ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
Turji

Al’ummomin yankin gabashin Jihar Sakkwato sun sake bayyana damuwa kan matsalar tsaro bayan rahotannin da ke cewa fitaccen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, da mabiyansa na gudanar da horo da amfani da makamai da dabarun yaƙi a wasu sassan ƙaramar hukumar Isa.

Lamarin ya ƙara jefa fargaba a zuƙatan mazauna ƙauyukan kan iyaka, waɗanda suka shafe shekaru suna fuskantar hare-hare, sace-sacen mutane da kuma satar shanu a yankin Sakkwato zuwa Zamfara.

Majiyoyin tsaro sun ce ana zargin ana gudanar da wannan horo ne a ƙauyukan Bingabale, Bafarawa, Bargaja da Gebe, waɗanda ke cikin yankin Sanatan Gabashin Jihar Sakkwato.

ADVERTISEMENT

An daɗe ana kallon wannan yanki a matsayin ɗaya daga cikin manyan wuraren da Bello Turji da ƙungiyarsa ke gudanar da ayyukansu.

Turji na daga cikin fitattun shugabannin ƴan bindiga da ake zargi da ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yammacin Nijeriya, musamman a jihohin Zamfara, Sakkwato da wasu sassan Jihar Neja.

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Ana danganta shi da hare-hare da dama da suka yi sanadin mutuwar fararen hula da jami’an tsaro, lalata hanyoyin rayuwa da kuma yin garkuwa da mutane da dama a yankin.

Rahotanni sun ce Turji na jagorantar mayaƙa da dama daga sansanoni daban-daban a Jihar Zamfara, ciki har da Zurmi, Sabon Birni, Anka da sauran yankuna.

A tsawon shekaru, an ce Turji ya yi watsi da ƙoƙarin sulhu da al’ummomin da abin ya shafa suka yi domin su samu damar komawa gonakinsu, makarantu, cibiyoyin lafiya da kasuwanni.

A watan Oktoban 2024, tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya umarci dakarun Operation Fansan Yamma da su tabbatar sun kama Bello Turji da sauran fitattun shugabannin ƴan bindiga, a raye ko a mace.

Yayin da yake jawabi ga dakarun a wata ziyara da ya kai Gusau, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da ƙoƙarinsu, tare da ƙarfafa musu gwiwa su ƙara himma wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankunan da suke gudanar da aiki.

Ya ce, “Shugaban Ƙasa a shirye yake ya samar muku da duk abin da kuke buƙata domin kawo ƙarshen rashin tsaro a Arewa maso Yamma da kuma faɗin Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa, “Shin kun shirya ku murƙushe su gaba ɗaya? Shin kun shirya kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a wannan ƙasa? Don Allah ku kamo min Turji, a raye ko a mace.”

A cikin wannan shekarar, babban hafsan rundunar sojoji ya kuma bayyana Turji a matsayin “mamaci mai tafiya”, yana mai alƙawarin ci gaba da kai hare-hare a kansa da mayaƙansa har sai an kawo ƙarshen ayyukansu.

Duk da waɗannan umarni da alƙawuran da kuma ci gaba da hare-haren da sojoji ke kai wa, Turji da ƙungiyarsa sun ci gaba da kai hare-hare da aikata sauran laifuka a wasu sassan Arewa maso Yammacin Nijeriya. ‘Ana Zargin Mayaƙan Turji Na Gudanar da Atisayen Soja da Sabbin Makamai’

Mai kula da ƙungiyar Moɓement for Social Justice and Good Goɓernance reshen Jihar Sakkwato, Basharu Altine Guyawa Isa, ya yi zargin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar cewa mayaƙan Bello Turji na gudanar da atisayen soja da horon amfani da makamai ta amfani da sabbin makaman da aka ce sun samu.

Ya ce daga cikin waɗanda ke halartar atisayen akwai Illa Manawa da Bomi, wanda ya bayyana a matsayin ƙanin Bello Turji.

