Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Bauchi ta buƙaci iyaye mata su riƙa shayar da jariransu nonon uwa zalla, tana mai cewa hakan ba ya sa nono ya zube.
Shugaban hukumar, Dakta Rilwanu Muhammad ne, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da Makon Shayarwa na Duniya na 2026 a Bauchi.
Ya ce sauyin da nono ke yi yana da alaƙa da shekaru, ba shayarwa ba.
Ya ce shayar da jariri nonon uwa zalla na watanni shida na farko yana kare yaro daga tamowa da cututtuka, sannan yana taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cututtuka kamar kansar nono da kansar mahaifa ga uwa.
A cewarsa, talauci, tsadar kayan abinci da rashin sanin yadda ake amfani da abincin gida masu gina jiki na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa tamowa a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa idan uwa tana cin abinci mai gina jiki, jaririnta ma zai amfana.
Dakta Rilwanu ya kuma buƙaci iyaye mata su fara ba jarirai nono awa ta farko bayan haihuwa, domin madarar farko tana ƙarfafa garkuwar jikin jariri.
A nata ɓangaren, Babbar jami’ar UNICEF a Bauchi, Dakta Nuzhat Rafique, ta ce duk da cewa yawancin iyaye mata na shayar da jariransu, kaɗan ne ke bin ƙa’idojin shayar da nono yadda ya kamata.
Ta gargaɗi iyaye da kada su bai wa jarirai ruwa, zuma ko wasu ruwan gargajiya kafin su cika watanni shida, saboda hakan na iya jefa su cikin haɗarin kamuwa da cututtuka.
UNICEF ta kuma yaba wa gwamnatin Jihar Bauchi bisa amincewa da hutun haihuwa na watanni shida ga ma’aikatan gwamnati mata, tana mai cewa hakan zai ƙara tallafa wa shayar da jarirai nonon uwa da inganta lafiyar uwa da yaro.














