Kasar Namibia za ta yi amfani da manufar soke haraji ta kasar Sin kan kayayyakin kasashen Afrika a matsayin wata muhimmiyar dama ta raya bangarorin bunkasa tattalin arziki, da bunkasa fitar da amfanin gona, da abincin ruwa, da furanni zuwa kasuwar kasar Sin.
Mai rikon mukamin babban jami’in hukumar bunkasa zuba jari da ci gaba ta Namibia Julia Muetudhana ce ta bayyana haka yayin wani taron tattaunawa tsakanin hukumomin gwamnati da bangarori masu zaman kansu, inda ta ce gatan da manufar ta Sin ta ba su, za ta iya taimakawa wajen bunkasa fitar da naman sa, da na rago, da akuya, da abincin ruwa, da inibi, da blueberries daga kasar.
Ta ce damar ta yi daidai da shirin raya kasa na 6 na Namibia, wanda ke son kara gudunmuwar da bangaren kiwon dabbobi da amfanin gona ke bayar ga alkaluman tattalin arziki na GDP daga kaso 4.6 zuwa a kalla kaso 8, ya zuwa shekarar 2030.
Har ila yau, ta ce manufar shirin ita ce kara yawan kason bangaren sarrafa kayayyaki cikin alkaluman tattalin arziki na GDP daga kaso 10.6 zuwa kaso 18, da kuma kara kason kayayyakin da aka sarrafa cikin kayayyakin da ake fitarwa daga kasar, zuwa kaso 60. (Fa’iza Mustapha)














