Ba wai mutanen Jihar Zamfara kadai ba ne ke zaman shaida ba kan gagarumin sauyin da ke gudana a fadin jihar cikin shekaru uku da suka gabata a karkashin “Shirin Ceto Jihar Zamfara” na Gwamna Dauda Lawal ba. Abin da mutane da dama ba su sani ba shi ne wannan sauyi na musamman da ke gudana a dukkan muhimman fannoni a jihar ya dauki hankalin shugabannin hukumomin tsaro a Nijeriya, Majalisar Dinkin Duniya, hukumomin gwamnati da kuma manyan kungiyoyin bayar da agaji da masu bayar da tallafi na duniya da sauransu.
Zamfara Za Ta Koma Kamar Dubai – Ministan Tsaro Musa
A ranar 18 ga Fabrairu, 2026, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya yi jinjijnar musamman ga Gwamna Dauda Lawal bisa samar da kayan aikin soji ga rundunonin tsaro domin karfafa yaki da da ‘yan bindiga a jihar.
Janar Musa ya ziyarci a Gusau, babban birnin jihar ne domin kaddamar da motocin yaki masu sulke guda 25 na zamani da kuma jirgin sa- ido marar matuki mai ingancin da zai iya yin aiki har na tsawon mita 80 a sama da rufe tazarar kilomita 50 tare da ci- gaba da aiki na tsawon awanni takwas, wadanda gwamnatin jihar ta saya.
Ministan Tsaron ya bayyana cewa sayen motocin yakin masu sulke da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi ya nuna jajircewar gwamnan. “Daga abin da na gani, idan aka ci- gaba da haka a wa’adi na biyu, jihar Zamfara za ta koma kamar Dubai” in ji Janar Christopher Musa.
“Tsaron rayuka da dukiyoyi ya fi kowace irin siyasa, bambancin jam’iyya ko ra’ayi muhimmanci, shi ya sa nake matukar farin cikin kasancewa a nan. Kasancewar ka jagoran wannan jiha da ke aiki domin kowa, ya nuna ka na da bambanci kuma ka na da kudurin kwarai a abin da kake yi.”
“Akwai bukatar juriya da kwarin guiwa ga shugabannin jiha su sadaukar da kudade masu yawa domin tabbatar da tsaron jama’a, kuma abin da ya fi burgewa shi ne duk an biya kudin baki daya. Wannan wani sako ne ga masu tayar da zaune tsaye.”
Lawal Ya Fitar Da Zamfara Daga Mawuyacin Hali – Shugaban NISS, Chif Odama
A ranar 29 ga Oktoba, 2025, aka yaba da hobbasar kwazon Gwamna Dauda Lawal lokacin da aka gayyace shi a matsayin bako mai jawabi ga mahalarta babban kwas kan Gudanar da Harkokin Leken Asiri (EIMC) 18 a cibiyar nazarin ayyukan tsaro da ke Abuja.
Taken taron shi ne: “Rawar da kungiyoyin da ba na gwamnati ba ke takawa a harkokin tsaro: Batutuwa, kalubale da hasashen samar da zaman lafiya da ci-gaba a Afurka- Daga mahangar Jihar Zamfara.”
Kwamandan cibiyar nazarin ayyukan tsaro ta kasa, Joseph Obule Odama, ya bayyana cewa Gwamna Lawal ya sauya fasalin Jihar Zamfara daga gurbataccen hali zuwa ingantaccen yanayi duk da manyan kalubalen da ya tarar a kasa a yayin da ya karbi mulki.
Mista Odama ya bayyana cewar Gwamna Lawal ya fuskanci kalubale sosai a lokacin yekuwar neman zabe amma kuma ya samu nasarar shawo kan su tare da canza fasalin jihar daga halin rai kwakwai- mutu kwakwai da ya same ta.
Ya ce “A yau Mai Girma Gwamna Lawal ya gabatar mana da ainihin gaskiyar mene ne halin da ake ciki da batutuwa, kalubale da kuma hasashen makomar Zamfara a nan gaba.
“A waje na, wannan ya kasance kamar bitar abin da na sani ne game da Zamfara. Na taso a can, kuma aikina ya kai ni sake komawa jihar. Na san duk irin kalubale da tsananin adawar da aka yi masa lokacin da yake takarar gwamna. Yanzu wannan ya riga ya zama tarihi domin ya sauya fasalin jihar daga mawuyacin halin da ya same ta zuwa kayatacciyar jiha.”
A Shirye Muke Mu Kulla Hadin Guiwa Da Jihar Zamfara – Mataimakiyar Sakataren MDD
A ranar 10 ga Afrilu 2026, Mataimakiiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Muhammad ta jagoranci tawagar Majalisar a ziyarar musamman a Zamfara. A cikin tawagar ta akwai shugaban UNDP Elsie Attafuah, shugaban UNODC, Cheik Toure, shugaban UNICEF, Wafaa Saeed, shugaban IOM, Sharon Dimanche, shugaban UNHCR, Arjun Jain, shugaban UNAIDS, Krittayawan Boonto da kuma shugaban UNFPA Francis Kuawu.
Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada cewa gabatarwar da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi mai ma’ana ce wadda ta fayyace komai wanda hakan ya ba su damar yin hadin guiwa.
Ta kara da cewar “Abin da kuka nuna mana a yau da farko shi ne kaunar da kuke da ita ga abin da kuke so mu taimaka muku a kai, kuma wannan shi ne abin da masu zuba jari ke nema wato suna son su san ainihin abin da kuke so.”
Ta ce “Na yi matukar farin cikin kasancewa ta a Zamfara a yau domin ina son nunawa duniya cewa ya kamata a mayar da hankali kan abin da ke faruwa a matakin kananan hukumomi domin a nan ne mutane suka fi rauni, a nan ne tsarin mulki ya fi rauni, kuma a nan ne ake da karancin albarkatu.”
“Lokacin da muka kawo ziyara, muna bayyana kokarin da aka yi da kuma tasirin abubuwan da ke faruwa a wasu sassa na duniya kan mutanen da ba su da hannu a abin da ya janyo shi tun da farko.”
“A Yau A Na Saukin Kaiwa Zamfara”
“Na ga harkokin ma’adinai, na ga damar da ke akwai, na ga kasuwa da bukatun jama’a, na kuma ga shugabanni da ke da niyar bin tsari da abubuwan da suka kamata tare da hadin guiwar da ake bukata domin a samu nasara.”
“Akwai dama mai yawa da za a amfana, amma dole kowa ya taka rawarsa, ba abu ne da gwamna shi kadai zai iya yi ba. Majalisar Dinkin Duniya a shirye take ta zama abokiyar hadin guiwa ta kwarai ga Jihar Zamfara.” in ji Amina Mohammed.
Da mutane Irin Gwamna Lawal, Za Mu Iya Magance Rashin tsaro – Babban Hafsan Soji
A ranar 21 ga Afrilu, 2026, Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya yabawa Gwamna Dauda Lawal, bisa goyon bayan musamman da yake baiwa ayyukan soji a jihar.
Oluyede ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara ta aiki da ya kai Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara a Gusau da kuma hedikwatar rundunar shirin Fansan Yamma a jihar, inda ya gana da gwamnan da kuma dakarun soji.
“Na zo ne a yau domin yabawa Mai Girma Gwamna bisa shirin Fansan Yamma, wanda hakika shiri ne na musamman. Ina so in yi maka godiyar musamman a kan hakan. “Haka kuma ina godiya ga al’ummar Zamfara da suke karrama baki. Kullum ina bayyana cewa Nijeriya kasar mu ce bakidaya kuma dole ne mu hadu bakidaya domin fuskantar wadannan kalubalen kai tsaye.”
“Da mutane irin Gwamna Dauda Lawal, za mu iya shawo kan wadannan matsaloli. Na zo ne domin na ziyarce ku da kuma gode muku bisa goyon bayan da kuke bayarwa.”
Muhimman Ayyukan Gwamna Lawal Sun Ciri Tuta – Kungiyar Kafafen Yada Labarai
Yabon da ake yi wa shirin Ceto Jihar Zamfara bai takaitu ga fitattun mutane kadai ba, domin har ma kungiyoyi sun nuna jin dadinsu kan kwazon da gwamnan ya nuna wajen mayar da Zamfara kan turbar ci- gaba.
A ranar 19 ga Afrilu, 2026, Kungiyar Kafafen Yada Labarai ta Kasa (BON) ta bai wa Gwamna Dauda Lawal lambar yabo a matsayin Gwamnan da ya fi kokari a fannin gine-ginen more rayuwa na shekara a sakamakon gagarumin ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a shirin sabunta birane a fadin jihar..
Kwamitin bayar da karramawar kungiyar ya kasance ne a karkashin jagorancin tsohon Darakta-Janar na Hukumar Kula da Kafafen Yadadan Labarai ta Kasa, Dakta Danladi Bako. Kwamitin karramawar ya hada da kwararru da wakilai daga Cibiyar Kula Da Tallace-Tallace ta Kasa da Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai.
“Kwamitin zaben ya bayar da dalilai da dama na bai wa Gwamna Dauda Lawal wannan karramawa, musamman irin ci- gaban da aka samu a fannoni daban-daban, musamman yadda aka sauya Gusau zuwa babban birnin jiha na zamani” n ji Dakta Danladi Bako.
Ya ce “Jhar Zamfara ta shaidi muhimman nasarori da ba a taba ganin irinsu ba a karkashin Gwamna Lawal, ciki har da gina sabon filin jirgin sama na kasa da kasa na zamani a jihar.
“Baya ga ayyukan sabunta birane da kuma ginawa da inganta asibitocin gwamnati, gwamnatin Dauda Lawal ta gina, ta gyara tare da samar da kayan aiki ga makarantu sama da 800 a fadi kananan hukumomi 14 na jihar.”
