ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

REA Da NCK Sun Ƙulla Yarjejeniya Da Jigawa Don Samar da Wutar Lantarki

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
Jigawa

Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA) ta sanar da cewa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tare da Gwamnatin Jihar Jigawa, Nigerian Commodity Exchange (NCX) da kamfanin Astound Power Limited domin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 7 (MW 7). An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a yayin Taron Zuba Jari na Jigawa (J-Invest 2026), inda za ta tallafa wa haɗin gwuiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu a cibiyoyin masana’antun noma guda bakwai da ke jihohin Jigawa, da Taraba, da Kaduna, Kebbi, da Ekiti, da Osun da Ebonyi.

REA ta bayyana cewa, a ƙarƙashin yarjejeniyar za ta gina kayayyakin samar da wutar lantarki domin tallafa wa tsarin ban ruwa da cibiyoyin sarrafa amfanin gona. Haka kuma, NCX za ta riƙa bai wa manoma da masu tara amfanin gona da suka cika ƙa’idoji takardun shaidar ajiya na rumbunan ajiyar kayayyaki da ke ƙarƙashin tsarin NCX, domin sauƙaƙa fitar da amfanin gona zuwa ƙasashen waje.

Da yake jawabi yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, Manajan Daraktan REA, Dakta Abba Aliyu, ya ce ingantacciyar wutar lantarki na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo masu zuba jari, da bunƙasa masana’antu da kuma samar da ayyukan yi a Nijeriya. Ya bayyana cewa haɗa makamashi mai tsafta da aikin noma zai ƙara ƙarfafa samar da wadataccen abinci, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa da kuma ƙara darajar tattalin arziƙin manoma da al’ummomin karkara.

ADVERTISEMENT

Dakta Aliyu ya ƙara da cewa makamashi shi ne ginshiƙin ci gaban kasuwanci da bunƙasar al’umma, yana mai jaddada cewa zuba jari na bin inda ake da damarmaki da kuma amincewa da tsarin gwamnati.

Ya ce ɗaya daga cikin manyan saƙonnin da gwamnati za ta iya isarwa ga masu zuba jari shi ne nuna ƙudirin samar da yanayin da kasuwanci zai bunƙasa. Taron J-Invest 2026 ya haɗa masu tsara manufofi, da masu zuba jari, da abokan hulɗar ci gaba da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu domin tattauna hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Jigawa, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buɗe taron a hukumance.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Jigawa
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
  • Abubakar Sulaiman
    Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

MASU ALAKA

Jigawa
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
Labarai

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Labarai

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Next Post
Sarkin Zazzau Ya Umarci A Soke Wasu Al’adu Da Ke Kawo Wa Aure Cikas

Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Jigawa

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.