Assalamu alaikum warahmatullah!da fatan an yi Sallah lafiya ,Allah ya maimaita mana, a wannan makon muna dauke ne da tsokacin ku ne a kan yadda kuka gudanar da bukukuwan Sallar Layya. Da abubuwa da ba zaku manta da shi ba? Ga dai irin yadda kuka bayyana ra’ayoyin naku.
Ibrahim Hassan Baban Adila
Gadiya ga Allah Madaukakin Sarki wanda ya bamu ikon ganin ranar sallah, abinda ba damu mantaba da shi ba shi ne ganin yadda Alhazai suka yi aikin haji a wannan shekara a kasa Mai tsarki duba da yadda tuntashin mu yawanci bamu taba ganin an dakatar da yin aikin ba a kasa Mai tsarki, daga karshe mu mutanen Nigeria mungudanar da sallah cikin koshin lafiya da fatan Allah yamai maita mana ya bamu ladan ibada da mu ka yi Ameen ya Allah.
Baban Khairat
Alhamdulillaah mun gudanar da bukukuwan sallah cikin koshin lafiya, In dai akwai lafiya, shi ne komai
Mahdee Bashir
Sallah mun yi ta lafiya duk da halin da ake ciki na matsin rayuwa don kuwa yawancin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihiohi basu samu albashi ba amma muna godiya da yake mun yi a cikin koshin lafiya
Aliyu Hassan Kumo
Masha Allah. Hidiman Sallah saidai godiya. Addu’ar mu shine, Allah ya yassare mana al’amura, ya kuma maimaita mana
Shamsuddeen Ahmad Idris
Amin ya Allah. Bikin sallah dai an yi shi yadda aka saba sai dai walwalar cikinsa kam ba kamar yadda ake yi kullum ba. Wasu wuraren ma in kashi ga kamar ba sallah ake yi ba. Ko kamshin nama da da muke ji ya mamaye unguwa gaba daya a lokacin sallah, yanzu kam sai ka wuce gida a kalla uku, kafin kaji kamshi a gida daya. Allah ya kyauta
Abinda ba za mu mantaba kuma shi ne wani hoto da ya zagaya yanar gizo da hoton shugaban kasa zai yanka wani dan karamin rago wai saboda ganin yadda tattalin arziki ya rushe a Nijeriya, tabbas ba zan manta da wannan rainin hankalin ba. Ina mana barka da sallah!!!
Muhd Basheer Sa’ad
Abu mai dadi gare ni da ba zan manta dashi ba shi ne, na yi Sallar idi tare da mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mai Girma Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk, Allah ya maimaita mana, Amin.
Hadiza Bello Hamza
Alhammdulillah, mun yi Sallah lafiya, da fatan Allah ya karba mana dukkan ibadunmu, ina mika gausuwa ga dukkan ma’aikatan jaridar Leadership Hausaa, Allah ya kara daukaka, amin.
Ahmad Bello Hamza
Mun yi Sallah lafiya kalau, mun gudanar da adu’o’in neman zaman lafiya ga kasar mu Nijeriya, Allah ya kawo mana karshen lamarin matsalar tsaro, Allah ya taimaki jami’an tsaronmu Ya kare mana su