ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NED – Hannun Tsoma Baki Da Ke Sanye Da “Tufar Dimokuradiyya”

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago
NED

Wani sabon rahoto na shekara-shekara da wata kungiya mai zaman kanta ta Amurka mai suna “National Endowment for Democracy” (NED) ta fitar, ya nuna wani salo da aka sani, kuma wanda ke kara tsananta, wato kungiyar na ci gaba da fadada samar da kudade ga cibiyoyinta domin ayyukan da suka shafi kasar Sin.

Cibiyoyin suna yin aikin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin da sunan “inganta dimokuradiyya”. Idan aka cire wannan “tufar dimokuradiyya”, za a iya ganin mugunyar fuskar NED a fili.

Na farko, asalin NED yana da fuska biyu: ta kira kanta kungiya mai zaman kanta, amma kudadenta kusan duka daga majalisar dokokin Amurka suke fitowa.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Allen Weinstein ya fayyace cewa, yawancin ayyukan da NED ke yi a yau, ayyuka ne da hukumar leken asiri ta CIA take yi a baya a boye.

Amma a yanzu ana gudanar da su a fili. Wannan kuma shi ne bambanci kadai, amma ainihin kudurin bai canza ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake kiran NED a matsayin “Kura da fatar Akuya” ga Washington.Na biyu, NED tana ikirarin cewa tana “bai wa masu gudanar da gwagwarmaya da juyin mulki karfi”, to amma abun tambaya shi ne wadanne kungiyoyi ko mutane ne take karfafawa?A yankin Hong Kong na kasar Sin, an fallasa cewa NED tana tallafa wa kungiyoyin da suka tunzura yin zanga-zanga a lokacin tashin hankalin shekara ta 2019.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin

A jihar Xinjiang ta Sin, kungiyoyin da ta tallafawa sun dade suna jagorantar masu neman a sanyawa kasar Sin takunkumai. A Tibet, cibiyoyin yanar gizo da take tallafawa sun ci gaba da yada labaran karya. Wannan ba “inganta dimokuradiyya” ba ne, maimakon haka tallafawa wanzuwar dakaru masu adawa da Sin ne.Bari mu kuma dubi jerin tallafin da NED ta bayyana a fili – kungiyoyin adawa a Serbia, da na Georgia, da na Ukraine, da kasashen Gabas ta Tsakiya, wadanda daga karshe suka haifar da tarzoma da zubar da jini.

Daga gabashin Turai zuwa Gabas ta Tsakiya, irin wannan tsarin tallafi yana tare da rikice-rikicen siyasa na “juyin juya halin don hambarar da mulki”.

Yanzu, an aiwatar da irin wannan mataki a Sin, don horar da cibiyoyin kawo baraka a cikin gidan kasar Sin, tare da yaudarar tunanin sassan kasa da kasa kan abin da take aiwatarwa.

NED ba ’yar kallo ba ce. Tana shiga cikin aikin kawo wa Sin barazana da cin zarafinta. Kazalika, kudadenta na karuwa, hannunta na kara shiga dukkanin sassa, kuma manufarta ba za ta taba canzawa ba, wato tsoma baki bisa hujjar “dimokuradiyya”, shi ne ainihin fuskar NED. (Mai zane da rubutu: MINA)

NED
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026
  • Sulaiman
    Shugaba Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Gabanin Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Kwanciyar Hankali Mai Ma’ana Ita Ce Hanya Mafi Kyau Ta Gudanar Da Alakar Sin Da Amurka
  • Sulaiman
    NLC Ta Goyi Bayan Buƙatar Albashi N500,000 Da Rage Farashin Mai Zuwa N500
NED
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
     Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta

MASU ALAKA

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

September 22, 2026
Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin
Daga Birnin Sin

Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin

September 22, 2026
Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin
Daga Birnin Sin

Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin

September 22, 2026
Next Post
Xi: Ya Kamata a Yi Amfani Da “Kwarewar Ci Gaban Yiwu” Yadda Ya Kamata

Xi: Ya Kamata a Yi Amfani Da "Kwarewar Ci Gaban Yiwu" Yadda Ya Kamata

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

September 22, 2026
Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci

Sabbin Alkaluman Haraji Sun Shaida Yadda Sin Ke Samun Saurin Ci Gaba A Fannin Sabon Ikon Sarrafa Hajoji Masu Inganci

September 22, 2026
Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin

Kashi 57 Bisa Dari Na Al’Ummar Amurka Suna Goyon Bayan Hadin Gwiwar Sada Zumunta Da Sin

September 22, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 51, 876 Sun Mika Wuya A Arewa Maso Gabas

Sojoji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu A Katsina Da Sakkwato

September 22, 2026
Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin

Jimillar Cinikayyar Lantarki Ta Karu Da 19.2% Cikin Farkon Watanni 8 A Sin

September 22, 2026
Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026

Sin Ta Fayyace Kamfanoni 500 Masu Zaman Kansu Mafi Karfin Jari A Shekarar 2026

September 22, 2026
Shugaba Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Gabanin Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin

Shugaba Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Gabanin Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin

September 22, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Gwamnatin Obi Za Ta Dawo Da Tallafin Man Fetur Ta Wata Hanya Daban – Kwankwaso

September 22, 2026
Ni Ya Kamata Na Lashe Ballon D’or Ta Bana — Mbappe

Ni Ya Kamata Na Lashe Ballon D’or Ta Bana — Mbappe

September 22, 2026
Binciken CGTN: Kwanciyar Hankali Mai Ma’ana Ita Ce Hanya Mafi Kyau Ta Gudanar Da Alakar Sin Da Amurka

Binciken CGTN: Kwanciyar Hankali Mai Ma’ana Ita Ce Hanya Mafi Kyau Ta Gudanar Da Alakar Sin Da Amurka

September 22, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.