ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Sin Ta Yafe Harajin Kwastam Ga Afirka: Alfanun Abin Ya Zarce Batun Cinikayya

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Sin

Daga ranar 1 ga watan Mayun bana, kasar Sin za ta yafe wa kasashe 53 dake nahiyar Afirka, da suka kulla huldar diflomasiyya da ita, harajin kwastam kan dukkan kayayyakin da suke sayarwa a kasuwanninta. Dangane da manufar, Babajide Tella, wani malami na jami’ar Howard ta kasar Amurka ya yi tsokaci, wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na Opinion Nigeria a kwanan baya.

A cewar Mista Tella, manufar nan ta kasar Sin, da farko dai, ta ba kasashen Afirka damammakin shigar da kayayyakinsu cikin kasuwannin Sin. Za a iya sayar da amfanin gona da sauran kayayyakin da aka kera a nahiyar Afirka a kasar Sin, wadda ke da yawan al’umma da ya kai biliyan 1.4, ba tare da biyan harajin kwastam ko kwabo ba. Hakan ya nuna sahihancin kasar Sin a fannin daidaita yanayin cinikin da take yi tare da kasashen Afirka.

Ban da haka, Mista Tella ya ambaci yadda manufar Sin ta yafe harajin kwastam za ta amfani kasashen Afirka a kokarinsu na raya masana’antu. A cewarsa, tun daga lokacin mulkin mallaka har zuwa yanzu, kasashen Afirka sun dade suna fitar da danyun kayayyaki, da shigar da kayayyakin masana’antu da aka sarrafa daga sauran kasashe, lamarin da ya sa su rashin samun damar adana kudi. Sai dai sabuwar manufar kasar Sin ta yafe harajin kwastam za ta karfafa wa ‘yan kasuwa gwiwa domin a sarrafa danyun kayayyaki a kasashen Afirka kafin a fitar da su, da zummar daga darajar kayayyakin a kasuwannin kasar Sin.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, Babajide Tella ya ce manufar kasar Sin ta amfanar da kasashen Afirka ta sa kaimi ga kasashen yamma domin su daidaita manufofinsu masu alaka da nahiyar Afirka. A cewarsa, kasashen yamma na ganin cewa, matakin kasar Sin na yafe harajin kwastam zai ba kasar damar samar da karin tasiri a nahiyar Afirka. Saboda haka, kasashen yamma suna kokarin daidaita manufofinsu da suka shafi nahiyar Afirka don kara janyo hankulan kasashen Afirka, da zummar takara da kasar Sin.

To, bayan karanta bayanin da Mista Babajide Tella ya rubata, ina so in ce, na yarda da yawancin ra’ayoyinsa. Sai dai na ga kamar bai samu cikakkiyar fahimtar dalilin da ya sa kasar Sin ta kuduri aniyar yafe wa kasashen Afirka harajin kwastam ba. Sau da dama ya ambaci yadda kasar Sin ke “yin tasiri”, tamkar dai abun da kasar Sin ke nema daya ne da na kasashen yamma. Amma a hakika, ainihin dalilin da ya sa kasar Sin daukar mataki na amfanar da kasashen Afirka shi ne burin kasar na gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A ganin kasar Sin, mabambantan kasashe da al’ummu suna bukatar kasancewa tare da juna a duniyarmu. Saboda haka, a lokacin da wata kasa ke neman habaka moriyar kanta, ya kamata ta lura da damuwar sauran kasashe, da ba kasashe daban daban damar samun ci gaba na bai daya. Wannan tunani ya sa kasar Sin kullum take neman kulla huldar hadin gwiwa mai amfanarwa ga juna tare da sauran kasashe, maimakon matakan cin moriya da faduwar wani da wasu kasashen yamma suka saba daukawa.

Wannan tunani ne ma ya sa kasar Sin bude kasuwanninta ga kasashen Afirka, a lokacin da wasu manyan kasashe ke kokarin saka shingayen ciniki. Hakika matakin yafe harajin kwastam da kasar Sin ke dauka a wannan karo ya riga ya zarce tsarin ciniki da na tattalin arziki, inda ya zamanto misalin yadda kasar Sin ke kokarin samar da gudunmowa wajen gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya a duniya. (Bello Wang)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP A Kaduna, Ashiru, Zai Koma ADC A Ranar Lahadi

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP A Kaduna, Ashiru, Zai Koma ADC A Ranar Lahadi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.