ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirye-shiryen Farko Na Ramadan Ga Uwargida

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
5 months ago
Ramadan

Shirye-shiryen farko na Ramadan ga Mata:

Ki tsaftace dakinki, ki dan canza tsarinsa kadan, ki yi masa tsabtacewa sosai. Ki wanke kayan Sallah da tabarmar Sallah, sannan ki sa musu kamshi, ki tanadi wani karamin kusurwa a dakinki domin ibada. Ko da wurin kankani ne ko ya matse, za a iya amfani da shi.

Ki ajiye kayan Sallah, tabarmar Sallah da Al-kur’ani a wannan kusurwa, ki rika yin Sallah da addu’a a wurin. Ya isa wannan wuri ya zama shaida a gareki a ranar Alkiyama.

ADVERTISEMENT

Sannan ki samo akwati na ajiya, ki rubuta “Akwatin Sadakar Ramadan,” ki rika sa dan kudi a ciki kullum, ki yi amfani da shi wajen aikin alheri kamar sayen kayan Sallah ga yara ko ciyar da marayu a lokacin buda baki.

Kyakykyawar shawara: Ki rika rabon kayan buda bakiinki da iyali marasa karfi kowace rana. Ki kara abinci kadan, ki sanar da su cewa kayan buda bakinsu daga gare ki ne.

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

Ki zabi wata sura daga Alkur’ani da kike so kuma kike jin kusanci da ita, ki dauki alkawari ga Allah za ki haddace ta. Za ki samu lada mai yawa a wannan wata mai albarka.

Ki yawaita nema gafara ga Allah, ki sanya niyya daban-daban a istigfarinki, kamar rokon Allah ya ba ki ‘ya’ya nagari, sauki daga damuwa, ko duk wata bukata da yawa daga matsaloli an warware su ta hanyar istigfari.

Ki dauki mutum uku (’yan’uwa ko abokai) a addu’arki. Kowace rana ki yi addu’a ga mutane uku da sunayensu, ki kuma roke su su yi miki addu’a, za ki ga sakamako kafin karshen watan. Mala’iku na cewa: “Kuma a gare ki irinsa.”

Ki yi Hajj da Umrah kowane mako a Ramadan. Eh! Ki zabi rana ko ranaku a mako ki yi haka: ki yi Sallar Asuba, ki zauna a kan tabarmar Sallah, ki yi addu’a, zikiri, da karatun Alkur’ani har fitowar rana, sannan ki yi raka’a biyu. Wannan yana ba da ladan cikakken Hajji da Umara.

Ki yawaita karatun Alkur’ani, ki yi niyyar kammala shi sau uku a Ramadan. Ko da ba ki kai ga kammalawa ba, za ki samu lada bisa niyyarki. Kowane harafi lada goma ki yi tunanin yadda ladan ya karu a Ramadan! Ki yi amfani da wannan dama.

Ki rika ajiye dan kudi kullum, sannan duk bayan kwanaki goma ki ba maraya sadaka dan kudi kadan a kullum tare da manufa a wannan wata mai tsarki, ki sadaukar da shi ga wani buri da kike fatan cikawa.

Ki tsara jadawalin ibadarki na kanki, ki bar shi sirri tsakaninki da Allah.

Ramadan
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Wainar Masara Da Miyar Yaji
Ramadan
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
  • Sulaiman
    Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Ramadan
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Yadda Shan Taba Ke Yi Wa Mata Illa

Yadda Shan Taba Ke Yi Wa Mata Illa

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.