ga bin ka’idar amfani da AI mai taken “don amfanar da jama’a kuma ta fannonin da suka dace”. A ganin kasar, ya kamata dan Adam ne ya jagoranci AI, kuma tana kin yarda da yin amfani da AI da sauran fasahohin zamani wajen neman nuna fin karfin soja, har da barazana ga sauran kasashe. Mabambantan zabi da ake yi wajen yin amfani da fasahar AI za su haifar da mabambantan sakamako, amma tabbas kasar Sin za ta yi zabin da ya sha bamban da na Amurka. Kasar Sin tana son hada kai da kasa da kasa wajen inganta tsarin kulawa da fasahar AI a karkashin MDD, don tabbatar da cewa bunkasar AI ta amfani ci gaban dan Adam.

AI
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
AI
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Buƙaci Sufeton 'Yansanda Ya Binciki Kashe-kashen Rayuka a Filato

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.