ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutum 53,000 Ke Mutuwa Duk Shekara Sakamakon Amfani Da Gurbataccen Abinci —Gwamnati

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Abinci

Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta bayyana a ranar Litinin cewa Nijeriya na samun kusan mutum miliyan 50 da ke kamuwa da cututtukan da ke da alaka da gurbataccen abinci, yayin da sama da mutum 53,000 ke mutuwa sakamakon irin wadannan cututtuka a duk shekara.

Karamin Ministan Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Iziak Salako, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai domin tunawa da Ranar Kula da Tsaron Abinci ta Duniya ta shekarar 2026.

Ya bukaci masana’antun sarrafa abinci da su sake duba kayayyakinsu ta hanyar rage gishiri, sukari da kitse marasa lafiya, tare da inganta tsafta, bin diddigin kayayyaki da bayyana sahihan bayanai a jikin kayan abinci domin rage yawaitar cututtukan da ke da alaka da abinci a kasar.

ADVERTISEMENT

Salako ya ce yara masu shekaru kasa da biyar ne ke daukar sama da kashi 80 cikin 100 na nauyin cututtukan da ke fitowa daga gurbataccen abinci a Nijeriya, yana mai gargadin cewa rashin ingancin abinci na lalata lafiya, ci gaba da kuma makomar miliyoyin yara a kasar.

A cewarsa, sama da mutum miliyan 40 na kamuwa da gudawa a Nijeriya na da alaka da kwayoyin cuta da ke cikin abinci kamar Salmonella infection, Escherichia coli infection, Campylobacter, Shigella da rotabirus. Ya kuma ce gurbatattun sinadarai, ciki har da gubar lead, na zama babbar barazana ga lafiyar jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Ministan ya jaddada cewa bai kamata a ci gaba da kallon tsaron abinci a matsayin batun fasaha kawai ba, sai dai a matsayin wani muhimmin batu na tsaron lafiya da ci gaban kasa.

Ya kara da cewa baya ga hana yaduwar cututtuka, dole ne tsaron abinci ya kuma magance yawaitar cututtukan da ba sa yaduwa daga mutum zuwa mutum kamar Hypertension, Stroke, Diabetes, Obesity da cututtukan zuciya, wadanda ke da alaka da yawan amfani da gishiri, sukari da kitse masu illa ga lafiya.

Salako ya bayyana cewa National Agency for Food and Drug Administration and Control ta kammala shirya dokokin rage sinadarin sodium a cikin abincin da ake sarrafawa, yayin da Nijeriya ke aiwatar da dokokin kawar da kitse na masana’antu (trans fats) bisa shawarwarin Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ya kuma kara da cewa gwamnati na karfafa harajin abubuwan sha masu yawan sukari tare da samar da tsarin bayyana bayanan sinadaran abinci a gaban marufi, domin bai wa masu amfani da kayayyakin abinci damar yin zabi mafi inganci ga lafiyarsu.

Ministan ya kuma yi kira ga masu sayar da abinci da masu gudanar da harkokin kasuwanci da su bi ka’idojin kasa na tsaron abinci, tare da rokon abokan huldar ci gaba, masu bincike da kafafen yada labarai da su mara wa kokarin inganta sa ido, wayar da kan jama’a da kuma kyawawan hanyoyin tabbatar da amincin abinci baya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin domin tunawa da Ranar Tsaron Abinci ta Duniya ta 2026, CAPPA ta yi gargadin cewa miliyoyin ’yan Nijeriya na kara fuskantar hadarin lafiya sakamakon yawan amfani da sukari, gishiri, kitse marasa lafiya da kuma abincin da aka sarrafa fiye da kima.

Babban Daraktan CAPPA, Akinbode Oluwafemi, ya ce: “Tsaron abinci ba wai kawai hana gubar abinci ba ne. Haka kuma yana nufin tabbatar da cewa abinci da abubuwan sha da ake samarwa ’yan Nijeriya ba sa lalata lafiyarsu da jin dadinsu a hankali.”

Ya yi gargadin cewa raunin matakan kariya na doka da kuma tallata kayayyakin da ba su da amfani ga lafiya cikin karfi na taimakawa wajen karuwar masu fama da Hypertension, Diabetes, Obesity, Stroke, cututtukan koda da kuma wasu nau’o’in cutar daji.

Abinci
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.