Babbar Manajar Kamfanin rabar da wutar lantarki a yankin Neja Delta NDPHC Injiniya Jennifer Adighije ta bayyana cewa, hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa NPA, ta taka gagarumar gudunmawa, wajen sake maido da manyan kayan aikin kamfanin, na biliyoyin Naira ga kamfanin, da aka yi watsi da su baya, a tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
Jennifer ta sanar da hakan, yayin da ta jagoranci tawagar mahukuntan kamfanin zuwa ziyara ga shugaban hukumar NPA, Dakta Abubakar Dantsoho a shalkwatar hukumar da ke a jihar Legas.
A cewarta, wannan daukin da hukumar ta NPA ta taimaka, ya bai wa kamfanin damar wanzar da mahimman ayyukansa, a daukacin fadin kasar.
Ta kara da cewa, daukin ya kuma, kare kamfanin daga tabka asara biliyoyin Naira, da suka kamata ya samu, a matsayin kudaden shiga.
Manajar ta kuma jinjina wa hukumar kan wannan daukin da ta taimaka a kan lokaci, inda ta kara da cewa, daukin ya kara taimaka wa kamfanin, wajen kara karfafa kayan aikinsa, tare da kuma tabbatar da, ci gaban ayyukan da kamfanin, ke ci gaba da gudanarwa.
Ta ce, kamfanin ya samo wadannan kayan aikin ne, domin ci gaba da gudanar da ayyukansa, inda ta kara da cewa, da NPA ba ta samar da daukin kan lokaci ba, da hakan zai iya janyo jinkiri ga ayyukansa, da kuma kara tsadar kudaden da kamfanin zai kashe na habaka samar da wutar lantarkin.
A cewarta, daukin da NPA ta sanar ga kamfanin, ba wai kawai na sake dawo da manyan kayan aikin kamfanin ba ne, har da ma, tsamo shi, daga tabka asarar biliyin Naira.
Manajar ta kuma bukaci da a ci gaba da yin hadaka a tsakanin NPA da kamfanin da kuma sauran hukumomin gwamnati, musamman, a bangaren samar da makamashi da kuma a fannin sufurin Jiragen Ruwa, domin a rage duk wani yanayi, na bata lokacin gudanar da ayyuka da sauran kalubale da za su iya, janyo jinkirin gudanar da bayar akwagila.
Ta kara da cewa, daukin da NPA ta samar kan lokaci ya kara taimaka wa, musamman, wajen bai wa ‘yan kwagilar da tawagar tabbacin kaucewa bata lokaci kan ayyukan da ake son gudanarwa kuma a kan lokaci.
Da take yin bayani kan dalilin ziyayar, ta ce, tawagar kamfanin ta kawo wannan ziyarar ce, musamman domin kara karfafa hadaka a tsakanin NPA da kuma kamfanin a fannon da ake da ra’ayin akai.
Ta kuma godewa shugaban hukumar da tawagar sa, kan ci gaba da taimaka wa kamfanin tare da kuma warwarewa kamfanin matsalolin da ya fuskanta a baya musamman, na gagarumar gudunmawa, wajen sake maidowa da samar da manyan kayan aiki, ga kamfanin.
Kazalika, ta kuma bai wa hukumar ta NPA tabbacin cewa, zai ci gaba karfafa hadaka da NPA musamman, a bangaren da ya shafi samar da wutar lantarki.
A na sa jawabin shugaban hukumar ta NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, yabawa kamfanin ya yi, musamman kan wannan ziyarar, inda kuma ya bai wa mahukunta kamfanin tabbacin taimaka wa shirye-shiyen sa da kuma yin hadaka a tsakanin su, musamam,n domin a kara ciyar da kasa gaba.
Kazalika Dantsoho ya kuma ya taya kamfanin murna kan gudunmawar da ya ke ci gaba da bayarwa, a fannin bunkasa samar da wutar lantarki a daukacin fadin kasar.
Dantsoho ya kara da cewa, samar da wadatacciyar wutar lantarki na kara taimaka wa, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar da kuma kara habaka walawala da jin dadin ‘yan kasar.
Shugaban ya bai wa mahukuntan kamfanin tabbacin barin kofar NPA a bude, musamman domin tattaunawar da za ta kara taimakawar ci gaba da yin hadaka a tsakanin hukumomin gwamnati da kuma sauran manyan masu ruwa da tsaki, a fannin, da ke ci gaba da taimaka, wa wajen ci gaba habaka fannin tattalin arzikin kasar.
Shugaban ya bayyana cewa, NPA ba za ta yi kasa a guiwa ba, musamman, domin kamfanin ya samu damar jigilar manyan kayan aikin a kan lokaci, domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan da ya sanya a gaba.














