ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rufe Kan Iyakoki Ke Ci Gaba Da Zama Barazana Ga Tattalin Arzikin Nijeriya

by El-Zaharadeen Umar
3 months ago
Iyakoki

Kimanin shekaru goma ke nan wasu daga cikin iyakokin Nijeriya da Nijar ke garkame bisa umarnin gwamnatin tarayya wanda ta ce akwai dalilai na tsaro kamar yadda suka taba ambata wa.

To, sai dai rufe wadannan kan iyakoki na cigaba da zaizaye yanayi da karfin tattalin arzikin ‘yan kasa musamman wadanda suke huldar saye da sayarwa ta hanya sahihiya.

A lokuta daban-daban gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin marigayi Muhammad Buhari ta dage cewa ana amfani da kan iyakokin wajen shigowa da makamai da kuma haramtattun kwayoyi zuwa Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Hatta gidajen mai da suke da alaka da wasu garuruwan kan iyaka sun fuskanci irin wannan yanayi wanda har yanzu wasu gidajen mai a rufe suke sakamakon wancan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka.

Sannu a hankali wannan matsala ta rufe kan iyakoki na cigaba da zama babbar barazana ga harkokin yau da kullum da kuma durkusar da tattalin arziki musamman al’ummomin da ke da alaka da iyakokin Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Farkon wannan gwamnati ta shugaba Tinubu ta bayyana aniyar ta na bude kan iyakoki amma daga baya, sai ta bude wasu ta bar sauran a rufe ba tare da karin haske ba.

Jihar Katsina tana da iyaka da kasar Nijar wanda a lokacin baya an yi hada hadar kasuwanci ta sahihiyar kuma amintacciyar hanya, a ya yin da wani bangare ake samun masu fasa kwabri wadanda ke bi ta barauniyar hanya.

Akwai iyakoki guda biyar da suke karkashin kulawar jami’an hukumar hana fasa kwabri ta kasa reshen jihar Katsina, amma babu wanda ke bude a hukumance a halin yanzu.

Wannan yanayi na cigaba da ta’azara musamman sabbin dokokin da kasar Nijar ke bijiruwa da su domin amfanin kasar su, wanda hakan ba karamin illa yake yi wa kasuwanci da ‘yan kasuwar Nijeriya ba

Bana shekaru biyu ke nan da gwamnatin Nijar ta hana shigowa da ragona zuwa Nijeriya ta wadannan kan iyakoki guda biyar da ke karkashin jihar Katsina wanda hakan ya taimaka wajen tsadar dabbobi a lokacin Sallah.

Mahukunta a kasar Nijar ba sa daukar abu da wasa, idan aka ce wannan abu doka ne, to, abinda zai raba ka da su lafiya shi ne, a kiyaye, idan kuma aka kuskure to hukunci sai ya tabbata.

Baya ga hana shigowa da dabbobi da gwamnatin Nijar ta yi, yanzu haka gwamnatin ta hana shigowa da man fetur zuwa Nijeriya domin yanzu man fetur din Nijar ya fi na Nijeriya sauki sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran.

Kasar Nijar ta dai rage kudin man fetur din ta, maimakon karawa, saboda haka man fetur din Nijar ya fi na Nijeriya sauki, amma sun hana shigo shi zuwa Nijeriya bisa wasu dalilan da ba su bayyana ba a hukumance.

Wani abu da ke ciwa ‘yan kasuwa da masu haya da motoci akan iyakokin Nijeriya da Nijar tuwo  a kwarya yanzu shi ne, wata sabuwar doka da gwamnatin Nijar ta bullo da ita, ta hana direbobi daukar fasinjoji cikin mota fiye da mutum daya shiga kasar Nijar din kai tsaye.

Yanzu duk motar hanyar da zata shiga Nijar daga Nijeriya ba zata dauki fiye da mutum guda ba, sai dai idan ta shiga Nijar din ta dauki ko mutum nawa suke iya dauka.

Lamarin da ya kai inda ya kai, inda mafiyawancin ‘yan kasuwa ke kokawa akan wannan sabbin dokokin kasar Nijar da ta bijiru da su, bayan wadanda ake fama da su tuntuni.

A wani taron tattaunawa da hukumar hana fasa kwabri ta kasa ta shirya tsakanin ‘yan jaridu da jami’an ta a jihar Kano kakakin hukumar na kasa Abdullahi Aliyu Maiwada ya yi karin haske game da wannan aika-aika da ake zargin gwamnatin tarayya ta yi.

Taron dai an shirya shi ne bisa dalilin kara fahimtar juna da kulla alaka tsakanin ‘yan jaridu da jami’an hukumar kwastom domin samun nasarar da ake bukata.

Kakakin ya tabbatar da cewa har yanzu wadannan kan iyakoki suna rufe wanda ya ce ba zai iya bayyanawa al’umma dalili ba saboda yanayi na aiki da kuma tsaron kasa

Rufe kan iyakoki dai na cigaba da kawo bakin sauyi a yanayi da siga irin ta kasuwanci musamman al’ummomin da suke da alaka da kan iyakokin Nijeriya da Nijar.

Iyakoki
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Sukar Da Ake Yi Wa Mbappé Ta Yi Yawa — Dembélé

Sukar Da Ake Yi Wa Mbappé Ta Yi Yawa — Dembélé

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.