Hukumar gudanarwar Matatar Man Dangote ta nuna damuwarta kan ci gaba da bayar da lasisin shigo da man fetur daga ƙetare, duk da cewa matatar tana da isasshen ƙarfin samar da man fetur (PMS) da zai biya bukatun cikin gida na Nijeriya.
A cewar bayanan kasuwa da matatar ta samu, kusan kashi 43 cikin 100 na man fetur da aka samar wa kasuwar Nijeriya a watan Yuli, an shigo da su ne daga ƙetare. Wannan yanayin ya haifar da tambayoyi kan buƙatar ci gaba da shigo da kaya masu yawa a lokacin da ake da isasshen ƙarfin tacewa a cikin gida.
DPRP ta bayyana cewa rashin bayyananniyar hanyar sanin ainihin adadin kayayyakin da za a shigo da su Nijeriya, na ƙara wa matatar wahalar tsara samarwa da adana kaya yadda ya kamata. Matatar ta ce ajiye kaya masu yawa ba tare da cikakken sani kan yawan shigo da kaya ba, na kawo tsadar farashin ajiya kuma hakan zai iya shafar farashin kaya a kasuwa.
Matatar ta jaddada cewa ƙaruwar fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashen waje ba alama ce ta rashin sadaukarwa ga kasuwar Nijeriya ba. A maimakon haka, fitar da kaya wata dabara ce ta hankali da matatar ke amfani da ita a fuskantar gaskiyar kasuwar da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙetare ke ci gaba da yin gogayya da man da ake tacewa a gida, duk da samuwar isasshen ƙarfin tacewa na cikin gida.
Bugu da ƙari, matatar ta ce idan har wani ƙaranci ya samu sanadiyyar ruɗanin kasuwa da ake haifarwa ta hanyar yawaita shigo da kaya, ko rashin iya hasashen buƙatar cikin gida daga masu samarwa na cikin gida, to bai kamata a ɗora alhakin hakan a kan Matatar Dangote ba, wadda a koda yaushe take nuna karfinta da ƙudurinta na biyan buƙatun kasuwar Nijeriya.