Hangen Nesa Da jajircewar Lawal Abin Koyi Ne – UNICEF
A ranar 13 ga Disamba, 2025 ne aka ayyana Jihar Zamfara a matsayin jiha mafi kwazo wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya a matakin farko a yankin Arewa- maso- Yamma.
An sanar da hakan ne a yayin bikin bayar da lambar yabo ta Cibiyoyin Kiyon Lafiya A Matakin Farko ta 2025 da aka gudanar a Abuja. A na bayar da lambobin yabon ne domin karrama gwamnonin da suka nuna kwazo da jajircewa wajen bunkasa fannin kiwon lafiya a matakin farko (PHC)
An kaddamar da wannan kalubale ne a shekarar 2022 ta hannun Kungiyar Gwamnonin Nijeriya domin karfafawa jihohi su inganta samar da kiwon lafiya a matakin farko tare da bunkasa hanyoyin dorewar samar da kudaden kiwon lafiya.
Shirin ya samun goyon baya daga Gidauniyar Bill da Melinda, Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) Gidauniyar Dangote da kuma Cibiyar Kula da Kiyon Lafiya A Matakin Farko ta Kasa.
Jihar Zamfara Ta Zo Ta Daya A Arewa Maso- Yamma Tare Da Lashe Kyautar Dala $500,000
Kwazo da jajircewar da jihohi suka nuna wajen lashe wannan gasar abin koyi ne kwarai kamar yadda Cristian Munduate wakiliyar Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Nijeriya ta bayyana.
“Jajircewar da suka nuna wajen inganta kiwon lafiya a mataki farko ya haifar da gagarumin tasiri mai ma’ana a rayuwar al’umma, musamman mata, ‘yan mata da yara. Nasara har sau biyu da Jihar Borno ta samu na nuna bayar da muhimmanci da hadin guiwa wajen bunkasa kiyon lafiya. Ina taya duk wadanda suka yi nasara murna bisa wannan kyakkyawan jajircewa a fannin kiwon lafiya a matakin farko.”
Lawal Ya Sauya Fannin iIimi Ta Hanyar Ciyar Da Dalibai – Cibiyoyin Kula Da Abinci Na Duniya
Kamar yadda ya yi fice a sauran fannoni, Gwamna Dauda Lawal ya samu yabo daga manyan kungiyoyin kasa da kasa kan shirin ciyar da dalibai. A watan Fabrairu 2026, wata tawaga daga International Food Policy Research Institute da World Food Programme, tare da abokan hulda na gwamnati daga shirin ciyar da dalibai suka bayyana hakan a yayin ziyarar da suka kaiwa Gwamnan.
“Manufarmu mai sauki ce amma a cikin gaggawa mun fahimci yadda shirin ciyar da dalibai a makarantu na jihar Zamfara yake wanda aka fara aiwatarwa kwanan nan a 2025″ in ji kungiyoyin na kasa da kasa a cikin wani rahoto na musamman mai taken Yadda Shirin Ciiyar Da Dalibai Ke Bunkasa Ilimi A Zamfara” wanda aka wallafa a ranar 27 ga Mayu, 2026.
“Jhar Zamfara ta fuskanci manyan kalubale a fannin ilimi. Talauci, rashin tsaro da karancin abubuwan more rayuwa sun bar dubban yara ba sa zuwa makaranta. A shekarar 2023, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ayyana dokar ta- baci a fannin ilimi, matakin da ya zama wani muhimmin juyin juya hali wanda ya haifar da kaddamar da sabbin manufofi da shirye- shirye da suka hada da gyaran makarantu, daukar malamai aiki, biyan bashin da ake biyawa hukumomin jarabawa (wanda ya kai ga fitar da sakamakon da aka rike na dubban dalibai) da kuma sake mayar da hankali kan inganta sakamakon karatu” kamar yadda rahoton Cibiyar Bincike Kan Tsarin Abinci Ta Duniya da Shrin Abinci Na Duniya ya bayyana.
Rahoton ya kammala da cewar “Darasin da za a koya daga Zamfara mai sauki ne amma mai tasiri domin idan a na samar da abinci mai gina jiki ga dalibai cikin tsari mai dorewa, yara na zuwa makaranta kuma suna ci- gaba da zama. A wuraren da ke fama da matsaloli da karancin kudade, ciyar da dalibai ba kawai shirin abinci ba ne, wata dabara ce ta ilimi, ta daidaiton jinsi da kuma bunkasa tattalin arzikin cikin gida.”
Yayin da shirin Ceto Jihar Zamfara ke cika shekaru uku da fara juyin juya hali, sakamakon da ke fitowa daga ko’ina ya bayyana karara a fili irin jinjina, yabo da karramawa suke tabbata ga jagoran raya Jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal.














Discussion about this post