ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?

by Abba Ibrahim Wada
2 months ago
Messi

A ranar Litinin ne danwasa Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa kwallon kafa bayan rasuwar mahaifinsa, inda a cewarsa matakin da ya dauka na ajiye takalmansa a Argentina yana da wahala amma kuma ya zama dole.

A ranar Litinin 31 ga watan Agusta kaftin din na Argetina ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa wasa. Messi zai ci gaba da buga wasa a kungiyarsa ta Inter Miami har zuwa shekarar 2028. Lionel Messi wanda ya taba lashe kofin duniya – ya ci wa Argentina kwallo 125 a raga a wasanni 207, inda ya zama danwasan da ya fi ci wa kasar kwallo a raga, duk kuwa da bajintar da Maradona ya yi a baya.

Gaba daya Messi ya ci kwallaye 921 a raga a Barcelona da Paris St-Germain da Inter Miami da kuma Argentina, kuma za a iya cewa duk da haka yana neman zura kwallaye dubu a rayuwrasa. A lokuta da dama Messi ya nuna bajinta wadda ba za a manta ba, musamman wasan hamayya na El-Clasico Messi ya fara zazzaga kwallaye uku rigis wato ‘hat-trick’ a karawa da Real Madrid. Messi ya ci kwallayen ne yana shekara 19, kuma duk shi ya ci wa Barcelona kwallayenta a ragar Real Madrid da suka tashi 3-3 a wasan Clasico a ranar 10 ga Maris na 2007.

ADVERTISEMENT

Karon farko da ya ci kwallo uku rigis a raga a Camp Nou gidan Barcelona – musamman kwallo ta uku da ya ci bayan ya yanke ‘yanwasan bayan Madrid. Kuma tun daga wannan lokaci ne Messi ya fara jan hankalin duniya. Sannan wata daya bayan ya ci kwallaye uku rigis, Messi ya ci wata kwallo a raga da ake ganin na cikin mafi shahara a rayuwarsa ta kwallon kafa.

Ya ci kwallon ne a wasan da Barcelona ta doke Getafe 5-2 a wasan dab da karshe na gasar Copa del Ray a ranar 18 ga Afrilun 2007.

LABARAI MASU NASABA

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona

A shekarar 2009 wasu masoya kwallon kafa a Ingila da ‘yan jarida sun nuna shakku Messi zai iya tabuka abin a zo a gani ga kungiyoyin Ingila – bayan ya kasa cin kwallo a ragar kungiyoyin Ingila a gasar Zakarun Turai a wasanni 10. Amma wannan shakkar ta kau, lokacin da Messi ya yi tsalle ya jefa kwallon da Dabi ya ba shi ta sama a ragar Manchester United – kuma wasan da ake ganin ita ce ta haifar da hamayyar farko tsakanin Messi da Cristiano Ronaldo.

Bayan shekara biyu zai sake zura kwallo a raga da ya samu nasara kan tawagar Sir a wasan karshe a gasar Zakarun Turai.

Karon farko da Messi ya ci kwallo hudu a rayuwarsa ta kwallon kafa inda Barcelona ta doke Arsenal a zagayen kusa da na karshe da ci 4-1 a shekarar 2010. Sannan ya sake irin wannan bajintar ta zuba kwallaye a raga bayan shekara biyu a wasan da Barcelona ta lallasa Bayer Leberkusen 7-1.

Messi yana shekara 24 ya kafa tarihin wanda ya fi yawan cin kwallo a raga a Barcelona. Ya kafa tarihin ne a wasan da Barcelona ta lallasa Granada 5-3 a ranar 20 ga Maris din 2012. Ya yi kafada da Cesar Rodriguez da ya ci kwallo 232. Kafin ya bar Barcelona a shekarar 2021, jimillar kwallayen da ya ci a raga sun kai 672 a Barcelona.

A 2012 Messi ya ci kwallo ta 91 a shekara daya a wasan da Barcelona ta doke Real Balladolid 3-1 a ranar 22 ga watan Disamba. Wannan nasarar ta sa ya shiga kundin tarihi na Guinness Book of Records.

Ya ci wa Barcelona kwallo 79 sannan ya ci wa kasarsa Argentina 12. A shekarar ne ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na hudu a jere- duk da cewa Copa del Rey kawai ne kofin da ya lashe duk da yawan kwallayen da ya ci a 2012.

Wannan ne karo na biyu da Messi ya kafa tarihi ta hanyar cin kwallo uku a lokaci guda.

