Rundunar ƴansandan Jihar Legas ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa mambobin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane, wadda ta sace wata ƴar kasuwa a yankin Ijedodo tare da karɓar kuɗin fansa har naira miliyan 21 kafin sakin ta. An kama waɗanda ake zargin, Semi Buawe mai shekaru 35, da Oluwatomi Obosi mai shekaru 37 da Bamure Telemowei, bayan an bi sawunsu zuwa maɓoyarsu a Agadagba, Jihar Ondo.
Binciken ƴansandan ya nuna cewa ƙungiyar ta kitsa aikin ne a Ondo, sannan ta je Legas a watan Afrilun 2026 domin yin garkuwa da wanda za ta samu. An ce sun sace matar a kusa da wani katafaren gida a Ijedodo, inda suka tsare ta a cikin daji na tsawon kwanaki uku kafin iyalanta su biya kuɗin fansar.
Buawe, wanda ya ce ya taɓa shiga harkar garkuwa da mutane tun shekarar 2010 amma ya yi niyyar barin ta, ya amsa cewa ya shiga wannan aikin ne bayan shugaban ƙungiyar mai suna ID, wanda har yanzu ba’a kama shi ba, ya nemi ya taimaka saboda ya san Legas ciki da waje. Ya ce daga cikin naira miliyan 21 da aka karɓa, an ba shi naira miliyan 1.5.
Shi kuwa Obosi ya bayyana cewa ya shiga aikin ne saboda yana son samun kuɗin da zai yi aure. Ya ce bayan an kammala aikin, an ba shi naira miliyan 2.5, wanda ya ce yana ganin zai ishe shi ya fara sabuwar rayuwa. Sai dai ya bayyana cewa shugaban ƙungiyar ya karɓi naira 200,000 daga hannun kowannensu bayan sun koma Agadagba.
Kakakin rundunar ƴansandan Legas, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da kama waɗanda ake zargin, inda ta ce suna hannun ƴansanda kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ta kuma ci gaba da ƙoƙarin kamo shugaban ƙungiyar mai suna ID, tare da kira ga jama’a da ke da bayanan da za su taimaka wajen kama shi da su tuntuɓi ƴansanda.













