Tun daga shekarar bana, kamfanonin kasashen duniya sun ci gaba da kara zuba jari a kasar Sin, lamarin da ya nuna amincewarsu kan tattalin arzikin kasar Sin. Kuma me ya sa, kamfanonin kasa da kasa suka nuna goyon baya ga kasuwannin kasar Sin ne? Mai yiwuwa, za mu sami amsa kan wannan batu daga sabon bayanin da gwamnatin kasar Sin ta fidda game da yadda aka tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasa na watan Yuli. Ko da yake cikin watan da ta gabata, kasashen duniya sun fuskanci kalubale da kuma yanayi maras kyau cikin kasa, amma, tattalin arizkin kasar Sin na ci gaba da karuwa cikin yanayin karko. Hakan ya ba da tabbaci ga kamfanonin kasa da kasa da su ci gaba da habaka ayyukansu cikin kasar Sin.
Haka kuma, cikin cikakken zaman taro na uku na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da aka gudanar a watan Yuli, an gabatar da muhimman ayyukan inganta harkokin bude kofa ga waje da kuma raya harkokin amfani da jarin waje. Kana, bayan da aka kaddamar da jerin matakan yin kwaskwarima, kasar Sin za ta ci gaba da raya tattalin arziki don cimma burinta a fannin bunkasa tattalin arziki a bana, yayin da take samar da damammaki ga kasa da kasa.
Hakan ya sa, kamfanonin kasa da kasa da yawa sun nuna amincewa da goyon bayansu ga kasuwannin kasar Sin. (Mai Fassara: Maryam Yang)