Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Babban Hafsan Sojin Nijeriya bisa tura ƙarin sojoji zuwa Karamar Hukumar Yauri domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar duba sabbin sojojin da aka tura yankin, inda ya ce matakin ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.
Gwamna Idris ya ce ƙarin sojojin zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan tsaro da dawo da zaman lafiya a Yauri, da Shanga, da Ngaski da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da su. Ya bayyana yankin Yauri a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da ke fuskantar matsalar tsaro saboda kusancinsa da jihohin Neja da Zamfara, yayin da Fakai ke da iyaka da Sakkwato, kuma Kebbi ke da iyaka da Jamhuriyar Benin.
Ya yaba wa jami’an tsaron da ke aiki a yankin bisa jajircewa da sadaukarwa, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba su dukkan goyon bayan da suke buƙata. Ya ce tsaro nauyi ne da ya rataya a kan kowa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin gwuiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnan ya kuma buƙaci sojojin da su ƙara kaimi wajen fatattakar ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka. Ya ce yana da yaƙinin cewa ƙarin sojojin, tare da horo da ƙwarewar jami’an tsaron Nijeriya, za su taimaka wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’ummomin yankin.
Ya ƙara da cewa ya kamata sojojin su ci gaba da bin ’yan bindigar ba tare da gajiyawa ba, domin dawo da cikakken zaman lafiya da bai wa manoman da suka gudu damar komawa gonakinsu. Gwamna Idris ya kuma gode wa jami’an tsaro bisa hidima da sadaukarwarsu, tare da yi musu addu’ar samun nasara da kariya a yayin gudanar da ayyukansu.














