ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Obasanjo Ya Kafa Kwamitin Bincike Akai Na, Amma Bai Same Ni Da Laifi Ba — Atiku

by Abubakar Sulaiman
5 months ago

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa tsohon shugabansa, Olusegun Obasanjo, ya taɓa kafa wani babban kwamiti domin bincikensa a lokacin da yake kan mulki, amma binciken bai gano wata alamar cin hanci ko rashawa a kansa ba. Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Prime Time Special na gidan talabijin na ARISE News a ranar Laraba.

A cewarsa, an kafa kwamitin ne ƙarƙashin tsohon Babban Lauyan Tarayya, Bayo Ojo (SAN), inda ya haɗa da fitattun mutane kamar tsohon shugaban Hukumar EFCC kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a yanzu, Nuhu Ribadu, da kuma tsohon ministan Babban Birnin Tarayya kuma tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Nasarorin Gwamna Lawal A Zamfara Abin Mamaki Da Alfahari Ne – Obasanjo

ADVERTISEMENT

Obasanjo Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 700 A Kamaru

Atiku ya ce duk da cewa yana da kariya ta kundin tsarin mulki a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a lokacin, ya amince a cire wannan kariya domin a gudanar da binciken. Ya ce jami’an kwamitin sun zo ofishinsa da umarnin shugaban ƙasa na su bincike shi, kuma ya basu damar yin hakan ba tare da wata tangarɗa ba.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Ya jaddada cewa sakamakon binciken ya wanke shi daga duk wani zargi, yana mai cewa babu abin da aka samu a kansa. Ya ƙara da cewa zarge-zargen rashawa da ake alaƙanta shi da su tsawon lokaci ba su da hujja, illa kawai siyasa ce ke haddasa su.

Atiku ya bayyana lamarin a matsayin abin da bai taba faruwa ba, inda shugaban ƙasa ya ba da umarnin binciken mataimakinsa da ke da kariya ta doka, yana mai cewa wannan shi ne karo na farko da yake bayyana hakan a bainar jama’a.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
Ce-ce-ku-ce Kan Batun Biyan Bashin Naira Tiriliyan 3.3 Na Kuɗin Lantarki

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.