Yayin da ake gudanar da babban taro kan ilimin ginshikin kimiyya na duniya wato ICBS na shekarar 2026 a birnin Beijing na kasar Sin, wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da Mista Martin Hairer, wanda ya taba samun lambar karramawa ta Fields Medal, kana mutumin da ya halarci bikin kaddamar da taron, tare da gabatar da lambobin yabo.
A cewarsa, babban taron ya shafi fannoni daban-daban, wanda ya burge shi kwarai da gaske.Game da tasirin fasahar kirkirarriyar basira wato AI ga ilimin lissafi wato mathematics a turance, Martin Hairer ya ce, abun da masana ilimin lissafi suka mayar da hankali a kai shi ne, batutuwan da aka kasa daidaita su bisa dabaru masu sarrafa kansu.
Sai dai game da ci gaban ilimin ginshikin kimiyya na kasar Sin, Martin Hairer ya ce, a ’yan shekarun nan, gwamnatin Sin ta yi ta kara zuba kudi a bangaren ilimin lissafi da ma baki dayan bangaren ilimin ginshikin kimiyya, al’amarin da ya yi matukar burgewa. (Murtala Zhang)