Ya ci kwallo uku a wasan da Barcelona ta yi nasara 5-1 kan Sebilla a ranar 22 ga Nuwamban 2014 inda ya zama danwasan da ya fi yawan cin kwallo a raga a tarihin La Liga. Messi ya yi kafada da yawan kwallayen Telmo Zarra 251 a 1955 danwasan gaba na Athletic Bilbao.

Ya kammala da yawan kwallaye 474 inda ya sha gaban Ronaldo mai yawan kwallaye 311 a Real Madrid. Nasarar da Barcelona ta samu kan Real Madrid 3-2 a ranar 23 ga Afrilun 2017 ba za a manta ba a tarihin El Clasico.

Kwallon da Messi ya zura ana dab da hure wasa ta ja hankali. Kwallon da ta ba wa Barcelona nasara a El Clasico kuma kwallon Messi ta 500 a Barcelona goal kuma ta ba wa Barcelona damar darewa kan teburin La Liga, kodayake Real Madrid ce ta lashe kofin gasar a shekarar. Bayan ya ci kwallon Messi ya cire rigarsa ya daga sama ya nuna wa magoya bayan Madrid a Bernabeu sunansa.

Abin da ake ganin ba zai faru ba ya faru a watan Agustan 2021 inda Messi ya bar Barcelona. Bayan shekara 21 da kwallaye 672 da kofi 35, dole Messi ya tafi domin kungiyar ba ta iya cika sharuddan yarjejeniyarsa saboda tsarin La Liga na takaita albashi. Sannan a ranar 11 ga watan Yulin 2021, Messi – yana shekara 34 – ya lashe kofin farko a Argentina bayan doke Brazil 1-0 a Copa America wasan karshe a Maracana. Shi ne ya lashe kyautar gwarzon gasar bayan zura kwallo hudu a raga.

Messi ya fadi kasa bayan hure wasan kuma abokan wasan sa suka cilla shi sama yayin da suke murnar nasara, sanann ya sake lashe Copa America bayan shekara uku. Wannan nasara ce kuma lokacin da ake ganin ba zai taba faruwa ba, ganin cewa Messi ya taba sanar da yin ritaya kafin ya yi amai ya lashe. Wannan ne babban kalubalen da ake alakanta shi da sauran zaratan ‘yankwallo musamman a muhawarar danwasan kwallon kafa da ba a taba yi ba a duniya.

Messi ya ci kwallo biyu yayin da Argentina ta doke Faransa a bugun fanariti bayan an tashi wasan karshe 3-3 Shi aka ba kyautar gwarzon danwasa a gasar bayan ya ci kwallaye bakwai.

Messi ya ci kyautar Ballons d’Or biyu bayan ya bar Barcelona – daya a Paris St-Germain daya kuma a Inter Miami – inda ya hada guda takwas. Ta karshe da ya lashe ita ce a watan Oktoban October 2023 bayan lashe kofin duniya.

Duk da gasar cin Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta karshe ga Messi, amma danwasan ya taka rawar gani domin ya ci kwallaye takwas a gasar inda ya hada jimilla 21 a matsayin wanda ya fi yawan kwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya kafin Mbappe ya zarta shi da ke da 22 a wasan neman na uku da Faransa ta doke Ingila. Messi mai shekara 39, bai yi nasara ba a wasan karshe – inda Argentina ta sha kashi a hannun Sifaniya a wasan karshe – amma tarihin kwallon kafa ba zai taba mantawa da shi ba.

Messi
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Shin Mece Ce Matsalar Super Eagles
  • Abba Ibrahim Wada
    Waye Da Gaskiya Tsakanin Ronaldo Da Jorge Jesus?
  • Abba Ibrahim Wada
    APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai

MASU ALAKA

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal
Wasanni

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal

October 21, 2026
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona
Wasanni

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona

October 20, 2026
Abubuwa 3 Da Za Su Sa Ɗan Wasa Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Bana
Wasanni

Abubuwa 3 Da Za Su Sa Ɗan Wasa Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Bana

October 19, 2026
Next Post
Sodiq Safoev: Kasar Sin Tana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Tabbatar Da Ci Gaba Mai Dorewa A Yankin Tsakiyar Asiya

Sodiq Safoev: Kasar Sin Tana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Tabbatar Da Ci Gaba Mai Dorewa A Yankin Tsakiyar Asiya

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.