ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Umarci A Farauto Ƴan Bindigar Da Suka Kashe Mutum 30 A Kaduna

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
1 month ago
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa mazauna ƙauyen Naridon da ke Unguwar Kamaru, Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Shugaban Ƙasan ya kuma umarci hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su ƙara tsaurara ayyukansu a al’ummomin da lamarin ya shafa domin gano waɗanda suka aikata harin tare da tabbatar da kuɓutar da duk wani mutum da aka yi garkuwa da shi.

Harin, wanda ya faru da sanyin safiyar Litinin, ya yi sanadin mutuwar kusan mazauna 30, ciki har da mata da yara, yayin da aka ƙona gidaje da dama.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana harin a matsayin wani ta’addanci marar dalili da aka kai wa fararen hula marasa galihu.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa za a gurfanar da duk waɗanda ke ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron da Jihar Kaduna ta samu kanta a cikin ƴan shekarun nan a gaban kotu.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, Gwamna Uba Sani, gwamnatin Jihar Kaduna da al’ummar jihar bisa wannan mummunan lamari.

Shugaban Ƙasa ya tabbatar wa gwamnatin jihar da al’ummomin da lamarin ya shafa cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba su goyon baya, yana mai cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar magance ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar.

Ya ce: “Na umarci Rundunar Sojin Nijeriya, ƴansanda da hukumomin leƙen asiri da abin ya shafa da su ƙara tsaurara ayyukansu a dukkan yankunan da lamarin ya shafa domin gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika cikin gaggawa, tabbatar da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.”

Shugaba Tinubu ya kuma ce gwamnatinsa “ta ƙuduri aniyar ƙarfafa ababen more rayuwar tsaro, samar da kayan aiki ga jami’an da ke mayar da martani ga barazanar tsaro, da kuma kawar da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasa.”

Sanarwar ta ce: “Ina kira ga al’ummomin yankunanmu da su ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar samar musu da sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen ɗaukar matakin gaggawa.”

Tinubu
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Tinubu
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

Jadawalin Zaɓen 2027: Masana Da Ƴan Siyasa Na Tafka Muhawara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.