ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
talauci

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya ba wai kawai yana ƙara tsananta talauci ba ne, har ma da raunana ƙarfin iyalai wajen farfaɗowa daga matsin tattalin arziki.

Rahoton mai taken “Rashin Tsaro, Hanyoyin Samun Abinci da Walwalar Jama’a a Arewacin Nijeriya” ya nuna cewa rikice-rikicen da ake fama da su a yankin na jefa mutane cikin talauci ta hanyoyi daban-daban, ciki har da rasa hanyoyin samun kuɗin shiga, lalacewar dukiyoyi, durkushewar kasuwanni da kuma ƙara jefa iyalai cikin mawuyacin hali.

An gabatar da sakamakon rahoton ne a wani taron Intanet da Chronic Poɓerty Adɓisory Network (CPAN) na Cibiyar Nazarin Ci Gaba ta Birtaniya, tare da Cibiyar Bincike da Ayyukan Ci Gaba da kuma shirin Ƙarfafa Zaman Lafiya da Juriya a Nijeriya (SPRiNG) mai samun tallafi daga Ma’aikatar Harkokin Waje, Ƙungiyar Commonwealth da Ci Gaba ta Birtaniya (FCDO) suka shirya.

ADVERTISEMENT

Da take gabatar da rahoton, mataimakiyar daraktar CPAN, Dakta Ɓidya Diwakar, ta ce binciken ya gano manyan nau’o’i uku na matsalolin tsaro da ke addabar Arewacin Nijeriya. Waɗannan sun haɗa da hare-haren Boko Haram/ISWAP a Arewa maso Gabas, rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya, da kuma ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma.

A cewarta, hare-haren Boko Haram da ISWAP sun fi yin mummunan tasiri ga rayuwar iyalai, inda gidajen da abin ya shafa suka samu raguwar kashe kuɗaɗen rayuwa da kaso tsakanin 8 zuwa 14 cikin 100 idan aka kwatanta da sauran gidaje a cikin shekaru biyu kafin gudanar da binciken. Haka kuma, bashin da rikice-rikicen suka haifar tun daga sheƙarar 2009 ya ƙara janyo asarar kashi 8 zuwa 13 cikin 100 ga waɗannan iyalai.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Rahoton ya kuma nuna cewa rikicin manoma da makiyaya ya fi shafar iyalan da ke dab da faɗawa cikin talauci a yankin Arewa ta Tsakiya, inda ya haddasa raguwar kashe kuɗaɗen rayuwa da kashi 14 cikin 100 ga iyalan da ke matakin kashi na 60 cikin 100 na samun kuɗin shiga. Haka kuma, ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma sun jawo raguwar kashe kuɗaɗen rayuwa da tsakanin kashi 4 zuwa 11 cikin 100, musamman ga iyalan da ke cikin matsakaicin talauci.

Duk da wannan mummunan yanayi, rahoton ya bayyana cewa faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga su ne hanyoyi mafiya inganci na fita daga talauci.

Rahoton ya ce, “Haɗa hanyoyin samun kuɗin shiga daga noma, ayyukan da ba na noma ba da kuma ƙananan sana’o’i su ne matakan kariya mafi tasiri ga iyalai a dukkan nau’o’in rikice-rikicen da aka yi nazari a kansu.”

Sai dai binciken ya nuna cewa kashi 13 cikin 100 kacal na shugabannin gidaje a Arewacin Nijeriya ne ke da hanyoyin samun kuɗin shiga fiye da guda ɗaya.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa ilimi na ƙara wa iyalai damar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga, amma gidajen da mata ko matasa ke jagoranta, waɗanda suka kai kashi 28.9 cikin 100 na gidaje a yankin, ba sa cin gajiyar irin waɗannan damammaki yadda ya kamata.

Da yake jawabi a taron, Ministan Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci, Bernard Doro, ya yi alƙawarin ci gaba da haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki, tare da buƙatar masu bincike su samar da ƙarin hujjoji da bayanai kan hanyoyin tantance waɗanda suka cancanta, tsara yadda za a aiwatar da shirye-shirye, da kuma hanyoyin da za su taimaka wa jama’a su fita daga talauci a ƙarƙashin shirin gwamnati na ” Tsarin Ba da Agajin Jin Ƙai da Martani Ɗaya Don Yaƙi da Talauci. “musamman domin tallafa wa mata da matasa da galibi ake bari a baya.

talauci
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Kotu Ta Soke Rajistar Jam’iyyar NDC A Matsayin Jam’iyyar Siyasa

Kotu Ta Soke Rajistar Jam'iyyar NDC A Matsayin Jam'iyyar Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.