Rasuwar muhimmin mutum da yake da kwarjini, faɗa aji,mai iya mu’amala da mutane daban- daban domin kuwa ya san mutane, kamar yadda suma su ka san shi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim ranar Litinin 29 ga Satumba 2014 rasuwar ta shi ta girgiza al’ummar Jihar Kano,ya bar babban lamarin da ba za a iya samun wanda cika gurbin da ya bari,a al’amarin Sarautar gargajiya ta Jihar Kano.
A shekarar 1935 ce a sananne kuma daɗaɗɗen Birnin Kano aka haifi aka haifi marigayi Turakin Kano, Hashim Abbas, Galadima,a shekarun da ya yi ko shakka babu yai amfani da damar da ya samu, wajen yin ayyuka ba kawai sai a masarautar ta Kano ba, ko Arewa amma Nijeriya baki ɗaya.
Yadda Galadiman Kano ya saba yi ma al’umma hidimomi wajen taimakawa Talakawa ga duk wani abinda ya shafe su.Hakan ya sa aka riƙa kiran sa da sunan‘Kakan Talakawa’ wannan shi ya sa bayan ƴan kwanaki da rasuwarsa mutane daban daban daga sassan Nijeriya, suka yi tururuwar zuwan gidan sa da ya ke a Jarkasa cikin birni, daura da fadar Sarkin Kano domin su isar da ta’aziyyarsu.
Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero shi ne ya naɗa Alhaji Tijjani Hashim,a matsayin Galidiman Kano a shekarar 1992, Galadiman Kano shin a kowa ne mai ƙarfi da mara ƙarfi a Nijeriya. Yana fara ganawa da mutane ne tun daga ƙarfe goma na safe zuwa ɗaya na dare in da yake saurarar kukansu ya kuma yi masu maganin abin.
A matsayin sa na Hakimin Birni har ila yau kuma Shugaban kwamitin lamarin kuɗaɗe na masarautar Kano marigayi Galadiman ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban Jihar.
Shi jikan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Abbas ya yi makarantar Firamare ta Bebeji a 1944 bayan ya kammalata ne sai ya wuci zuwa muhimmiya kuma sananniya makarantar ake kira da suna Kano midil Sukul, wadda yanzu ake kira da sunan Kwalejin Rumfa 1948.
Ya bar makarantar ne bayan ya yi shekara uku inda ya fa aiki a sashen kulawa da lafiyar dabbobi na Hukumar lardi wadda take yanzu a matsayin ƙaramar hukuma. Daga ƙarshe dai jinin Sarautar ya shiga harkokin sarauta a shekarar 1956 lokacin da ya tsaya takarar zaɓen zuwa majalisar Arewa ya kuma samu nasarar lashe zaɓen, a mai wakiltar Sumaila, a muƙamin da shi ne ya buɗe ma shi babi wajen samun nasara a harkokin siyasa.
A shekarar 1966 ce, lokacin da Sojoji suka karɓe karagar mulki sai aka naɗa shi Ɗan Isan ci gaban al’ummar Jihar Kano, matsayin da shi ne ya buɗe ma shi hanya ta samun wurin zama na babbar hanya ta kasancewa da faɗa aji kan lamarin sarautar gargajiya ta Kano. An ɗaga matsayin shi zuwa Turakin Kano a shekarar 1976, wannan muƙami na Turaki shi ya ba shi dama ta kasancewa mamba na Masarautar Kano amma bayan shekaru 13,a shekarar 1989 ce aka,ƙara ɗaukaka darajar muƙamin sa zuwa Dan Iyan Kano.
Isma’il Mudashir, Kano shi ne ya rubuta wannan tarihin rayuwar cikin Turanci Jaridar Daily Trust ta wallafa shi ranar4 ga Oktoba 2014. Jaridar Leadership Hausa ta fassara saboda muhimmancin sa.













