“Na kasance mai aminci, biyayya, da gaskiya. Zan yi hidima ga Nijeriya da dukkan ƙarfina. Zan kare haɗin kanta, kuma in kare mutuncinta da darajarta. Allah Ya taimake ni.”
Na samu gata da ɗaukaka mai girma kasancewar ina hidimta wa ƙasarmu mai girma. Duk wani aiki da na gudanar yana tuna min da wannan alƙawari da na ɗaukar wa ƙasa.
Wannan alkawari shi ya zama babban jagora ga manufofin da nake aiwatarwa a Ma’aikatar Tsaro.
Na ɗora wa kaina da mataimakana bayyananniyar falsafar aiki: jagoranci ta hanyar zama abin koyi. Sakamakon da muka samu tare a baya-bayan nan shaida ce ta wannan jajircewa.
Ma’aikatar Tsaro ita ce cibiyar aiwatar da manufofin tsaro a Nijeriya. Wannan na buƙatar zurfin tunani da hangen nesa, domin tsara manufofi da aiwatar da su na da tasiri mai faɗi ga tsarin tsaron ƙasa baki ɗaya.
Ina sane da wannan babban nauyin da ake sa ran zan ɗauka, kuma saboda haka nake maimaita alkawarin ƙasa a zuciyata a duk lokacin da dama ta samu.
Wannan ya ci gaba da zama ginshiƙin jagorancina cikin watanni bakwai da suka gabata a Ma’aikatar Tsaro.
Mun fuskanci lokuta masu wahala da suka gwada ƙudurarmu ta tunkarar barazanar tsaro a ƙasar nan, kuma martanin da muka mayar ya kasance cikin tsari mai kyau kuma an daidaita shi da yanayin kowace barazana, la’akari da yadda wasu daga cikin waɗannan barazanon suke da salo na musamman waɗanda ba na gargajiya ba.
Sauyawa daga kwamandan soja zuwa mai tsara manufofin tsaro ya faru cikin gaggawa. A gare ni, babban bambancin shi ne kawai na maye gurbin kayan sojan daji na da babbar riga (kaftan) da kwat.
Wannan sauyin sutura bai sauya yadda nake tunani ko yadda nake kallon al’amura ba.
Na kasance cikakke cikin sanin muhimmiyar rawar da Ma’aikatar Tsaro ke takawa a tsarin tsaron ƙasa. Saboda haka, na ƙaddamar da taron taƙaitaccen bayani kan harkokin tsaro na kowane wata, inda shugabannin rundunonin tsaro ke gabatar wa Ma’aikatar Tsaro rahoton ayyukansu domin taimakawa wajen tsara manufofi da kuma fayyace alkiblar ma’aikatar.
Wannan mataki na dabaru ne da aka ƙirƙira domin samar da sauyi na hukuma wanda zai ba da damar gudanar da bitar yadda ake aiwatar da ayyuka, tare da ci gaba da ƙarfafa ƙaimi wajen aiwatar da ayyukan tsaro a dukkan yankunan da ake gudanar da hare-haren soji a faɗin ƙasar.
Wannan tsari shi ne irinsa na farko a tarihin Ma’aikatar Tsaro, kuma ya tabbatar da cewa dukkan manyan masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da harkokin tsaron ƙasa suna tafiya da manufa ɗaya kuma suna aiki da fahimta.
Yayin da muke ci gaba da tafiya a wannan hanya, mun yanke shawarar sake duba batun haɗin gwiwar ƙasashen yanki wajen yaƙi da matsalolin tsaro.
Al’amarin rashin tsaro a yankin Sahel ya kai matakin da ke tayar da hankali. Saboda haka, a Ma’aikatar Tsaro mun fahimci muhimmancin samar da kariya ta hanyar kulla haɗin gwiwa da ƙasashen yankin.
A wani muhimmin mataki na samar da wannan kariya domin kare Nijeriya daga yaɗuwar matsalolin tsaro da ke ƙara tsananta a yankin Sahel, Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Tarayyar Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ba Ma’aikatar Tsaro izinin sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da Jamhuriyar Kamaru, domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu, musamman a kan iyakar kudancin da suka haɗa juna.
Muhimman fannonin da Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) ta ƙunsa sun haɗa da ƙarfafa daidaiton gudanar da ayyukan tsaro, musayar bayanan sirri, tallafin kayan aiki da dabarun yaƙi, horar da sojoji tare, shirye-shiryen musayar jami’an soja, da kuma inganta hanyoyin haɗin gwiwa wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro da ke tasowa.
Sanya hannu kan wannan yarjejeniyar tsaro da Jamhuriyar Kamaru ya kasance mataki na dabaru, domin ƙasashen biyu suna daga cikin manyan masu ruwa da tsaki wajen ƙarfafa tsaron teku da kuma kare muradun tattalin arziki da tsaro a yankin Tekun Guinea (Gulf of Guinea).
Yankin Tekun Guinea ya daɗe yana ɗaya daga cikin wuraren da suka fi fama da matsalolin fashin teku, fashi da makami a cikin teku, satar ɗanyen mai, da sauran barazanar tsaro da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasashen yankin da kuma muradunmu na bai ɗaya.
Muhimmancin haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya ma bai ɓace mana ba a Ma’aikatar Tsaro. Hakika duniya ta zama wuri guda, kuma babu wata ƙasa da za ta iya cewa ita kaɗai ce ke da dukkan mafita ga matsalolin tsaro. Wasu ƙasashe suna da abin da muke buƙata, haka kuma su ma suna buƙatar abin da muke da shi.
