Tawagar ƙasar Argentina da ta wakilci ƙasar a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kwanakin baya ta fuskanci turjiya da tsana ga wasu daga cikin magoya baya bisa yadda aka yi zargin suna samun goyon bayan hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, da kuma halayyar da ƴanwasan ƙasar suka nuna musamman a wasan ƙarshe da suka yi rashin nasara a hannun Sifaniya.
Wani hali da ake ganin ƙasar Argentina da ta ci kofin duniya sau uku ta tsinci kanta ciki.
Maƙiya wani lokacin ba dole sai na kusa ba, na nesa ma ana tattaro su a zo da su ba tare da lura ba.
Kuma lokacin da tawaga ta ƙasaita take iya doke kowa kamar yadda Argentina ta yi a Kofin Duniya na 2026, hakan ka iya tara mata maƙiya masu yawa.Hukumar ƙwallon ƙafa ta FIFA ce ke tsara yadda jadawalin wasannin gasar duniya ke gudana, bayan an kammala karkaɗe wajen raba rukuni. Abin da ya fara jan hanakalin masu bibiyar wasan ƙwallon ƙafa shi ne Argentina ba ta haɗu da ko ɗaya daga cikin ƙasashe 10 na jadawalin FIFA ba.
Sai a wasan kusa da na ƙarshe ne suka fafata da Ingila suka doke ta da ci biyu da ɗayaMafi yawan ƙungiyoyi masu ƙarfi da ke jadawalin FIFA sai aka tara su a wuri guda irinsu: Portugal, Jamus, Faransa, Sifaniya da dai sauransu. Wannan ya janyo fusata daga masu adawa da Argentina tare da zargin cewa FIFA ta yi hakan ne da sani don ta taimakawa ƙasar.
Tun a wasan farko da Argentina ta buga na Gasar Kofin Duniya mutane suka tare da nuna cewa FIFA na ɗauke kai ga ƙasar da kuma ƴanwasanta. Kyaftin ɗin ƙasar Lionel Messi ya taka ɗanwasan Algeria a wasan da ya ci ƙwallo uku rigis, irin takun da ake korar duk wanda ya yi, amma shi ko katin gargaɗi ba a bashi ba.
Wannan ya janyo surutu daga masu sharhi da masu bibiyar wasanni a faɗin duniya.
Duk da cewa an buga wasan ne cikin dare amma saboda Messi da kuma rashin nisan da gasar ta yi ana ɗokin ta miliyoyin mutane ne a faɗin duniya suka kalli wasan.
Alƙalin wasa bai je ya duba na’urar da ke taimaka masa ba, haka masu kula da ita ba su kira shi domin dubawa ba. A gasar, irin ƙetar da Messi ya yi ba a bashi komai ba, irinta ɗan wasan gaban Amurka Folarin Balogun ya yi aka ba shi jan kati kai tsaye.Wasan da Masar ta fafata da Argentina na daga cikin wasannin da suka bar baya da ƙura. Saboda idan mai karatu bai manta ba, sai da masar ta ci 2-0, amma aka farke aka ƙara mata cikin ƙanƙanin lokaci.
Masar ta ci ƙwallo ta uku ta hannun Zico a wata kora mai kyau da suka samu amma daga ƙarshe aka kashe ƙwallon, da zargin an taka Martinez kafin a ƙwace ƙwallon a ci Argentina.
Masana harkokin alƙalancin wasa a duniya sun samu rabuwar kai, wasu da dama na cewa ba a yi komai ba, wasu kuma na cewa an taka Martinez gabanin ɗaukar ƙwallon da aka ci.
Messi da sauran ƴanwasan Argentina sun riƙa nuna baƙin ɗabi’u, doke-doke, yawan faɗa da rashin haƙuri – kamar yadda ƴan nahiyar Kudancin Amurka suka saba. A wasan da Argentina ta doke Switzerland an ga Messi na nuna yatsa ga alƙalin wasa Joao Pinheiro ɗan ƙasar Portugal yana yi masa gargaɗin ya girmama shi.
