ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NiMet Ta Yi Hasashen Ruwan Sama Da Wuri, Ta Nemi Manoma Su Jinkirta Shuka

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
7 months ago
Nimet

Hukumar Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen ruwan sama na farkon lokaci a Kano, Neja, Ribas da wasu jihohi goma sha biyu na tarayya.

Ministan Sufuri da Ci gaban Jiragen Sama, Festus Keyamo, SAN, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Talata, yayin da ya kaddamar da Hasashen Yanayi na Lokutan Damina na 2026 (SCP) da NiMet ta shirya, inda ya gargadi manoma da su yi hattara kada su fara shuka iri kafin lokacin damina ya fara.

  • Sojoji Sun Ceto Mutane Takwas Da Aka Sace A Yayin Wani Bikin Aure A Shanono
  • Tsaro: Har Yanzu ‘Yan Ta’adda Na Ci Gaba Da Yi Wa Mutane Kisan Kiyashi A Arewa

Ministan ya ce, ko da yake an samu ruwan sama na farkon lokaci a wasu sassan kasar, kamar Lagos, Ribers, da Bayelsa da wasu, ainihin lokacin damina bai fara ba, inda ya jaddada cewa ana sa ran yanayi mai tsanani tsakanin Maris zuwa Mayu na wannan shekara.

ADVERTISEMENT

Hasashen SCP ya nuna yiwuwar samun ruwan sama mai yawa a yankunan kudu na kasar a wannan shekara, tare da hasashen farkon damina, karshen damina da yanayi mai tsanani a 2026.

Rahoton ya nuna cewa, ana sa ran farkon damina a Bayelsa, Ribers, Akwa Ibom, Cross Riber, Benue, Kogi, Nasarawa, Oyo, da wasu sassan Kebbi, Neja, Jigawa, Katsina, Kano, Adamawa, da Taraba. Yayin da a Borno ake sa ran fara damina ne a jinkiri.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa karshen damina na iya kasancewa da wuri fiye da yadda aka saba a wasu sassan Ogun, Osun, Ondo, Imo, Ribers, Akwa Ibom, Kogi, da Neja. Sai dai kuma, a Lagos, Ogun, Anambra, Enugu, Cross Riber, Benue, Nasarawa, da Kaduna ana sa ran karshen damina zai jinkirta fiye da yadda aka saba.

Duk da haka, ana sa ran kakar ruwan sama zai kasance mai tsawo fiye da yadda aka saba a jihohi kamar Lagos, Benue, Enugu, Ebonyi, Ogun, Oyo, Nasarawa, Anambra, Kwara, Kebbi, Kaduna, Gombe da Taraba. Yayin da wasu sassan Borno, Yobe da Neja ake sa ran kakar ruwan sama zai kasance gajere fiye da yadda aka saba.

Ana sa ran adadin ruwan sama na shekara-shekara zai kasance daidai da yadda aka saba a mafi yawan sassan Nijeriya, idan aka kwatanta da matsakaicin tsawon lokaci. Ruwan sama fiye da kima ana sa ran a jihohi kamar Borno, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Enugu, Cross Riber, Abia, Ebonyi, Akwa Ibom, da Babban Birnin Tarayya (FCT); yayin da a wasu sassan Katsina, Zamfara, Kwara, Oyo, da Ogun ake sa ran ruwan sama kasa da kima.

A lokacin kakar Maris zuwa Mayu, ana sa ran zafi da bushewa mai tsanani fiye da kwanaki 15 a wasu sassan Oyo da Ogun, yayin da bushewa mai matsakaici ake sa ran a jihohi kamar Ekiti, Kogi, Osun, Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Abia, Cross Riber da Delta, da kuma wasu sassan Kogi da Kwara.

Bugu da kari, a lokacin kakar Yuni-July-Agusta, ana hasashen bushewa mai tsanani wanda zai iya kai wa kwanaki 21 a wasu sassan Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Kebbi, Kwara, Nasarawa, Neja, Oyo, Filato, Sokoto, Yobe, da Zamfara.

A gefe guda, ana hasashen samun karancin ruwa, wanda ake kira “August Break,” zai fara daga karshen watan Yuli, kuma zai kasance mai tsanani da tsawo a jihohi kamar Lagos, Ogun, Ekiti, da wasu sassa na Oyo. Adadin kwanakin da ba za a samu ruwan sama ba ko kadan zai kasance tsakanin kwanaki 28 zuwa 40. Ana sa ran tasirin matsakaicin karancin ruwan sama a jihohi kamar Ondo, da wasu sassan Kwara da Edo.

Babban Sakataren Ma’aikatar Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Dr. Yakubu Adam Farmata, ya bayyana cewa SCP na ci gaba da zama wata muhimmiyar hanya ta karfafa hadin gwiwa tsakanin kimiyyar yanayi da tsara ci gaban kasa.

Ya ce gabatar da Hasashen Yanayi na Shekara ba kawai aikin kimiyya ba ne, amma wata muhimmiyar tattaunawar kasa ce da ke nufin karfafa shiri da aiwatar da tsare-tsaren ci gaban kasa.

Nimet
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas
Nimet
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Nimet

Har Yanzu Dai Kan Batun Tu’ammali Da Kayan Maye A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.