ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi

by Sulaiman
7 months ago
Iran

Tun bayan ɓarkewar zanga-zangar tsadar rayuwa da ta rikiɗe ta koma tarzomar kin jinin gwamnati daga wasu acikin al’ummar Iran a ƙarshen Disamba 2025 da farkon Janairu 2026, akwai karuwar muhawara tsakanin Iran da Amurka, ciki har da tsauraran kalamai da barazanar juna tsakanin shugabannin kasashen biyu. 

Amurka ta nuna goyon baya ga masu zanga-zangar ta Iran, tana kira ga gwamnatin Tehran da ta daina yin amfani da karfi wajen murkushe su, wanda hakan ya sanya Shugaba Donald Trump ya yi barazanar cewa, Washington na iya “taya” masu zanga-zangar ko ma ɗaukar matakai idan hukumomin Iran suka yi amfani da karfi wajen kashe mutane.

ADVERTISEMENT
  • Yanzu- Yanzu An Sako Masu Ibadar da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
  • Ƴansanda 5,000 Za Su Yi Ritaya A 2026

A nata martanin, Iran ta zargi Amurka da tsoma baki sosai a harkokinta na cikin gida, tana cewa wannan wani yunkuri ne na kifar da gwamnatinta, wanda kuma ba za ta lamunci hakan ba. A cikin martanin da aka fitar a hukumance, Tehran ta yi gargaɗin cewa, duk wani yunƙurin Washington na kai hari Tehran zai dagula zaman lafiyar yankin, inda ta sha alwashin mayar da martanin hari kan duk wani sansanin sojin Amurka dake yankin da kuma duk kasar da ta bari Amurka ta yi amfani da kasarta ko sararin samaniyarta wurin kai mata (Iran) hari.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Amurka dai, tuni ta tura jiragen yakinta na ruwa masu ɗaukar jiragen yaki zuwa tekun kusa da Iran, inda ita kuma Iran ta sha alwashin mayar da kakkausar martani.

Tataburzar siyasar da ake yi game da siyasar yankin gabas ta tsakiya na ci gaba da tona asirin yadda turawan yamma ke ci gaba da cin tuwo da miyar bara. Tun daga rikicin yankin Palasdinu zuwa abubuwan da ke faruwa kwanan nan kan batun Iran, duk da a zahiri suna haifar da koma-baya, amma kuma a badini suna kara mayar da burin yammacin duniyar tamkar mafarkin da ba zai taba zama gaskiya ba saboda kiyayyarsu da take karuwa a zukatan al’ummomin yankin.

Bayan harin Amurka da Isra’ila na shekarar 2025 da gajeren rikicin da ya biyo baya, wasu masana sun lura cewa maimakon hakan ya raunana Iran daga zuci, sai ya kara mata kwarin gwiwar karfafa matsayinta na tsaro tare da kara zurfafa dangantakarta ta diflomasiyya musamman da manyan kasashe masu fada-a-ji a yankin Asiya.

Fankamar yammacin duniya ita ce karfin tattalin arziki da kuma makamai. Amma kuma yaki daga zuciya ake cin nasararsa. Ko an zubar da jini, wutar gaba mai ruruwa a zukatan al’umma ba ta mutuwa, sai dai ta sake rincabe nasarar da aka ci. Ga misalai nan a kasashen da Amurka da kawayenta suka afka musu, kamar Afghanistan, Iraqi da Libiya da kuma sauran kasashen da suka yi musu munakisa.

Duk da cewa takunkuman da aka kakabawa Iran sun lalata tattalin arzikinta kuma sun shafi rayuwar talakawan kasar, amma kuma ba su samar da tasirin siyasa da Washington ta yi tsammani ba. A halin yanzu, galibin fushin da al’ummar Iran ke yi bisa yanayin da aka jefa su ciki na kara karkata zuwa ga wadanda suka kakaba takunkuman duk kuwa da zanga-zangar da aka yi kwanan baya, saboda haka, matsin tattalin arzikin yammacin duniya bai ba su asalin muradin abin da suke nema ba.

A wani tsokaci da ya yi ta kafar sada zumunta, wani farfesa daga tsangayar nazarin muhalli ta Jami’ar BUK dake Nijeriya, Malam Aliyu Salisu Barau ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashen yammacin duniya su fahimci rashin tasirin dabi’ar tilastawa a wannan zamani, inda ya kafa hujja da cewa, sassauta takunkumi da inganta yanayin jin kai na iya sauya ra’ayoyin al’umma fiye da tayar da husuma. Kazalika, kyakkyawar diflomasiyya da hulda ta tattalin arziki na iya samar da yanayi mafi dacewa na ci gaba da kuma zaman lafiya na dogon lokaci.

Komai za mu ce, sai dai muce, Allah shi kyauta.

Iran
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano

HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.