Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta Sin, Huang Ling ta bayyana cewa, bangaren Amurka ya kaddamar da bincike na sashe 301 ga kasashe masu karfin tattalin arziki guda 16 ciki har da Sin bisa hujjar “Samar da kayayyaki fiye da kima”, wanda ya siyasantar da batun tattalin arziki da ciniki, tana cewa aiki ne da ya nuna ra’ayin bangaranci da kafa shinge, kuma bangaren Sin yana adawa da hakan.
Ta kara da cewa, Sin za ta ci gaba da sa ido sosai da kuma tantance matakan da bangaren Amurka zai dauka a nan gaba, kuma yana da ikon daukar dukkan matakan da suka wajaba.Huang ta bayyana hakan ne a gun taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar yau Alhamis, yayin da take amsa tambaya game da shirin gwamnatin Amurka na kara harajin kwastam na kashi 7.5% kan kayayyakin da Sin ke shigarwa kasar.
Da ta ambaci nasarorin da aka samu a fannin hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da sauran kasashe mambobin kungiyar SCO, Huang Ling ta bayyana cewa, a cikin shekaru 25 da suka gabata bayan kafa kungiyar, yawan cinikayya tsakanin Sin da sauran kasashe ya karu daga dalar Amurka biliyan 12.1 a shekarar 2001, zuwa dalar Amurka biliyan 523.5 a shekarar 2025, wanda ya kai kashi 8% na jimillar cinikin da Sin ke yi.
Bugu da kari, Huang Ling ta ce hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasar Kyrgyzstan ya ci gaba da bunkasa cikin kwanciyar hankali, wanda ya samar da sakamako masu kyau a fannoni daban-daban. (Safiyah Ma)














