A matsayin babbar kasa a duniya, Sin na ci gaba da samun kwarewa a fannin ikonta da kuma kwazon gina kanta, kana da samar da gudunmawa ga ci gaban duniya baki daya. Bisa hakan ne ma ta gabatarwa duniya shawarar bunkasa ci gaban duniya ko GDI a takaice, wadda manufarta ita ce taimakawa sassa kasa da kasa da dabarun cimma burikansu, da cimma nasarar ajandar MDD ta wanzar da ci gaban duniya.
Kazalika, shawarar ta zo a gabar da duniya ke fama da gibin ci gaba wanda ke kara fadada a zahiri.Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar a shekarar 2021, Sin ta mayar da hankali ga yayata alfanunta, da nufin baiwa dukkanin kasashen duniya, musamman ma masu tasowa damar amfana daga damarmakin ci gaba.
Kuma jim kadan da kaddamar da ita, shawarar GDI ta samu matukar karbuwa daga MDD, da hukumomin kasa da kasa da ma akasarin kasashen duniya, duba da yadda ta fayyace dabarun warware batutuwan gaggawa na al’ummun duniya, irinsu zaman lafiyar duniya, da ci gaba da kuma hadin gwiwa.Ko shakka babu, sassan kasa da kasa suna fuskantar manyan kalubale ta fuskar aiwatar da ajandar wanzar da ci gaba ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, yayin da gibin ci gaban duniya ke kara fadada. Har ila yau, batutuwan ci gaban duniya ba sa samun kulawar da ta kamata.
Wasu kasashen duniya na daukar matsaya ta kashin kai, da baiwa kasuwa kariya, kana wasu na kafa shingaye, da kokarin mayar da wasu saniyar-ware, matakan da ke gurgunta tsarin samarwa da rarraba hajojin masana’antun kasa da kasa. Dukkanin wadannan dalilai da ma wasu, suna taka rawa wajen fadada kalubalen siyasar yankuna da duniya ke fama da su, suna kara ta’azzara sauyin yanayi, da matsalar makamashi da ta kamfar abinci, tare da illata moriyar kasashen duniya baki daya, musamman ma kasashe masu tasowa, tare da mayar da hannun agogo baya game da burin cimma nasarar ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030.
To sai dai kuma, bisa kwarewar da ta samu a tsawon shekaru, musamman ta fuskar gwada dabarun samar da ci gaba, da ayyukan yaki da fatara a yankunan karkara, da sauran manufofi na mayar da al’umma gaban komai, kasar Sin ta baiwa duniya gudunmawar shawarar GDI. Kuma yayin da ake cika kusan shekaru biyar da gabatar da ita, shawarar na samun manyan nasarori daga matakin gabatarwa zuwa na aiwatarwa.
A yanzu haka, tana samun karin goyon baya, inda karin kasashe sama da 130 suka shiga cikinta, baya ga hukumomin kasa da kasa masu yawa, kana ya zuwa yanzu, sama da kasashe 80 suka shiga rukunin abota na wannan shawara ta GDI, matakin da ke tabbatar da kabuwarta da kuma alfanunta ga duniya. (Saminu Alhassan)














