Rahotannin da aka ruwaito sun ce, a ranar 7 ga watan nan, kasar Indiya ta sanar da wai “daidaitattun sunaye” na wasu wurare 27 na “Arunachal Pradesh”. Kuma ma’aikatar cikin gidan kasar Indiya ta sanar da cewa, buga sunayen wuraren a taswira, zai taimaka wa al’umma kara fahimtar wuraren.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 10 ga watan nan cewa, yankin Zangnan, yanki ne mallakin kasar Sin, kuma kasar ba ta taba yarda da wani yanki mai suna wai “Arunachal Pradesh” da Indiya ta kafa ba. Yunkurin da Indiya ta yi na bullo da wai “daidaitattun sunaye” don maye gurbin sunayen wuraren da Sin ta dade tana amfani da su, abu ne da ya saba wa doka kuma mara amfani, kana, ba zai sauya gaskiyar al’amarin ba, wato Zangnan yanki ne mallakin kasar Sin. (Murtala Zhang)














