ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Da Kwastam Sun Kulla Yarjejeniyar Haɗin Guiwar Aiki

by Muhammad
4 months ago

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa,NDLEA, da Hukumar Kwastam ta Nijeriya, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa domin inganta ayyukansu da ƙarfafa haɗin kai tsakanin su.

An cimma yarjejeniyar ne a wani taro na manyan jami’ai da aka gudanar a hedikwatar NDLEA da ke Abuja a ranar 27 ga Afrilu, 2026, inda shugaban NDLEA, Mohamed Buba Marwa, da shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, suka sanya hannu kan sanarwar yarjejeniyar.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce hukumomin biyu sun amince cewa ƙalubalen da ke tattare da laifukan ƙasa da ƙasa, musamman fataucin miyagun ƙwayoyi, na buƙatar haɗin kai mai ƙarfi da tsari na zamani.

ADVERTISEMENT

Sabuwar yarjejeniyar na da nufin kawar da maimaita aiki, rage rikice-rikice tsakanin hukumomi, da samar da sauƙin musayar bayanan sirri.

Shugabannin hukumomin sun jaddada aniyarsu na ƙarfafa mutunta juna da ƙwarewa yayin gudanar da ayyukansu na kare tsaron ƙasa da sauƙaƙe kasuwanci na halal.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Sanarwar ta ƙunshi muhimman matakan haɗin gwiwa da suka haɗa da:

  • Samar da ingantaccen tsarin musayar bayanan sirri domin dakile laifuka tun kafin su faru
  • Kafa rundunonin haɗin gwiwa a wurare masu muhimmanci tare da cikakkun ƙa’idojin aiki
  • Mutunta hurumin kowace hukuma domin kauce wa katsalandan
  • Kafa kwamitin dindindin na haɗin gwiwa domin warware sabani cikin gaggawa
  • Ƙarfafa aiki tare a tashoshin jiragen ruwa, filayen jiragen sama da iyakokin ƙasa

Marwa da Adeniyi sun bayyana cewa wannan haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci ga ƙasa, domin zai taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da inganta tsaron hanyoyin shiga da fita na Nijeriya.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Tir Da Muguwar Aniyar Japan Game Da Wurin Bauta Na Yasukuni

Kasar Sin Ta Yi Tir Da Muguwar Aniyar Japan Game Da Wurin Bauta Na Yasukuni

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.