A cewarsa, atisayen ya haɗa da amfani da manyan makamai na zamani waɗanda ake zargin an yi amfani da su a arangamar baya-bayan nan da jami’an tsaro a yankin.

Basharu ya kuma yi zargin cewa bayanan farko da suka tattara sun nuna cewa makaman na cikin wani sabon kaya ne da ƙungiyar ta samu kwanan nan, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a kan yiwuwar ƙaruwar ƙarfin makaman da ƙungiyoyin ƴan bindiga ke da su a yankin.

Ya ce, “Bincikenmu ya nuna cewa mayaƙan na gudanar da horo kan amfani da makamai da dabarun yaƙi da sabbin makamai, ciki har da wasu daga cikin manyan makaman da aka ce an yi amfani da su a arangamar da aka yi da jami’an tsaro kwanan nan.”

An ce ana gudanar da waɗannan atisayen ne a ƙauyuka masu nisa da ke kan iyakar jihohin Sakkwato da Zamfara, yankin da har yanzu jami’an tsaro ke fuskantar ƙalubalen tabbatar da cikakken tsaro duk da ci gaba da aikin Operation Fansan Yamma.

Mai rajin ya kuma yi zargin cewa wasu sabbin mayaƙa da ake kyautata zaton suna da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, kuma suna da ƙwarewa a yaƙi da amfani da makamai, sun shiga yankin domin horar da mayaƙan Turji da ƙarfafa su.

Ya ce, “Akwai alamun cewa wasu daga cikin sabbin waɗanda suka iso suna da ƙwarewa ta musamman wajen yaƙi da sarrafa makamai. A cewar majiyoyi, manufarsu ita ce horarwa da kuma ƙarfafa mayaƙan Turji da ke aiki a yankunan kan iyakar jihohin Sakkwato da Zamfara.”

A cewarsa, bayanan sirri da aka samu daga majiyoyi a Binchi sun nuna cewa na’urar hangen nesa ta dare (night ɓision deɓice) da ake zargin Turji ya saya a makon da ya gabata na daga cikin kayan aikin da aka kai sansaninsa.

Basharu ya kuma yi zargin cewa Kachalla Haru Dole da Kachalla Ibrahim Chimo, waɗanda ya bayyana a matsayin kwamandojin manyan sansanonin ƴan bindiga da ke bayan Kogin Maradun, suna da hannu wajen sayowa da jigilar waɗannan makamai.

Ya ce mutanen biyu sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da isar da makaman tare da Turji.

Har ila yau, ya yi zargin cewa binciken da ake yi na ci gaba da gano bayanai kan ƙawancen da ke ƙara ƙarfi tsakanin Chimo da Turji, wanda ya ce na iya kasancewa wani ɓangare na dabarar faɗaɗa ayyukansu a Gabashin Jihar Sakkwato.

Ya bayyana damuwa cewa wannan haɗin gwiwa na iya zama shirin kai hare-hare a lokaci guda kan hedkwatocin ƙananan hukumomi biyar na yankin kafin damina ta yi ƙarfi.

Basharu ya ce ana sa ran ƙarin bayanai za su fito yayin da bincike ke ci gaba kan wannan ƙawance da ake zargi, jigilar makaman da kuma tasirin hakan ga tsaron al’ummomin Gabashin Jihar Sakkwato.

A ƙarshe, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara sanya ido tare da ɗaukar matakan gaggawa domin tantance sahihancin waɗannan bayanan sirri da kuma dakile duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Turji
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna

MASU ALAKA

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu
Rahotonni

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau
Rahotonni

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara
Rahotonni

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Next Post
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam'iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

July 17, 2026
Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

July 17, 2026
Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

July 17, 2026
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

July 17, 2026
Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

July 17, 2026
Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

July 17, 2026
Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

July 17, 2026
Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

July 17, 2026
Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.