ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ce-ce-ku-ce Kan Batun Biyan Bashin Naira Tiriliyan 3.3 Na Kuɗin Lantarki

by Ra'ayinmu
5 months ago

Har yanzu a ƙasar, ana ci gaba da yin taba-taba kan batun ɗimbin kuɗaɗen da gwamnatin ke iƙirin ta baya, na bashin kuɗin wutar lantarki da kuma kamfanonin da ke rabar da Iskar Gas, amma duk da hakan, an gaza samarwa da ‘yan ƙasar, wadatacciyar lantarki.

Akasarin kamfanoni da asbitoci da sauransu da ke dogaro da yin amfani da lantarki, sun jima suna ci gaba da gudanar da ayyukansu ne, kawai, da Janareto waɗanda kuma wasu Janarentan, bas u da tabbas wajen gudanar da aiki, yadda ake buƙata.

Kano Pillars Ta Lallasa Bendel Insurance A Kano

ADVERTISEMENT

Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Tiriliyan ₦4.4 Na Shekarar 2026

A kwana-kwanan nan dai, shugaba Bola Tinubu, ya amince da a fitar da wuri na gugar wuri har Naira tiliyan 3.3, domin a biya kamfanonin da ke samar da lantarki, basukansu, tun daga tsakanin watan Fabirairun 2015 zuwa na Maris ɗin, 2025.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Tuni dai, kamfanoni sha biyar suka sanya hannun kan biyansu bashin da ya kai na kimanin Naira tiriliyan 2.3.Kazalika, gwamnatin taraya ta keɓe Naira biliyan 501, domin fara sauke wannan nayin, inda ta rabar da Naira biliyan 223.A ganin gwamnatin, biyan wannan bashin, abu ne da ke matuƙar mahimmanci, amma a ɓangaren ‘yan ƙasar, na ci gaba da yin tambaya, amma mai ya sa, lantarkin, baya iya wadatar da ƙasar.

A gefe ɗaya kuma, kamfanonin da ke samar da Isgar Gas, saboda bashin da suke bi, sun dakatar da turawa. Kamfanin masu kula da kuma gudanar da tafkin wutar lantarki na ƙasa wato NBET ya tantance cewa, Naira tiriliyan 1.8 da ƙarin wata Naira tiriliyan 4 da kamfanin samar da wutar lantarki 27 suka yi iƙirari suna bi, za a iya rage yawansu, amma ya danganta, idan an kai ƙarshen biyan bashin da kamfanonin ke bi.

Bugu da ƙari, a watan Okutoba, an rattaba yarjejeniyar biyan kamfanonin wani bashin da ya kai na Naira tirliyan 4, yanzu kuma ga wani bashin, da ake shirin ƙara biyansu. Fannin dai, na ci gaba da lashe kuɗaɗe amma har yanzu, ana ci gaba da barin ‘yan ƙasar, a cikin duhu dimɗin.

Ko a shekarun baya, gwamnatin ƙasar ta samar da ɗauki ga fannin da ya kai na sama da Naira tiriliyan 10, wanda za a iya cewa, kusan tun lokacin da aka sayar da hannun jarin fannin, a 2013, amma har yanzu, ba a iya samar da ƙarfin lantarkin da ya kai megawatt 5,000. Ra’ayin mu a nan shi ne, akwai banbanci kan biyan bashin, domin biyan bashi ba zai wani haifar da ɗa mai ido ba, matuƙar ba yiwa fanning aba ɗaya, garanbawul ba.

Misali, a wani taro a kwanan baya ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya gabatar da wasu alƙaluma a wani taro, inda ya shelanta cewa, kuɗaɗen shigar da fannin ya samar, sun ƙaru zuwa kaso 70 daga Naira tirliyan ɗaya, a 2023 zuwa Naira tiriliyan 1.7 a 2024.

Ya ƙara da cewa, samar da lantarki ya ƙara daga megawatt 13,000 zuwa megawatt 14,000, inda adadin megawatt ɗin, ta ƙaru zuwa 5,801 MW a ranar 4 na watan Maris ɗin 2026, amma duk da hakan, ‘yan ƙasar basu samun wadatacciyar lantarkin.

Sai dai, duk wannan nasarorin da ministan yayi iƙirarin fannin ya samu, amma bai taɓo batun lalacewar babban layin wutar lantarkin ƙasar, da ta yi ta aukuwa, a 2025 ba.Batun na sanar da lantarki mai ƙarfin megawatt 5,801, ga ‘yan ƙasar miliyan 220, hakan na neman zama tatsuniya ce, kawai.

Kamfanin samar da lantarki duk da kuɗaɗen da suke samu, amma su gaza, rabar da lantarkin, ga abokan huɗɗarsu A gefe ɗaya kuma, an shafe shekaru, kamfanonin, na ci gaba da tsula kuɗin lantarki ga masu amfani da ita, amma ba tare da sun samu wadacciyarta ba.

Hakazalika, batun shirin rabar da mitar lantarki na fadar shugaban ƙasa, da ake son rabawar da ‘yan ƙasar su miliyan 3.45, shi ma, kusan za a iya cewa, shirin ya sha ruwa.

Ya zama wajibi, batun na biyan bashin Naira tirilyan 3.3, ya zama an gindaya sharuɗɗa, musamman domin a kaucewa, koma ‘yar gidan jiya. Lalubo da mafita kan ƙalubalan samar da lantarki a ƙasar nan dai, za a iya cewa, batu ne, da ya gagagari sauran gwamnatocin baya, wanda za iya cewa, tun bayan da ƙasar, ta samu ‘yancin kai, daga gun turawan mulkin mallaka.

Za a iya cewa, ƙalubalen na ci gaba da faruwa ne, saboda rashin nuna kishi na tilasta ganin ana bin ƙa’ida. Biyan bashin abu ne, da ya zama wajibi, musamman domin saita fannin na samar da lantarki na ƙasar.

A saboda haka, ya zama dole a yanzu, gwamnatin ta nuna cewa, da gaske take, domin kawo ƙarƙashen ƙalubalen rashin wadatacciyar lantarki, a ƙasar.

Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Za A Tuhumi Bukola Saraki Da Abdulfatai Ahmed Da Laifin Kisa

Za A Tuhumi Bukola Saraki Da Abdulfatai Ahmed Da Laifin Kisa

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.