ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, June 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauki (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani and Sulaiman
5 months ago
SAW

…ci gaba daga makon da ya gabata.

 

Mun zayyano wasayal Ashri (10) a karatun farko na makon da ya gabata, yanzu za mu dora daga na 11:

ADVERTISEMENT

11- An haramta muku auren uwayenku mata, da ‘ya’yanku mata, da ‘yan uwanku mata, da ‘yar uwar mahaifinku, da ‘yar uwar mahaifiyarku, da ‘ya’yan ‘yan uwanku mata, da ‘ya’yan ‘yan uwanku maza, da uwayenku da suka shayar da ku nono, da ‘yan uwanku da kuka sha nono tare, da agololinku da kuka raina a gidanku, da matayen ‘ya’yanku, kuma karku hada ‘yan uwa biyu.

Har ila yau, an haramta muku auren kowace mace da take katangaggiya (wacce take da wanda yake kula da ita ba miji ba, sai kun nemi izini daga wannan da ke kula da ita, in babu sai hukuma ta yi), ko kuma a yi kwantiragin auren – magana ce mai fadi.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Banda wannan abun da muka lissafo, komai an halasta muku amma sai kun nema da kudinku sannan ku aura ko kuma ku yi kwantiragi, kuma ku kare kanku daga taruwa akan saduwa da mace daya ko matan su taru akan namiji daya.

Akwai haram a bangaren abinci, ga su kamar haka: An haramta muku mushe, da jinin da ya zuba, da naman Alade, da dabbar da aka yanka ba da sunan Allah ba, da dabbar da aka shake har ta mutu, da dabbar da aka buga a kai ta mutu, da wadda ta fado da sama ta mutu, da wacce ‘yar uwarta ta soka da kaho ta mutu, da wadda namun daji suka ci wani sashinta har ta mutu, da dabbar da aka yanka wa wani mutum-mutumi ko wani jarumi da sunan bauta ba wacce aka yanka a liyafar bikin tunawa da wasu jarumai ba, wannan halal ne. Amma duk wanda ya matsu, ba laifi zai iya cin duk wannan abincin da muka lissafo.

Bugu da kari, Allah ya haramta muku riba, sannan mafi hadari, yi wa Allah karya “wa antakulu alallahi mala ta’alamun.”

Riba, ana nufin ajiye wasu kudade da nufin bayarwa rance, amma za a dawo da fiye da abun da aka karba rancen. Amma wasu taron jama’a masana kasuwanci ko wani kamfani da zai amsa kudaden jama’a domin yin kasuwanci sannan a raba ribar da aka samu, wannan kasuwanci ne na “Halal” ba “Riba ba”.

Alhamdulillah, wannan Haram-haram da muka lissafo, babu wata Majalisar Dokoki a duniya da za ta halasta su.

Bayan ‘HARAM’, akwai ‘HANI’, shi ba haram ba ne, “wa kad fassala lakum ma harrama alaikum – an fayyace muku duk abin da aka haramta muku” a bangaren hani kuma, Ubangiji cewa, ya yi, “wal takun minkum ummatun yad’una ilal kairi wa ya’amuruna bil ma’arufi wa yan hauna anil munkari – a samu wata al’umma daga cikinku da za ta zama tana kira zuwa ga aikata alkairi da hani ga aikata abin ki”.

Hakan na nuni da cewa, Majalisar Dokoki, za ta iya zama ta hana wani abu in ya zama aikata wannan abun zai kawo cikas ga kasa.

 

Abu uku ne kadai ke dakile ‘HALAL’:

1 – Abin da halittarka ba ta so, misali, abincin da kana gani ko ka ci, za ka fara Amai ko kuma zai sauya maka tsarin jikinka.

2 – Abin da al’adar garinku ba ta so, don a zauna lafiya, sai a bar wannan abun amma in ka koma wani gari da wannan abun babu komai yin shi a wurinsu, babu laifi ka yi.

3 – Abin da kundin tsarin mulkin kasa ya hana. Misali, zamanin COBID-19, kasa ta hana gudanar da duk wani taron jama’a a cakude.

