ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 30, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ragin Farashin Fetur: Tasirinsa Ga Sufuri, Farashin Kayan Masarufi

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago
Fetur

A duk lokacin da farashin litar man fetur ya sauya a Nijeriya ko sama ko ƙasa hakan na da tasiri kai-tsaye a kowane lungu da saƙo na rayuwar al’umma. Bayan saukar farashin da aka samu a gidajen mai sakamakon sauye-sauyen kasuwa da matakan rage matsin tattalin arziƙi, ƴan ƙasa da dama sun fara zura ido don ganin yadda wannan sauyi zai sauƙaƙa raɗaɗin tsadar rayuwa da aka shafe lokaci ana fama da shi.

Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar yin ragin Naira ₦66 kan kowacce litar Fetur a gidajen man NNPCL.

Fetur

Ga yadda wannan sauƙin farashi ke shafar muhimman ɓangarorin rayuwa da tattalin arzikin ƙasa:

ADVERTISEMENT

1. Kuɗin Sufuri: Farkon Matakin Samun Sauƙi

Sufuri shi ne ɓangare na farko da ke fara bayyana tasirin duk wani sauyi a harkar man fetur.

  • Fasinjojin Cikin Gari: Duk da rashin ba mai yawa ba ne sosai, amma direbobin motocin haya, ƴan adaidaita sahu, da masu babura a manyan birane sun samu raguwar kuɗin da suke zuba wa a motocinsu, wanda hakan zai iya sanya wa a samu ragin farashin abun hawa.
  • Tafiye-Tafiyen Dogon Zango: Saukar kuɗin mai na rage kashe kuɗaɗen motocin haya masu ɗaukar fasinjoji tsakanin jihohi, wanda hakan ke sauƙaƙa wa matafiya, musamman ma’aikata da ƴan kasuwa masu zirga-zirga a kai a kai.

2. Kayan Masarufi da Abinci:

Hanyar dakon kaya ita ce jigon da ke sarrafa farashin abinci a kasuwannin Nijeriya. Saboda yawancin kayan lambu da hatsi na tasowa ne daga gonakin karkara zuwa manyan kasuwannin birane, mafi yawan lokuta farashin fetur ne yake yanke hukuncin yadda farashin dakin kaya zai kasance.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

Raguwar farashin fetur na rage kuɗin lodi da kuɗin hayar motocin tirela da na ƴan koli. Wannan na ba dillalan kasuwa damar sayar da kayayyaki a farashi mai sauƙi ba tare da sun tafka asara ba, wanda ke taimakawa wajen daidaita hauhawar farashin kayan abinci. Wannan ƙaramin ragin ana sa ran zai kawo sauƙin kaya ko ba mai yawa sosai ba yadda ake fata.

3. Rage Matsin Tattalin Arziƙi

A lokacin da farashin mai ya yi tashin gwauron zabi, kaso mafi tsoka na albashi ko kuɗin shigar talakawa na ƙare wa ne a kan kuɗin mota da wajen man janareto.

Wannan ƙaramin Sauƙin farashin fetur da aka samu na nufin:

  • Magidanta: Da yiwuwar iyalai su samu ƴar rarar kuɗin da a baya ke ƙarewa a kan fetur domin magance sauran buƙatu na lafiya, da ilimin yara, da inganta ingancin abincin da suke ci a gida.
  • Tsarin Kasafin Kuɗi: Wasu iyalai zai taimaka musu yin kintace da tsara kuɗin shigarsu ba tare da fargabar karyewar darajar kuɗin rana ɗaya ba.

4. Tallafi Ga Ƙananan Sana’o’i (MSMEs)

Man fetur ba wai kawai na mota ba ne; shi ne tushen wutar lantarki ga miliyoyin ƙananan ƴan kasuwa. Masu sana’ar aski, ko teloli, da masu walda, ko masu sana’ar kayan sanyi na abin sha, da masu aikin kwamfuta sun dogara ne kacokan kan janareto don gudanar da sana’o’insu.

Raguwar farashin mai na rage musu kudin sayen man fetur na kullum, wanda hakan zai iya haɓaka ribarsu, kuma yana hana su ƙara farashi ga kwastomomi. Wannan na ba da kariya ga ayyukan yi tare da farfaɗo da kasuwancin matasa da dama.

Duk da cewa wannan sauƙi na farashin fetur ba mai yawa ba ne kuma ba zai warware matsalolin tsadar rayuwa mai yawa ba, amma hakan zai zama babban mataki na farfaɗo da fatan al’umma.

A hannu guda kuma, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC (Trade Union Congress), Kwamared Festus Osifo, ya bayyana cewa duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na rage farashin man fetur, har yanzu farashin ya yi wa ma’aikatan Nijeriya tsada sosai kuma ya fi ƙarfinsu.

Ya buƙaci a hanzarta inganta matatun man cikin gida domin kawo ƙarshen dogaro da man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje, a faɗaɗa shirin motocin safa masu amfani da iskar gas (CNG), sannan a tabbatar da cewa dukkan jihohi da hukumomi sun aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi domin ƙarfafa ma’aikata su iya fuskantar tsadar rayuwa.

Fetur
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu
  • Abubakar Sulaiman
    Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

MASU ALAKA

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu
Labarai

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

October 29, 2026
Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano
Manyan Labarai

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

October 29, 2026
Kotu Ta Umarci Uzodinma Ya Daina Kiran Kansa Ɗan Takarar APC Na Sanatan Imo Ta Yamma
Manyan Labarai

Kotu Ta Umarci Uzodinma Ya Daina Kiran Kansa Ɗan Takarar APC Na Sanatan Imo Ta Yamma

October 29, 2026
Next Post
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Mahaukaci Ne Kaɗai Zai Zaɓi Tinubu A 2027 - Amaechi

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

October 29, 2026
Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

October 29, 2026
An Kammala Cikakken Zama Na JKS Inda Aka Amince Da Kudurin Ci Gaba Da Bin Cikakken Tsarin Shugabancin Kai Na Jam’iyyar

An Kammala Cikakken Zama Na JKS Inda Aka Amince Da Kudurin Ci Gaba Da Bin Cikakken Tsarin Shugabancin Kai Na Jam’iyyar

October 29, 2026
Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyya Game Da Karon Da Jiragen Kasa Suka Yi A Spain Da Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane

Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyya Game Da Karon Da Jiragen Kasa Suka Yi A Spain Da Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane

October 29, 2026
Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu

Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu

October 29, 2026
Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

October 29, 2026
Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

October 29, 2026
Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

October 29, 2026
NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

October 29, 2026
Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

October 29, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.