A yau Alhamis, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa kasar tana matukar adawa da matakin Amurka na sanya mutum-mutumin inji da na’urar lantarki ta inbata da aka kera da fasaha mai zurfi a kasashen waje, a cikin jerin abubuwan da hukumar sadarwa ta tarayya (FCC) ta hana shigo da su.
Hukumar FCC ta sanar a ranar Talatar da ta gabata cewa, daga yanzu sabbin samfuran mutum-mutumin inji da na’urorin lantarki na inbata da aka kera da fasaha mai zurfi a kasashen waje, ba su daga cikin kayan da hukumar ta ba da izinin shigo da su, inda hakan ya yi cikakkiyar haramta shigar da su kasuwar Amurka.
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin ta Sin ya bayyana cewa, Sin tana kira ga Amurka da ta janye wadannan matakai nan take tare da dakatar da kurakuran da take tafkawa. Jami’in ya kuma ce, idan Amurka ta ci gaba da aiwatar da matakan, Sin za ta dauki kwararan matakan mayar da martani domin kare muradunta. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)