Romero na daga cikin ƴan wasan da suka riƙa buga wasa tamkar yaƙi a gasar, ko kuma idan sun yi nasara kan wata ƙasa su je su yi ta ihu gaban abokan wasan nasu domin cusa musu damuwa.
Ɗan wasan da ke buga wasa a Ingla ya yi irin wannan murnar ne a gaban mai tsarin ragar Ingilan, sai dai bai ce masa komai ba.
Ban da wasan ƙarshe na Kofin Duniya babu wani wasa da Argetina ta yi da babbar tawaga sai wasan Ingila, kuma shi ma kamar sauran wasanni ya bar baya da rikici.
Wasa ne wanda a tarihi yake da daɗaɗɗiyar gaba, kuma ake sabunta ta duk lokacin da za a yi shi.A shekarun 1980 an yi yaƙin kwana 74 kan rukunin tsuburan Falklands, tsakanin Argentina da Burtaniya. Tsibirin da ke kusa da Argentina duka ɓangarori biyun sun yi iƙirarin mallakarsa, abin da ya kai su ga yaƙi da kashe sojojinsu.
Dab da za a fara wasan, mataimakiyar shugaban ƙasar Argentina ta wallafa wani saƙo a shafinta na Intanet, inda ta yi magana kan tsibirin. Bayan Argentina ta yi nasara ƴan wasanta sun ta ɗaga tutar wadda fassarar ke nufin “tsiburin Falklands na Argentina ne”. Duk da cewa sun kwana da sanin hakan ba daidai ba ne amma sun yi.
Rahotanni sun ce FIFA za ta ɗauki mataki kan wannan abin da suka yi, ta hanyar hukunta su.Ko a 2014, FIFA sai da ta ci tarar hukumar ƙwallon ƙafa ta Argentina fan dubu ashirin 20,0000 bayan ta ɗaga tuta makamanciyar wannan a wani wasan sa da zumunta da suka yi da Slovenia.
Amma abubuwan da suka faru a wasan ƙarshe na gasar kofin duniya ka iya haifarwa da ƙungiya baƙin jini da tarin maƙiyan da ba a yi zato ba saboda halayyar da ƴanwasan ƙasar suka nuna a lokacin buga wasan da bayan an tashi.
Ƴan wasan Argentina Paredes da Molina da Almada da kuma mai taimakawa koci Roberto Ayala duka an gansu da hannu cikin rikicin lokacin da Sifaniya ke murnar samun nasara da ci 1-0.An ga Parades ya shaƙi wuyan Eric Garcia ɗan wasan Sifaniya da kuma kayar da Gaɓi yana yunƙurin taushe shi yayin da shi ma Almada ya taimaka masa. Paredes bayan ya kayar da ɗan wasan na Barcelona ya nemi ya dake shi a fuska.
Tuni FIFA ta kafa kwamitin bincike kan lamarin, tare da alƙawarin tara mai tsoka kan duk wanda aka kama da laifi domin kamar yadda masana suka bayyana abin da ƴan wasan suka nuna ba ɗabi’ar kirki ba ce, kuma mai yin ta ba zai gaza samun ɗimbun maƙiya ba.
Argentina ta fi kowacce ƙasa cin kofuna a duniya, ta ci kofina 23 jimmila, wadda ke kusa da ita Brazil ce da kofina 20 saboda haka bai kamata a ce ƙasa mai irin wannan tarihin tana nuna halin rashin tarbiyya ba.
Ga magoya bayan Ronaldo, adawar dake tsakanin Messi da Cristiano Ronaldo tana cikin abubuwan da suka ƙarawa tawagar baƙin jini saboda Ronaldo yana da miliyoyin magoya baya, duk da cewa shima Messi yana da su, amma ana ganin kamar ba su kai irin na Ronaldo ba.
Saboda haka ana ganin duk abin da Messi da Argentina za su yi a wajen abokan gabarsu ba zai zama abin yabo ba, duk kuma abin da suka yi na ɓaci zai zama abin zambo a gare su. Sannan salon wasansu da suke bugawa da ƙarfi da sa jiki yana daga cikin abin da yake sa wasu na jin haushinsu.














