Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian ya jagoranci wani taron manema labarai na yau da kullun. Da yake amsa tambayoyi game da mu’amalar matsayin koli tsakanin Sin da Amurka, Lin Jian ya bayyana cewa bangarorin biyu suna ci gaba da tuntubar juna game da batun mu’amala tsakanin shugabannin kasashensu a bana.
Dangane da ikirarin da hukumomin Amurka suka yi kwanan nan na zargin hare-haren yanar gizo daga masu satar bayanai a kwamfuta na Sin, Lin Jian ya ce kalaman da bangaren Amurka ya fitar ba su da tushe kuma suna jirkita gaskiya. Sin ta nuna rashin gamsuwa da kuma adawa da yadda bangaren Amurka ke amfani da batutuwan tsaro na yanar gizo don bata mata suna.
Bugu da kari, dangane da dangantakar Sin da Japan, Lin Jian ya bayyana cewa dalilin haifar da manyan matsalolin dake cikin dangantakarsu a halin yanzu yana shafar maganganu da ayyukan da hukumomin Japan suka yi kan batun Taiwan da kuma fannin tsaro.
Ya ce ya kamata manyan jami’an Japan su yi tunani sosai kan wadannan kurakurai, sannan su dauki matakai na zahiri don kare tushen siyasa na dangantakar Sin da Japan.(Safiyah Ma)