Shi ‘HANI’ ba har abada ba ne, na dan wani lokaci ne. Don haka, ya dace al’umma ta yi kokarin fayyace bambanci tsakanin ‘HARAM’ da ‘HALAL’.

Da yawa, HANIN da yazo a sunna, wannan abun da muka ambata yake nufi, – na dan wani lokaci.

IBADA ta rataya ne tsakanin bawa da Ubangijinsa, ranar lahira zai samu ladansa, amma KYAWAWAN DABI’U na duk halitta ne. Idan muka yi kyawawan dabi’u, za mu zauna lafiya, kasa za ta zauna lafiya, za mu yi ibada cikin nutsuwa da zaman lafiya. Lahira babu kyawawan dabi’u, wa za ka yi wa gaskiya, ma’ana akwai karya kenan. Hisabi kuwa, na lahira ne. Mu zauna da kyawawan dabi’u, mu karbi juna. Shari’a tana da iyaka “Hududu” ce, kar mu tauye ta.

In muka kalli Annabi SAW ta wannan abubuwan Uku (3) da muka lissafo: An aiko Annabi SAW ga duk halitta (kyawawan dabi’u), an aiko Annabi SAW rahama ga duk halitta (Annabin sauki, jinkai da tausayin halitta), sannan kuma an aiko Annabi SAW ya zama cika makon Annabawa (ya kawo sauki, ya cika shari’o’in sauran Annabawa), za mu zauna lafiya da juna.

Yayin da yake amsa tambaya ga wani bawan Allah da ya nemi Mai Diwani ya yi kira ga masu da’awar soyayyar Annabi SAW, kuma ba sa kula da yin Sallah, shehin ya ce, ya dace mu fahimci cewa, soyayya daban aiki daban! Sabida Hadisin wani sahabi da ya shawo giya, Annabi SAW da sahabbansa SAW, suna dukansa domin ladabtarwa sai sayyadina Umar ya hada da zagi, take Annabi SAW ya ce masa, ya Umar kar ka tsine wa dan uwanka, yana son Allah da Annabinsa. Son Allah da Annabinsa daban, jarrabawa ko ibtila’i ta inda Allah ya ce da dan Adam mai rauni, har ya fada cikin wannan ibtila’i daban.

An tambayi Imamul Junaid cewa, ko Arifa (masanin Allah) zai iya sabo? Sai ya ce, “wakanna amrullahi kadaran makdura – shi lamarin Allah, kaddara ce da yake kaddara ta”.

Shari’a karatu ce, Ana cewa, “Barna babba – Malami mai keta haddi, amma wanda ya fi shi barna – jahili mai riko da addini”, sabida wahi hukuncin, sabanin mazhaba (Malikiyya, Shafi’iyya, Hanafiyya da Hambaliyya) ne. Amma duk wanda ya yi da’awar soyayyar Annabi SAW, to ya kiyaye barna.

Daga karshe, Almaddah Mai Diwani, ya yi karin haske da cewa, kuskure ne cewa, duk abin da Annabi SAW bai yi ba, a bar shi. Abin da Alkur’ani ya tabbatar shi ne, “wama atakumurrasulu fakuzuhu, wama nahakum anhu fantahu – duk abin da ma’aiki SAW ya kawo muku, ku rike shi, kuma duk abin da ya hane ku, ku hanu” iya karfinku. Sabida ita Shari’a, so take taga hukunci a bayyane.

Akwai abubuwan da Annabi SAW ya bari da yawa sabida al’adarsa (Larabawa) ba sa yi, kamar cin naman Damo, akwai abin da mantuwa ne, kamar rafkanwar Sallah, akwai barin wani abu, sabida tsoron kar a farlanta, kamar Sallar tarawihi. Wata rana ya fito cikin dare ya yi sallah, wadanda ke cikin masallacin duk suka bi shi, washe gari suka fadawa mutanen cikin gari, da wani daren ya zagayo, Masallaci ya cika makil, wani daren da ya zagayo, Masallaci da unguwa duk sun cika, Annabi SAW ya ki fitowa, sabida tsoron kar a farlanta wa al’ummarsa. Sai hakan ya zama sunnar Sayyadina Umar da duk wanda ya ga dama, ko ka yi a masallaci ko ka yi a gida.

