Kasar Sin ta samu karuwar yawan sabbin kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a kasar, tare da samun gagarumin ci gaba wajen samun jarin kasashen waje na kai-tsaye a masana’antun manyan fasahohin zamani, cikin watanni bakwai na farkon shekarar 2026, duk da cewa jimillar kudaden zuba jarin na kasashen waje ta ragu, kamar yadda bayanan da mahukunta suka fitar yau Jumma’a suka nunar.
Bayanan daga ma’aikatar cinikayya ta Sin sun nuna cewa, a tsakanin wannan lokaci, an kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje 37,711, adadin da ya karu da kashi 4.4 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, yayin da kuma jarin kasashen waje da aka zuba kai-tsaye da aka fara amfani da shi a zahiri, ya kai yuan biliyan 438.33, watau kwatankwacin dalar Amurka biliyan 64.63, wanda ya ragu da kashi 6.2 idan aka kwatanta da na bara.
Idan aka dubi bangaren, sashen masana’antu ya samu jarin kasashen waje na kai-tsaye yuan biliyan 109.43, yayin da bangaren ayyukan ba da hidima ya samu yuan biliyan 319.95.
Duk da raguwar jimillar da aka samu, jarin waje na kai-tsaye da aka zuba a masana’antun manyan fasahohin zamani ya habaka da kashi 32.7 cikin dari, inda ya kai yuan biliyan 182.31, wanda ke nuna ya kai kashi 41.6 na jimillar na kasa baki daya, lamarin da ya nuna an samu karuwarsa da kashi 12.2 cikin dari idan aka kwatanta da na bara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














