ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisun Dokokin Jihohi Sun Goyi Bayan Kafa ‘Yansandan Jiha

by Idris Aliyu Daudawa
3 months ago
Jihohi

Shugabannin majalisun Jiohi a karkashin, kungiyar shugabannin majalisun Nijeriya (CSSLN), sun ba da nasu goyon bayan dangane da lamarin kirkirar ‘yansandan Jiha.

Sun bayyana cewa maganar kafa ‘yansandan jiha, ai tun tuni ne ya dace ace an kafa ta saboda yadda lamarin tababarewar tsaro yake a fadin Nijeriya, don haka  ya ce, ba abu ne maikyau ace an ki amincewa da shawarar yin hakan.

  • An Yi Musayar Kwarewa Game Da Ayyukan Rage Talauci Ga Masu Bukatar Musamman Na Sin a Dandalin FAO
  • Za a Gudanar Da Tattaunawa Kan Batun Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka a Faransa Daga Ranar 14 Zuwa 17 Ga Watan Maris

Maganar kafa ‘yansandan jihar makon da ya gabata ta kara samun tagomashi yayin da sabon Shugaban rundunar ‘yansanda ta kasa, wanda aka rantsar makon da ya gabata, Tunji Disu, ya ba da  tashi amincewar inda ya kafa kwamitoci domin   su gano hanyoyin da za’a bi na kafa su.

ADVERTISEMENT

Disu, wanda ya  yi hira  ne da masu daukar labaranfadar Shugaban kasa jim kadan bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi a matsayin Shugaban rundunar ‘yansanda na 23 a fadar Shugaban kasa,  ya ce maganar samar da ‘yansandan Jihohi wani abu ne da za a iya kira da “tsari ne wanda lokacin shi ya yi.”

Kafin dai a samu zuwa wannan lokacin da halin da ake ciki, Tinubu ya yi kira da majalisun kasa su ba lamarin taimako na shari’a.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

An samu mabambanta ra’ayoyi akan maganar da sabon Shugaban rundunar ‘yansanda ta kasa ya yi. Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), Afenifere, da takwarar ta, ta kudu maso kudu, da kungiyar sashen masu arzikin manfetur (Pan Niger Delta Forum), sun goyi bayan lamarin na ‘yansandan Jiha.

Duk da yake dai ita maganar ‘yansandan Jiha an dade ana yin ta lokaci mai tsawo, tana bukatar gyaran tsarin mulki ne domin a samu cimma burin na kafa ta, domin kuwa ai abin ya shafi Jihohi 36 na Nijeriya.

Shugaban kungiyar ya bayyana ra’ayin sa

Shugaban kungiyar CSSLIN,Honorabul Emomotimi Dennis Guwor ya bayyanawa LEADERSHIP a hirar da ya yi da ita ranar Lahadi ta makon da ya gabata, inda ya ce wani lamari ne wanda  ya dace ace ya zuwa halin da ake ciki, an gama shi, ba ma kamar idan aka  yi la’akari da irin halin  tabarbarewar  tsaro da Nijeriya ta ke fuskanta yanzu, tun da ‘ yan Nijeriya sun yi maraba da shi lamarin.

Kamar dai yadda Shugaban ya ce,Tinubu  tuni ne ya kalubalanci wadanda suke da ruwa da tsaki“su fara tunanin hanya mafi dacewa da ta kamata ayi gyaran shi tsarin mulkinsaboda a samu damar sa lamarin  ‘yansandan Jiha ko, a samu dama ita kasar Nijeriya ta samu zaman lafiya wanda ya dace, ko su fara aiki a dazuzzukan mu,a samu ceto daga masu cutar da su, ya kasance tsoro ya fita daga idon mutane.”

Ya ce kungiyar ta Shugabannin majalisun Nijeriya ba su da wata matsala su, suna goyon bayan lamarin ba tare da wata matsala ba.

“Yawancin ‘yan Nijeriya da wasu kungiyoyi a shekaru ashirin da suka gabata sun fara maganar duk kuma daya ce da ta shafi ‘yansanda Jiha, hakan yana nuna matukara aka kafa ‘yansandan na Jiha ita ce hanya da ta fi dacewa wadda a dalilin yin haka nana iya samun ci gaba da kuma bankwana da rashin tsaron da ake fama,  kamar yadda ya ce,”.

Guwor, wanda har ila yau shi ne Shugaban majalisar Jihar Delta, majalisar Jihar, sun bada tabbaci da ke nuna cewar ba za ta yi wasa da lamarin ba, tun da yake yanzu shi ne ya dawo da maganar .

Zai iya tunawa majalisar dattawa sun tabbatawar ‘yan Nijeriya cewa za su yi ma lamarin na ‘yansanda  Jiha duk yadda ya dace, ba za su yi wasa da shi ba, domin abu ne muhimmi, ba za su bari abin ya shiga wani hali ba,za su dauki abin da muhimmaci saboda kuwa ai sun san lamari ne da bai son bata lokaci, da zarar an tura  ma su ‘yan majalisa nan da nan za su yi abinda ya fi dacewa da  lamarin.Ba za su  sa ido har ace an fara yin kamfe na siyasa.

Ya yi kira da masu ruwa da tsaki da su yi duk abubuwan da suka dace da suka san za su taimakawa kokarin da suke yi,kada su sa wata  gazawa tare da su, idan kuma an kai ga kirkiro su ‘yamsanda na Jihohi kada ayi amfani da su wajen cimma burin da ya wuce na harkar tsaro, a kuma tanaji hukunci  mai tsauri da zai hana yin amfani da su ta hanyar da bata kamata ba.

Don haka ne ma ya tuna da, da irin maganar da mai magana da yawun ‘yan majalisar dattawa , Sanata Yemi Adaramodu, ya yi “ Za mu yi duk abinda ya dace mu yi dangane da lamarin; muna bada tabbacin kafi karshen wannan shekarar, za mu yi duk gyare- gyare da suka kamata, wabda hakan ne za mu samu dama ta kirkiro’yansandan Jiha.”

Guwor  ya ce ita maganar  tsarin ‘yansandan Jiha babu wata matsala ba ce ta kanta saboda ana iya amfani da ita domin taimakawa al’umma.

“Maganar gaskiya matsalar ita ce Nijeriya ba kasafai ake yin abubuwa kamar yadda doka ta shinfida ba, inda kuma ba’a kiran mutane su yi bayani akan abubuwan da suka yi da basu dace ba. Hakanan a wurin da ba ‘a iya daukar mataki na hukuntawa kan wadansu abubuwan da aka ki yi hakanan,a irin wannan hali masu irin wadancan halayen za su yi dukkan abubuwan da suka dama. Hakanan ma babu wata maganar kage, ana iya yin amfani da dansanda ayi abinda aka dama ta ko wane irin hali — ko dai a karkara, Jiha ko kuma tarayya, matukar har duk wadanda suke jagorancin wuri za ‘a kyale su, su yi ta yin abubuwan da suka daman a karya doka.”

Jihohi
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

MASU ALAKA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
Labarai

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma
Labarai

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Next Post
Manyan Kamfanonin Sin Suna Zuba Karin Jari A Jihar Xinjiang Ta Kasar

Manyan Kamfanonin Sin Suna Zuba Karin Jari A Jihar Xinjiang Ta Kasar

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.