Har ila yau, akwai abin da Annabi SAW bai yi ba, sabida abun bai zo masa ba, misalin hawa mimbari, sai da ga baya ta faru bayan zuwan wata baiwar Allah daga Habasha ta nuna yadda sarakuna ke yin mimbari su hau su yi lacca akai ga mutanensu, sannan ne ta saka wani bawanta ya yi, kuma Annabi SAW ya hau ya ji dadinsa. Akwai tsoron, kar Annabi SAW ya sauya zuciyar wasu, sabida a lokacin aka fara musulunta, kamar soyayyar wareware ginin Ka’aba a yi mata kofa biyu, kowane musulmi ya rika shiga.

Don haka, batun Annabi SAW bai yi ba, ba hujja ba ne, amma Annabi SAW ya hana, shi ne hujja.

Asalin komai, HALAL ne sai wanda Shari’a ta HARAMTA, a wurin daukar rai, komai HARAM ne sai wanda Shari’a ta HALASTA.

in ba haka ba, kusan komai da muke amfani da shi a yanzu, Annabi SAW bai yi amfani da shi ba.

Annabi SAW
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ posts Bio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari
Annabi SAW
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 8 Zuwa Sararin Samaniya
  • Sulaiman
    Mujallar Qiushi Za Ta Buga Muhimmin Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Ciyar Da Ilimi, Fasaha Da Kwararru Gaba Tare”
  • Sulaiman
    Amfani Da Matar Soja Wajen Isar Da Sakon Bukata
  • Sulaiman
    Ɗan Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan NDC A Zaɓen Kano na 2027

MASU ALAKA

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

May 29, 2026
Next Post
Trump Ya Yi Barazanar Sake Kai Hari Nijeriya Kan Zargin Kisan Kiristoci

Trump Ya Yi Barazanar Sake Kai Hari Nijeriya Kan Zargin Kisan Kiristoci

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Hauhawar Farashi Ya Kai Kashi 15.93 Cikin 1000 A Watan Mayu A Nijeriya – NBS

Hauhawar Farashi Ya Kai Kashi 15.93 Cikin 1000 A Watan Mayu A Nijeriya – NBS

June 16, 2026
Sojoji Sun Ceto Matar Tsohon Kakakin Hedikwatar Tsaro A Katsina

Sojoji Sun Ceto Matar Tsohon Kakakin Hedikwatar Tsaro A Katsina

June 16, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

Atiku Ya Soki Hukuncin Kotu Kan Ba Da Umarnin Soke Rajistar ADC

June 16, 2026
Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 8 Zuwa Sararin Samaniya

Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 8 Zuwa Sararin Samaniya

June 15, 2026
Mujallar Qiushi Za Ta Buga Muhimmin Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Ciyar Da Ilimi, Fasaha Da Kwararru Gaba Tare”

Mujallar Qiushi Za Ta Buga Muhimmin Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Ciyar Da Ilimi, Fasaha Da Kwararru Gaba Tare”

June 15, 2026
Amfani Da Matar Soja Wajen Isar Da Sakon Bukata

Amfani Da Matar Soja Wajen Isar Da Sakon Bukata

June 15, 2026
Ɗan Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan NDC A Zaɓen Kano na 2027

Ɗan Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan NDC A Zaɓen Kano na 2027

June 15, 2026
2023: Tinubu Ya Zaɓi Kashim Shettima A Matsayin Mataimaki

Shin Har Yanzu Shettima Ne Abokin Takarar Tinubu?

June 15, 2026
Dunkulewar Kasa Shi Ne Burin Bai Daya Na Jama’ar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan

Dunkulewar Kasa Shi Ne Burin Bai Daya Na Jama’ar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan

June 15, 2026
Daraktoci Da Jami’an FCT 7 Na Fuskantar Tuhume-tuhume Kan Badakar Fili

Mariya Mahmoud: Aiki A karkashin Jagorancin Wike

June 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.