ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NNPP Ta Yi Barazanar Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Bin Umarnin Dawo Da Tambarinta A Kan Lokaci

by Sadiq
2 months ago

Jam’iyyar NNPP ta yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bayan ta mayar da tambarin jam’iyyar na asali.

Sai dai jam’iyyar ta ce za ta maka INEC a kotu tare da neman diyyar Naira biliyan 10, tana zargin hukumar da jinkirta aiwatar da umarnin kotu.

Rikicin ya fara ne bayan wani ɓangare na jam’iyyar da ake dangantawa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Buba Galadima ya yi ƙoƙarin karɓe ragamar jam’iyyar, lamarin da ya haifar da saɓani kan tambarin NNPP.

ADVERTISEMENT

Daga bisani, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta dawo da tambarin NNPP na asali tare da amincewa da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar.

Da yake magana da manema labarai a Abuja, Shugaban NNPP na ƙasa, Dakta Agbo Major, ya tabbatar da cewa INEC ta dawo da tambarin jam’iyyar mai “Kwandon ‘Ya’yan Itatuwa A Kan Taswirar Nijeriya.”

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ya ce hakan ya tabbatar da cewa shi da wanda ya kafa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam, su ne halastattun shugabannin NNPP.

Major ya kuma ce jam’iyyar ta fara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 ta hanyar miƙa sunayen ‘yan takarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na wucin gadi a shafin INEC.

Ya zargi INEC da rashin bin umarnin kotu saboda ba ta amince da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam’iyyar cikin wa’adin da kotu ta bayar ba.

A cewarsa, wannan jinkiri ya jawo wa jam’iyyar asara, saboda haka lauyoyinta sun fara shirin shigar da ƙara tare da neman diyyar Naira biliyan 10 a wajen INEC.

Major ya kuma yi kira ga matasa, mata da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da su shiga jam’iyyar NNPP.

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Kaduna Da Filato

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wasu Da Aka Sace A Zamfara, Katsina Da Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.