Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta bayyana cewa a halin yanzu mutane bakwai na fuskantar shari’a a Jihar Gombe bisa laifukan da suka shafi safarar jarirai da safarar mutane, yayin da wasu biyu aka same su da laifi tare da yanke musu hukuncin ɗauri a kurkuku.
Kwamandan NAPTIP na Jihar Gombe, Aminu Shira, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai a Gombe, inda ya ce hukumar na ƙara ƙaimi wajen rusa ƙungiyoyin masu safarar mutane tare da tabbatar da an gurfanar da masu hannu a gaban kuliya.
Shira ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya gano cewa wasu ma’aikatan lafiya da jami’an kula da walwalar jama’a sun haɗa kai da masu safarar mutane wajen sauƙaƙa safarar da sayar da jarirai ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, NAPTIP ta ƙara ƙarfafa tattara bayanan sirri, gudanar da bincike, kama waɗanda ake zargi da kuma gurfanar da su a kotu, a matsayin wani ɓangare na yaƙin da take yi da safarar yara da sauran nau’o’in safarar mutane a jihar.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro da na tabbatar da doka domin tabbatar da cewa an kama duk masu hannu a wannan haramtacciyar sana’a tare da gurfanar da su bisa tanadin doka.














