A hukumance, guguwar gudanar da gangamin yakinin neman zabukan kakar 2027, musaman na takarar Kujerar shugaban kasa, tuni gangamin ya fara daura damara.
A gafe daya kuma, babban abinda ya kamata ‘yan kasar su bukata na da ban su ne, musamman cancantar dan takara, sauran wasu shirye-shiyen da suka sha ban ban da na baya, ba wai irin romon baka da ‘yan takara suka saba yi masu lokacin yakin neman zaben ba, na bijiro masu da batun wanda ya fi cancanta, yin amfani da kabilanci ko addini domin neman kuri’un masu yin zabe ba.
Zaben na shugaban kasa a 2027, kusan za a iya cewa, zai kasance mafi cike da dimbin tarihi, musamman ga ‘yan Nijeriya duba da irin dimbin matsin rayuwa da na tattalin arziki, kalubalen rashin tsaro rashin aikin yi da ke ci gaba da yin kamari, tabarbarewar fannin samar da wutar lantarki da kuma rashin tabbas daga bangaren ‘yan siyasa masu rike da madafun iko.
Babu makawa, gwamnatin shugaba Bola Tinubu mai ci, na da matukar muradin, son yin tazarce a 2027, musamman duba da yadda gwamnatin ke ci gaba da kafa hujja kan sauye-sauyen da ta kirkiro da su, wanda a nata ra’ayin, abubuwa ne, da ke bukatar lokaci, kafin ‘yan kasar, su fara gani a cikin Kokonsu.
A tsagin jami’iyyun hamayya kuwa, suna ta ci gaba da yin yarfen siyasa wajen shelantawa ‘yan kasar cewa, gwamnatin Tinubu, ta gaza sauke nauyin da ‘yan Nijeriya suka dora mata, wanda a saboda haka, ya kamata ‘yan kasar, su sake tunani, kan zabar wata sabuwar gwamnatin.
Ya zama wajibi, ‘yan kasar su tabbatar da sun kyamaci duk wani nau’i gangamin yakin neman zabe na jifan junansu da kalaman habaici domin kawai, su samu karbuwa a gun masu jefa kuri’a.
Sai dai, wani abin takaicin shi ne, tuni ‘yan takarar suka yi nisa na aikata, wannan dabi’ar kalaman musamman yadda suke fakewa a inuwar addini da bangaranci da kuma nuna irin matsayin irin kimar suke da ita a kasar.
Kazalika, batun ba wai APC mai mulki ko jami’iyyun hamayya ba ne, da suka cancaci lashe zaben ba ko kuma yadda ‘yan takarar suke fakewa da wasu batuw suna yiwa junansu habaicin siyasa ba.
Amma kamata ya yi ‘yan takarar su baje kudurorin su a Faifai, da su son yiwa ‘yan Nijeriya kafin su zabe su, wanda hakan zai bai wa ‘yan kasar, damar tantance irin shugabannin da ya kamata su zaba a 2027.
‘Yan kasar, na da hakkin sanin irin alkawuran da ‘yan takarar suka zo da su, kudaden da za su kashe a lokacin yakin neman zaben, me suke da burin wanzarwa, domin amfanin ‘yan kasar wanda hakan, zai sanya ‘yan kasar za su samu damar auna irin kokarin da ‘yan takarar suka yi a baya.
Haka zalika, ya wajaba ‘yan takarar shugaban kasa su tabbatar da sun wanzar da alkawarin da suka rattaba hannu, na tabbatar da zaman lafiya a lokacin yakin neman zamansu.
‘Yan takarar shugaban kasa da dama, ciki har da, Peter Obi da Omoyele Sowore ne, suka halarci wajen rabbata hannun yarjejeniyar ta zaman lafiyar, inda shi kuma shugaba Tinubu, sakataren gwamnatin tarayya sanata George Akume, ya wakilce shi.