Wannan ne ya bayyana dalilin da ya sa aka sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwar soja da Jamhuriyar Turkiyya wasu watanni da suka gabata.
Jamhuriyar Turkiyya na daga cikin ƙasashen da suka ci gaba sosai a fannin fasahar soja da ƙirƙire-ƙirƙiren tsaro. Ta yi suna a duniya wajen ƙwarewa da ƙarfin da take da shi a harkokin tsaro.
Saboda haka, yanke shawarar sanya hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tsaro ya kasance ne domin zurfafa haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu, tare da ƙara haɓaka ƙarfin tsaron Nijeriya da inganta ƙwarewar rundunonin tsaron ƙasar.
An samu gagarumar nasara a wannan fanni, kuma an fara ganin sahihan sakamako a zahiri.
Sojojin Amurka suna Nijeriya. Wannan batu ya haifar da muhawara da sharhi da dama a tsakanin jama’a.
Sai dai nasarorin da aka samu a yaƙi da ta’addanci sun tabbatar da amfanin wannan haɗin gwiwa. Wannan nasara ce ga Nijeriya.
Ko kaɗan ba za a iya ɗaukar hakan a matsayin tauye ikon ƙasar ko cin zarafin ikon mallakar ƙasarmu ba.
A zahiri, yarjejeniyoyin tsaro an kulla su ne domin haɗin gwiwa, ba domin tsoma baki cikin ikon wata ƙasa ba. Wannan shi ne ainihin manufar Kungiyar Haɗin Gwiwa ta Amurka da Nijeriya (US–Nigeria Joint Working Group).
A nan gaba zan ware lokaci in yi cikakken bayani kan wannan batu, musamman game da manufar “Yarjejeniyar Matsayin Sojoji (Status of Forces Agreement)” a cikin haɗin gwiwar tsaro na ƙasa da ƙasa.
A Ma’aikatar Tsaro, muna ci gaba da faɗaɗa fagen haɗin gwiwarmu tare da sabunta da ƙarfafa tsofaffin yarjejeniyoyin tsaro da kawayenmu na duniya.
Misali, kwanan nan na karɓi baƙuncin wata babbar tawaga daga Birtaniya, karkashin jagorancin mai ba Firaministan ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Jonathan Powell, domin halartar Tattaunawar Haɗin Gwiwar Tsaro da Kare Ƙasa ta huɗu tsakanin Birtaniya da Nijeriya (SDP4).
Birtaniya ta daɗe tana ɗaya daga cikin kawayen Nijeriya. Muna da tarihin haɗin gwiwa na tsawon lokaci, kuma sake nazarin fahimtar juna kan harkokin tsaro domin ta dace da sabon yanayin ƙalubalen tsaron da muke fuskanta yana da matuƙar muhimmanci.
Hakan ya yi daidai da sabon tsarin manufofin Ma’aikatar Tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi.
Haka kuma, ana ci gaba da ɗaukar manyan matakai domin haɓaka ƙarfin Nijeriya na ƙerawa da bunƙasa kayan tsaro da fasahohinta na cikin gida.
Wasu makonni da suka gabata, na halarci taron Omniverse Africa 3.0 Summit da aka gudanar a Legas, inda na kasance Babban Baƙo na Musamman tare da gabatar da muhimmin jawabi.
Na gabatar da muƙala mai taken: “Dokar Kashi 70/30: Dalilin da Ya Sa Ajandar Tsaro da Ajandar Ƙirƙire-ƙirƙire ta Nijeriya Suka Zama Aiki Ne Guda na Ƙasa.”
Babban saƙon da ke cikin takardar shi ne cewa: “Makoma tana buƙatar mu haɗa jarumtaka da fasaha, hangen nesa, ƙarfin masana’antu da ƙirƙire-ƙirƙire domin gina irin ƙwarewa da ƙarfin da za su tabbatar da tsaron ƙasa a nan gaba.”
Wannan matsayi yana bayyana a fili cikin sauye-sauyen da ake ci gaba da aiwatarwa a Kamfanin Masana’antun Tsaro na Nijeriya (DICON), domin samar da tsarin da zuba jari a fannin tsaro zai zama abin da ke haɓaka tattalin arziki, samar da manyan ayyukan yi masu alaƙa da fasaha, ƙarfafa binciken jami’o’i, da kuma buɗe sabbin kasuwannin kasuwanci.
Wannan muhimmin mataki ne, musamman ganin cewa mun fahimci ƙalubalen tsaron da muke fuskanta na cikin gida ne, masu haddasa su ’yan cikin gida ne, kuma mafita mafi ɗorewa ita ma dole ta kasance ta cikin gida.
Waɗannan su ne wasu daga cikin fannonin da muka samu nasara a Ma’aikatar Tsaro.
Kuma hakan ya samu ne sakamakon gagarumin goyon bayan Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma sauran masu ruwa da tsaki a tsarin tsaron ƙasa.
Shin za mu yi ƙasa a gwiwa mu huta?
A’a. Ba za mu yi haka ba, kuma ba za mu daina ba har sai mun shawo kan masu aikata laifuka da ke cikin al’ummarmu.
Alkawarin ƙasarmu shi ne tushen burinmu, burinmu kuma shi ne cikar wannan alkawari.
Janar Christopher Gwabin Musa, CFR (mai ritaya), Ministan Tsaron Tarayyar Nijeriya. Kafin ya samu wannan muƙami, shi ne Babban Hafsan Tsaron ƙasar













