Kakakin Ofishin jakadancin Sin dake kasar Japan, ya soki lamirin ziyarar da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Japan suka kai haikalin Yasukuni, matakin da ya ce ya illata nasarorin da aka cimma bayan yakin duniya na biyu, da odar kasa da kasa da aka cimma bayan yakin.
Da yake amsa tambayar manema labarai dangane da batun a jiya Asabar, kakakin ya ce, ziyara da karrama haikalin Yasukuni, makwancin manyan kusoshin kasar da suka aikata munanan laifukan yaki yayin yakin duniya na biyu, wanda firaministanr kasar Sanae Takaichi, da wasu ministocin kasar, da manyan ‘yan siyasar Japan suka gudanar, abu ne da Sin ke matukar adawa da shi, kuma ta yi Allah wadai tare da gabatar da korafi mai karfi, da nuna rashin jin dadi kan hakan ga bangaren Japan.
Kakakin ya kara da cewa, Sin na kira ga bangaren Japan da ya yi matukar karatun ta nutsu dangane da laifukan da ya aikata a tarihi, ya yi koyi daga abubuwan da suka gabata, ya martaba alkawuran neman ci gaba ta hanyar lumana, kana ya aiwatar da matakai na hakika don kaucewa amfani da karfin tuwo, da dakatar da mummunan yanayin sake farfado da rundunar soji, da kaucewa sake sanya kasar a matsayi na abar tuhuma a tarihi. (Saminu Alhassan)













