ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mu Leka Yadda Sin Ke Ba Da Misali Ga Duniya Wajen Raya Aikin Noma Da Kauyuka

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
Noma

Ranar 6 ga watan Yuli ita ce ranar raya kauyuka ta duniya. An kafa wannan rana ne saboda kusan kashi 80% na mutanen da ke fama da matsanancin talauci a duniya suna zaune ne a yankunan karkara, inda suke fuskantar kalubale kamar rashin ingantattun ababen more rayuwa, yawan kaurar jama’a da talauci bisa mabambantan dalilai. Don haka, akwai bukatar zabar hanyar da ta dace wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a yankunan karkara.

Bari mu leka yadda Sin take ba da misali don samun mafita, inda bayanan hukumar kididdiga ta Sin suka nuna cewa, a shekara ta 2025, matsakaicin kudin shiga na kowane manomi ya kai Yuan 24,456, wanda ya karu da kashi 6.0% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan. Rabon kason kudin shiga tsakanin mazauna birane da karkara ya ragu zuwa maki 2.31, wanda ke nuna cewa bambancin yana raguwa na a-zo-a-gani. Yawan amfanin gona da Sin ta samar ya dade a kan matsayin kilogram tiriliyan 0.7 a kowace shekara, kuma an gina ingatattun filayen noma masu kyau sama da ekta miliyan 66.7.

Muna iya gane wa ido irin wannan ci gaba daga abin dake faruwa mai kyau na zahiri, wato a kauyen Tantou na gundumar Yudu a lardin Jiangxi, an bunkasa masana’antar kayan lambu na musamman dangane da kasa mai arzikin sinadarin Selenium, matakin da ya sa kudin shigar jama’ar kauyen ya karu daga Yuan 80,000 a shekara ta 2018 zuwa fiye da Yuan miliyan 3.5 a yauzu, inda adadin ya karu da kusan sau 44, wadannan bayanai sun zama shaida wajen samar da wata hanya da ta dace don magance talauci da kuma samun ci gaba mai dorewa a yankunan karkara a duk fadin duniya.Ci gaban kauyukan Sin ba zai rabu da ayyukan fasaha ba.

ADVERTISEMENT

Alal misali. Ana amfani da dandalin raba bayanai na barkono na dijital, a lambun shuka barkono mai arzikin sinadarin Selenium a garin Shanghu na birnin Gao’an na lardin Jiangxi, inda manoma za su iya sanin dukkan bayanan noman barkono daga wayar hannu, su kuma sarrafa wasu ayyuka daga nesa duk ta wayoyinsu.

A kauyen Xifu na gundumar Changsha na lardin Hunan, jami’ar noma ta Hunan tana aika daliban digiri na biyu sama da 100 a kowace shekara zuwa kauye bisa cibiyar fasaha da aka kafa a kauyen, inda suke horar da manoma kusan 1,500 a wurin, tare da taimaka wa manoma wajen samun karin kudin shiga har Yuan miliyan 18.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Matakin ya kyautata salon da aka dade ana bi a masana’antar noma ta gargajiya, wato aiki a gonaki kawai, ya kuma karkata zuwa sabon salo na zamani.Yawan amfani da fasahohin zamani a yankunan karkarar Sin ba wai kawai suna amfanar da mazauna kauyukan Sin ba ne, har ma suna amfanar da hadin gwiwar Sin da Afirka. A lardin Mashonaland ta Yamma na Zimbabwe, kungiyar kwararrun manoma ta Sin ta gina “gidan kaji na zamani”, inda injin kyankyashe kwai ke iya kyankyashe kajin sama da 2,000 a kowane wata.

Nomsa Ncube, wata mazauniyar kauyen, tana samun dala 320 a kowane wata ta hanyar kiwon kaji. Shugaban kungiyar kwararru Zhao Ke ya ce, “Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni”. Ban da wannan kuma, Sem, dalibi mai digiri na uku na farko da cibiyar fasaha ta Sin da Afirka ta horar, yana aiki a cibiyar yada fasahar noma a gundumar Lisasadzi na Malawi, inda yake koyar da manoma yadda ake sarrafa taki da kuma shuka daidai.

Manoman Sin na samun ci gaba bisa dogaro da yawan amfani da kimiyya da fasaha da daidaitattun matakai, kuma a kauyukan Afirka, ana samun bunakasa bisa abin koyi da Sin take kawo musu ta la’akari da halayen da suke ciki, matakin da ya kasance mafi kyawun hanyar hadin gwiwar noma tsakanin Sin da Afirka, wato samar da dabarar da za ta ba mazauna kauyuka damar dogaro da kai.

A wannan muhimmin lokaci na bikin ranar raya karkara ta duniya, abun da Sin take bayarwa ga duniya ya zama hanya mafi dacewa wajen raya yankunan karkarar duniya, kuma abin koyi ne ga hadin gwiwar aikin noma tsakanin kasashe masu tasowa.(Marubuciya: MINA)

Noma
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Noma
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Kan Ayyukan Rigakafin Ambaliyar Ruwa Da Karfafa Ceton Jama’a

Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Kan Ayyukan Rigakafin Ambaliyar Ruwa Da Karfafa Ceton Jama’a

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.