Sai dai, abin dubin a nan shi ne, akasarin irin wannan yarjeniyar a kasar, ta kan kasance kawai, ta jeka na yi ka ce, domin wasu ‘yan takarar suna yi mata hawan kawara, yayin gudanar da gangaminsu, na yakin zeman zaben.
Abin tambayar a nan shi ne, idan ‘yan takarar suka sabawa wannan yarjejeniyar, ta hanyar tunzura haifar da tashin hankali da yiwa ‘yan kasar romon baka, shin, menene zai biyo baya? Wa zai gudanar da bincike? Wanne irin takunkumi, za a kakaba masu, kan take wannan yarjejeniyar ? A nan, kafin yakin neman zaben, sukar juna da kalaman habaici da janyo tayar da tarzoma, rukunin da ya kamata su amsa wadannan tambayoyin su ne, hukumar zabe ta kasa INEC, hukumomin tsaro, jami’iyyu, kungiyoyi masu zaman kansu.
Bugu da kari, babban nauyin da ke kan INEC sun hada da, tabbatar da kare, kimar kuri’un tare da tsarin kuri’a na zamani wato BBAS, musamman domin tabbatar samar da sahihi samakamon zaben da kuma bin ka’idojin gudanar da yin zabe.
Bai kamata tsarin yin amfani da kimiyyar zamani domin gudanar da zabuka, su zama wata kafa ta nuna shakku a tsakanin ‘yan kasar ba, amma kamata ya yi su kara samun kwarin guiwar, fatan gudanar da sahihi kuma tsarkaken zaben.
Ya wajaba, duk ‘yan takara su sani cewa, dole a lokacin duk wata gasa, akwai wanda zai yi nasara, da kuma wanda zai sha kayi.
Bugu da kari, ya zama dole, a magance batun sayen kuri’u a lokacin da ke kan ganiyar jefa kuri’a, haka ya zama wajbi, ‘yan kasar, su daina bari, ‘yan takara suna raba masu Taliya ko wasu kayan masarufi, domin su zabe su ko kuma kirikiro masu da wasu shirye-shirye na jeka nayi kan, wadanda bayan zabe, ba su kara yin wani tasiri.
‘Yan Nijeriya na da hakkin sauraron tattaunawar da za a yi da ‘yan takarar na shugaban kasa, a bagiren da aka saba gudanarwa, musamamn duba da cewa, wajen tattaunawar, ta kasance, wani bagire ne, da ‘yan takarar za su baje kolinsu, ta hanyar bayyana yadda za su kai kasar, ga tudun muntsira, in sun lashe zaben.
Bagiren tattaunawar dai, wajen da ke bai wa ‘yan takarar, damar amsa dimbin tambayoyi da suka hada da, kan fannin tsaro, tattalin arzikin kasa, ilimi, samar da aikin yi, da sauransu.
Kazalika, kafafen yada labarai, suma akwai nauyi a kansu a lokacin gudanar da zaben, musamman wajen gujewa yada labaruka da rahotannin da ke da nasaba da addini, kabilanci, da kuma yada labarukan kanzon Kurege.
Zaben shugaban kasar na kaka mai zuwa, bai kamata ya zama tamkar wani fagen dagar kada kuri’un raba gaddama, a tsakanin kan irin salon salon shugabancin Tinubu da ‘yan takara masu hamayya ba, amma kamata ya yi, zaben ya kasance, na kishin ciyar da Nijeriya gaba kuma wanne dan takara ne, ya fi cancanta, ya shugabanci Nijeriya.
Tuni dai, an riga an kada Gangar zaben, inda ‘yan takara za su fara zawarcin kuri’un ‘yan kasar da suka kai munzalin jefa kuri’a.
A wannan muna gani tambayar da ta kamata ‘yan Nijeriya su yiwa ‘yan takarar ita ce, shi ne, me za su yi da madafun ikon da suke ta kai gwaro da mari, idan an zabe su ?














